Sanata Ya Cire Fargaba, Ya Tona Wadanda Suke Daukar Nauyin Kisan Mutane a Filato
- Sanata Diket Plang ya yi ikirarin cewa kungiyoyin kasashen waje ne ke daukar nauyin kisan mutane da ake yi a Bokkos, jihar Filato
- Ya bayyana cewa hare-haren sun jawo mutuwar mutane, lalata gonaki da gidaje da tilasta mazauna Mushere tserewa daga gidajensu
- Sanatan ya bukaci karin matakan tsaro, hadin kan al’umma, gina tituna, da taimakon gaggawa ga wadanda harin ya shafa a yankin
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Sanata Diket Plang ya yi ikirarin cewa kungiyoyi daga kasashen waje ne ke daukar nauyin kashe kashen da ake yi a karamar hukumar Bokkos, jihar Filato.
A wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin, sanatan ya ce "wannan mummunan aiki" ya tarwatsa zaman lafiya da ma rayukan mutanen Filato.

Asali: Twitter
Sanata ya magantu kan hare-haren Filato
Jaridar The Cable ta rahoto cewa Sanata Plang shi ne ke wakilatar mazabar Filato ta Tsakiya, kuma shugaban kwamitin kwadago da daukar aiki na majalisar dattawa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin sanarwar, sanatan ya ce hare-haren da aka kai sun yi sanadin mutuwar mutane da dama da lalata gonaki da gidaje tare da tilasta mutane yin hijira a masarautar Mushere da ke cikin Bokkos.
Sanarwar ta ce:
"A bayyana take a fili cewa burin masu daukar nauyin wannan ta'addancin shi ne korar mutane daga gidajensu domin su gaje kasar.
"Wadannan miyagun mutane sun fara aiwatar da mugun nufinsu ne daga Afrilun wannan shekara, inda suka fara da Bokkos tare da fadada shirinsu zuwa sassan Filato ta Tsakiya.
"Sai dai abin takaici, duk da kokarin da jami'ai da hukumomin gwamnati suka yi na yin sulhu da wasu kungiyoyi da daidaikun mutane, har yanzu ba a kawo karshen hare-haren ba.
Sanatan ya nemi a tsaurara tsaro a Filato
Yayin da Sanata Plang ya yabawa kokarin jami'an tsaro, ya nuna bukatar su fadada ayyukansu tare da daukar matakai masu tsauri na dakile 'yan ta'addar daga kwace garuruwan mutane.
Ya yi kira ga shugabannin al'umma, 'yan banga da mazauna wadannan garuruwa da su hada kansu, su taimakawa jami'an tsaro don magance matsalar tsaron, inji rahoton Tribune.
Sanatan ya kuma ba da shawarar a gaggauta gina tituna a yankunan da ake kai wa hari domin ba sojoji damar rika kai dauki cikin gaggawa, wanda zai taimakawa mutanen Mushere.
Ya kuma ba da shawara ga jami'an tsaro da su mayar da hankali kan tsaron iyakoki da muhimman wurare domin tabbatar da tsaro da dawowar jama'a ga gidajensu.

Asali: Twitter
Filato: Plang ya nemi taimakon NEMA
Sanata Plang ya ce zai yi amfani da matsayinsa wajen bin kafa a duk inda ya kamata don ganin al'ummar Filato ta Tsakiya ta samu salama daga 'yan ta'adda.

Kara karanta wannan
Davido: Mawakin Najeriya ya yi auren kece raini, ya kashe sama da Naira biliyan 5
"Ina jajantawa mutanen Mushere, shugabannin Bokkos da gwamnatin Filato bisa wadannan hare-hare da suke faruwa.
"Ina kira ga hukumar NEMA, Red Cross da duk hukumomin da abin ya shafa da su kai daukin kayan jin-kai ga wadanda harin 'yan bindiga ya shafa."
- Sanata Diket Plang.
Mutfwang ya yi tone-tone kan matsalar tsaro
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Gwamna Caleb Mutfwang ya bayyana cewa rikicin da ke faruwa a jihar Filato ba faɗan manoma da makiyaya ba ne.
Mutfwang ya ce wasu ɓata gari ne a gefe, suke kitsa duk wannan kashe-kashen da ke faruwa domin hana jihar Filato zaman lafiya.
Gwamnan ya tabbatar wa al'umma cewa da ikon Allah, gwamnati da hukumomin tsaro za su shawo kan lamarin kuma zaman lafiya zai dawo.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng