Katsina: Yan Siyasa, Sarakuna Sun Zauna da Yan Bindiga, an Kafa Sharuda 20 na Zaman Lafiya
- An samu fahimtar juna bayan sake zaman tattaunawar sulhu da yan bindiga a karamar hukumar Safana a jihar Katsina
- Karamar hukumar ta kulla yarjejeniyar sulhu da ‘yan bindiga, kamar Jibia, Batsari, da Danmusa, domin samar da zaman lafiya
- Yarjejeniyar ta ba manoma damar noma cikin kwanciyar hankali, yayin da Fulani ke zuwa kasuwa da asibiti ba tare da tsangwama ba
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Safana, Katsina - An sake zama da yan bindiga domin dakile yawan hare-hare a jihar Katsina da ke Arewa maso Yamma.
Karamar Safana a jihar Katsina ta shiga yarjejeniyar sulhu da ‘yan bindiga, kamar Jibia, Batsari, da Danmusa, domin samar da zaman lafiya.

Source: Facebook
An yi sulhu da 'yan bindiga a Katsina
Rahoton Daily Trust ya nuna kafin wannan, kananan hukumomi uku ne suka kulla yarjejeniya, inda aka ba manoma damar shiga gona cikin lumana.

Kara karanta wannan
Nasara daga Allah: Sojoji sun babbake yan bindiga fiye da 100 a Zamfara, an yada hotuna
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Haka kuma, yarjejeniyar ta bai wa ‘yan bindiga damar zuwa kasuwa, asibiti, da shaguna cikin garuruwa domin harkokin yau da kullum.
Kananan hukumomi kamar Kankara, Faskari, Dutsinma, Sabuwa, Malumfashi, Kurfi, Bakori, Funtua, da Dandume ba su amince da wannan yarjejeniya ba, har yanzu suna fama da hare-hare.
Taron sulhun Safana ya gudana a gefen dajin Gemi, Runka, tare da halartar shugaban karamar hukumar, manyan sarakuna, da al’ummar gari.
An yi wa yan bindigan Katsina wa'azi
Bangarorin biyu sun amince su yi sulhu, su gina amana, tare da tabbatar da zaman lafiya a Safana da kewaye, cewar rahoton Bakatsine a shafin X.
Alhaji Sada Rufa’i ya yi farin ciki, ya bukaci manya ‘yan bindiga su ji tsoron Allah, su zauna lafiya, su mutunta yarjejeniyar.
Da yake jawabi, Kachalla Ruga Alhaji Usman ya ce:
“Tun da muka yanke shawarar yin sulhu, mu zauna lafiya, kowa ya yi aikinsa.”

Source: Original
Katsina: Sharudan da aka kafa da yan bindiga
Shugaban matasa, Abdulhamid Danda, ya bukaci matasa daga dukkan bangarori su ji tsoron Allah su kuma goyi bayan wannan yarjejeniya.
Shugaban karamar hukumar, Abdullahi Sani Safana, ya yi farin ciki, ya alkawarta kare mutuncin kowa da kuma inganta wuraren kiwon lafiya da ilimi.
Ya kuma tabbatar da samun damar shiga asibiti, kasuwa, da sauran muhimman wurare, tare da gyara tafkunan ruwa don amfanin jama’a da dabbobi.
Daga cikin manyan sharuɗɗa 20 da aka gindaya sun hada da daina kai hari, kashe-kashe, da garkuwa, tare da bai wa manoma damar shiga gonaki ba tare da tsangwama ba.
Malami ya soki tsarin sulhu da yan bindiga
Kun ji cewa Sheikh Ishaq Adam Ishaq ya yi watsi da ra'ayin tattaunawar sulhu da ‘yan bindiga, yana mai cewa Musulunci ya umurci a yake su ba tare da bata lokaci ba.
Malamin ya bayyana cewa addini da dokar kasa duk sun amince a kashe su ko a hukunta su matukar suna ci gaba da barna a doron kasa.
Ya kalubalanci masu cewa ‘yan bindiga sun fi karfin jami’an tsaro, yana mai jaddada cewa gwamnati na da ikon kawo karshen su duk lokacin da ta ga dama.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
