'Mutum 30,000 Za a Dauka': Matasan da Suka Nemi Aikin CDCFIB Sun Haura Miliyan 1.9
- CDCFIB ta ce mutane miliyan 1.91 ne suka nemi guraben aikin da aka ware wa mutum 30,000 kacal a hukumomin tsaro hudu
- Kididdigar ta nuna jihar Kogi ce ta fi yawan masu neman aiki da mutum 116,243, sai Kaduna 114,599, sannan Benue mai mutum 110,644
- Yayin da ta sha alwashin daukar aikin bisa cancanta, CDCFIB ta ce za ta aika sako ga wadanda suka tsallake tantancewar farko
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Hukumar kula da hukumomin NSCDC, gidajen gyaran hali, FRSC da NIS (CDCFIB) ta ce 'yan Najeriya miliyan 1.91 ne suka nemi aiki da ita.
Idan ba a manta ba, mun ruwaito cewa gwamnatin tarayya ta ayyana daukar mutane 30,000 aiki a karkashin hukumar CDCFIB.

Asali: Twitter
Mutane miliyan 1.91 sun nemi aikin CDCFIB
Legit Hausa ta tattara bayanai game da adadin wadanda suka nemi aikin da jihohin da suka fito daga shafin daukar aiki na CDCFIB da ke kan yanar gizo.

Kara karanta wannan
Bayan shekara 3 ana farautarsa, babban dillalin kwayoyi a Najeriya ya shiga hannu
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mutane miliyan 1.91 da suka cike guraben neman aikin ya haura adadin mutanen da gwamnati za ta dauka a hukumomin tsaron guda hudu.
Wannan na nufin cewa mutane 69 ne za su fafata a neman gurbin aiki daya, yayin da hukumar CDCFIB ta sha alwashin yin amfani da cancanta wajen daukar aikin.
Kamar yadda kididdiga ta nuna, jihohin da aka fi yawan samun masu neman aikin su ne Kogi, da mutane 116,243; sai jihar Kaduna da ke binta da mutane 114,599 sai kuma Benue da mutane 110,644.
Kididdigar masu neman aikin CDCFIB
Kididdigar ta nuna adadin mutanen da suka nemi aikin daga kowacce jiha kamar haka:
Kano - 89,421
Niger - 79,567
Kwara - 78,467
Katsina - 76,917
Nasarawa - 76,677
Adamawa - 68,381
Oyo - 67,255
Plateau - 63,450
Osun - 62,399
Borno - 56,955
Ondo - 53,963
Akwa Ibom - 52,531
Bauchi - 52,159
Imo - 48,301
Taraba - 45,188
Gombe - 45,074
Jigawa - 44,468
Ogun - 42,070
Enugu - 41,291
Yobe - 38,169
Kebbi - 34,612
Edo - 33,581
Anambra - 32,933
Ekiti - 32,719
Cross River - 32,226
Abia - 31,716
Sokoto - 31,155
FCT Abuja - 30,320
Zamfara - 29,282
Delta - 27,980
Ebonyi - 23,617
Rivers - 22,217
Lagos - 14,221
Bayelsa - 11,680

Asali: Twitter
CDCFIB ta aika sako ga masu neman aiki
A cewar sanarwar da hukumar ta fitar a shafinta na X, za ta tuntubi wadanda suka haye zagayen farko na daukar aikin, tare da fada masu mataki na gaba.
"An kammala cike gurbin neman aiki a hukumomin NSCDC, gidajen gyaran hali, FRSC da NIS, yanzu an rufe shafin cike gurbin.
"Muna godiya ga dukkanin wadanda suka nuna sha'awar neman aikin da kuma burinsu na yi wa kasa hidima.
"Za a tuntubi wadanda suka tsallake matakin farko da abin da za su yi a gaba. Ku ci gaba da duba akwatunan imel da na tes a makonni masu zuwa."
- Hukumar CDCFIB.
"Ina matasa za su sanya kawunansu?"
A zantawarmu da Alhaji Hussaini Baban Nur, ya ce akwai bukatar matasan Najeriya su farga, su gane cewa babu ayyuka a gwamnati, don haka su nemi sana'o'in dogaro da kai.
Alhaji Hussai Baban Nur ya ce:
"Watakan ni abin yana matukar ba ni mamaki, sai ka rasa gane ina matsalar take? Da na duba adadin wadanda suka aikin nan sai na tambayi kai na, shin babu hanyoyin samun kudi ne sai aikin gwamnati?
"Ya kamata fa matasanmu su farga, tun lokacin tsohon shugaban kasa, marigayi Buhari aka fada masu cewa babu ayyuka a gwamnati, su nemi sana'a, amma sun ki ji.
"Yanzu don Allah ta ina za ka fara daukar wannan aikin, ace mutane kusan miliyan biyu sun cika gurbin neman aikin mutum 30,000 kacal, ai kasan akwai matsala."
Ya ba matasa shawara su kama sana'o'in hannu kamar noma, kiwo, walda, aski, saye da sayar da kayayyaki da dai sauran hanyoyin samun kudi na halal.
Shi kuwa Abubabar Sagir da muka zanta da shi ya nuna matukar damuwa kan yawan wadanda suka cike aikin da ya gani.
"Ni ma na cike, na nemi hukumar kashe gobara. Amma ni na karaya gaskiya, don daga ganin wannan sai wane da wane za su samu, wa ka sani, wa ya sanka.
"Don Allah ina matasa za su sanya kansu? Aikin gwamnatin ba ma samu, sana'ar ma sai kana da jari, ga shi komai ya yi tsada, mun gama makarantar sai yawo muke da takardu."
- Abubakar Sagir.
CDCFIB ta kori ma'aikata a hukumar NCoS
A wani labarin, mun ruwaito cewa, hukumar CDCFIB ta sallami jami'ai 15 na hukumar gidajen gyaran hali ta ƙasa (NCoS) tare da ragewa wasu ma'aikata 59 girma.
A wata sanarwa da kakakin hukumar, Umar Abubakar ya fitar, ya ce an ɗauki wannan matakin saboda jami'an sun aikata laifuffuka da rashin ɗa'a.
Umar Abubakar ya ce ƙarƙashin jagorancin ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, hukumar za ta tabbatar da cewa jami'anta na bin ƙa'idoji.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng