Jiragen Sojojin Sama Sun Saki Bama Bamai a Dajin Zamfara, An Hallaka Miyagu 100

Jiragen Sojojin Sama Sun Saki Bama Bamai a Dajin Zamfara, An Hallaka Miyagu 100

  • Sojojin Najeriya sun kashe fiye da ’yan bindiga 100 a dajin Makakkari da ke jihar Zamfara a wani harin sama da ƙasa da aka kai
  • An gano ’yan ta’adda sama da 400 dauke da makamai sun taru a Makakkari don kai farmaki, amma sojoji suka dakile su
  • Rundunar Operation FANSAN YANMA ta ce za ta ci gaba da matsa lamba don murkushe ’yan bindiga da wadanda ke ba su tallafi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Zamfara - Sojojin Najeriya sun sake dakatar da wata babbar barazanar ‘yan bindiga a Arewacin ƙasar, inda suka kashe fiye da ‘yan ta’adda 100 a Zamfara.

An rahoto cewa sojojin sun yi luguden wuta ta sama da kuma hare-haren ƙasa kan 'yan bindigar a dajin Makakkari da ke ƙaramar hukumar Bukuyum.

Kara karanta wannan

'Yan sandan Kano sun fara binciken kisan 'ɗan fashi' bayan koken uwarsa

Sojojin sama sun yi ruwan bama bamai kan 'yan ta'adda a Zamfara, an kashe miyagu 100
Sama da 'yan bindiga 100 sun bakunci lahira yayin da sojojin sama suka sakar masu bama bamai a Zamfara. Hoto: @NigAirForce
Source: Twitter

Sojoji sun gano matattarar 'yan ta'adda

Rahoton Zagazola Makama ya bayyana cewa tsawon makonni, jami’an leƙen asirin rundunar Operation FANSAN YANMA suna bibiyar wani motsi da ba su saba gani ba a yankunan Sunke, Kirsa, da Barukushe — wuraren da ake yawan samun ‘yan bindiga.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bincike ya gano cewa sama da mayaƙa 400 dauke da makamai, waɗanda wasu fitattun shugabannin ‘yan ta’adda ke jagoranta, sun taru a dajin Makakkari da nufin kai farmaki a Nasarawan Burkullu, wani ƙauye a ƙaramar hukumar Bukuyum.

Majiyar tsaro ta bayyana cewa shirin farmakin na ‘yan ta’addan wani bangare ne na ramuwar gayya kan kashin da suka sha a baya a hannun jami’an tsaro da rundunonin haɗin gwiwa.

“Sun yi tunanin za su iya sake taruwa, su sake samun makamai, su kuma kaddamar da wani sabon hari. Sai dai ba su san cewa sun fada a tarkon da aka dana masu ba," inji majiyar.

Kara karanta wannan

Rundunar ƴan sandan Kano ta fara binciken kisan hadimin gwamna, sadiq Gentle

An jefawa 'yan bindiga bama bamai a Zamfara

An rahoto cewa sojoji sun fara tura jiragen leken asiri, wadanda suka yi shawagi a matatarar 'yan ta'addar tare da tabbatar da cewa sun wajen.

Daga nan ne aka tura jiragen yakin sojojin sama, inda suka sauke wa 'yan ta'addar ruwan bama bamai, wanda ya haddasa tashin wuta da turnukewar hayaki.

Majiyar tsaron ta ci gaba da cewa:

“Wasu daga cikin shahararrun shugabannin ‘yan bindiga da mayakansu sun mutu kafin ma su sami damar harba harsashi. Waɗanda suka yi ƙoƙarin gudu kuma suka gamu da ajalisuna hannun dakarun sojin ƙasa."

An ce baya ga kashe daruruwan 'yan ta'adda, an kuma lalata daruruwan baburansu da suke amfani da su matsayin abin sufuri wajen kai hare-hare.

An ce sojojin sama sun yi luguden wuta kan 'yan ta'addan sannan sojin kasa suka kashe masu niyyar tserewa
Jiragen yakin sojojin sama suna hanyar kai farmaki kan 'yan ta'adda. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Alwashin da sojoji suka ci kan 'yan ta'adda

Majiyar ta kara da cewa abin da ya sa wannan farmaki ya zama na musamman shi ne yadda aka samu haɗin kai sosai tsakanin sojojin sama da na ƙasa.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: 'Yan bindiga sama da 200 sun farmaki ofishin 'yan sanda a Kwara

Rundunar Operation FANSAN YANMA ta sha alwashin ci gaba da matsa lamba, ba wai kawai kan ‘yan bindigar da ke cikin daji ba, har ma da hanyoyin da suke samun tallafi.

Majiyar ta ce:

“‘Yan indiga na samun karfi ne daga fargaar da suke dasawa mutane da rashin hukunta su da ake yi. Amma komai na canjawa yanzu, muna murkushe su daya bayan daya."

An kashe 'yan ta'adda 30 a Rann

A wani labarin, mun ruwaito cewa, sojoji sun dakile harin ‘yan ta’adda a garin Rann, bayan kazamin artabu da ya yi sanadin mutuwar miyagu da dama.

Air Commodore Ehimen Ejodame ya ce bayanan ISR da hare-haren sama sun taimaka wajen dakile mummunan shirin 'yan ta'addan.

A cewar rundunar sojin NAF, an gano shirin 'yan bindigar na kai hari kan dakarun sojin kasa da ke Rann, kuma an yi nasarar kakkabe su,

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com