Ana Wata ga Wata: Hukumar EFCC Ta Tsare Tsohon Gwamnan Sokoto, Aminu Tambuwal
- Hukumar EFCC ta tsare tsohon gwamnan Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, kan zare Naira biliyan 180 daga banki ba bisa ka’ida ba
- Rahotanni sun ce cire kudaden ya sabawa dokar yaki da safarar kudi ta 2022, kuma ana zarginsa da aikata hakan lokacin mulkinsa
- Tambuwal ya isa ofishin EFCC da safiyar Litinin, inda jami’an hukumar ke yi masa tambayoyi yayin da ake dakon karin bayani kan lamarin
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Rahotannin da Legit Hausa ta samu yanzu na nuni da cewa hukumar EFCC ta tsare tsohon gwamnan Sokoto, Aminu Wiziri Tambuwal.
An rahoto cewa Tambuwal ya shiga kumar EFCC ne kan zargin cire wasu kudade da suka kai N180bn daga banki ba bisa ka'ida ba.

Source: Facebook
Aminu Tambuwal ya isa ofishin hukumar EFCC
Jaridar The Cable ta rahoto cewa cire kudaden da ya tsohon gwamnan ya yi ya sabawa dokar yaki da safara da wanke kudin haram ta 2022.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya zuwa lokacin da aka fitar da rahoton, jaridar ta ce ba ta iya sanin a tsawon wane lokaci ne tsohon gwamnan ya cire wadannan kudade ba.
An rahoto cewa Tambuwal ya isa ofishin hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC da misalin karfe 11:30 na safiyar Litinin.
An ce tsohon gwamnan jihar na Sokoto ya gurfana gaban jami'an EFCC, inda yake amsa masu tambayoyi game da zargin da ake yi masa.
Zargen zargen da ake yi wa Tambuwal
Wani babban jami'in EFCC, da ya nemi a sakaya sunansa ya ce Tambuwal na fuskantar tambayoyi kan cire kudade ba bisa ka'ida ba.
Haka zalika, ana tuhumar sa da zare biliyoyin kudaden a lokacin da yake kan kujerar gwamnan Sokoto - abin da ake zargi da ya saba wa doka, inji rahoton Vanguard.
"Yanayin yadda aka cire wadannan kudade ya sabawa dokar yaki da safarar kudi," a cewar majiyar, yana mai cewa an shafe watanni ana bincike kafin gayyatarsa.

Source: UGC
Hukumar EFCC ba ta ce uffan ba tukuna
Mai magana da yawun hukumar EFCC, Dele Oyewale, ya ce ba zai yi magana a kan lamarin ba har sai an kammala yi wa Tambuwal tambayoyi.
Tambuwal dai ya kasance babban jigon PDP, wanda ya yi gwamnan Sokoto daga 2015 zuwa 2023 kuma a baya ya riƙe kujerar kakakin majalisar wakilai.
Ana ci gaba da dakon karin bayanai game da tsare Tambuwal da EFCC ta yi, da kuma abin da binciken hukumar ya bayyana.
Tambuwal ya hango faduwar Tinubu a 2027
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Aminu Tambuwal ya ce idan Allah ya yarda jam'iyyar PDP za ta karɓe mulkin Najeriya daga hannun APC a zaɓen 2027.
Tsohon gwamnan na Sokoto ya bayyana hakan ne a wurin taron fara rabon kayan abinci ga al'ummar mazaɓarsa da ma Sokoto baki daya.
Aminu Waziri Tambuwal ya ce jam'iyyar PDP ta shirya dawo da abin da aka ƙwace mata a zaɓen 2023, yana mai rokon ƴaƴan jam'iyyar su haɗa kansu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

