Hukumar Sojin sama ta samu sabon jirgin yaki ATR-42 na leken asiri (Hotuna)
Hukumar mayakan saman Najeriya ta samu sabon jirgin yakin leken asiri mai suna ATR-42 a ranar Juma'a, 3 ga watan Yuli, 2020.
Mai magana da yawun hukumar, Ibikunle Daramola, ya bayyana hakan ne a jawabin da ya saki a shafin yanar gizo.
Jawabin yace: "Bisa ga cigaba da kokarin tabbatar da cewa ana samun labaran leken asiri domin yakin yan ta'adda a yan tada zaune tsaye a fadin tarayya, hukumar Sojin Najeriya a yau 3 ga Yuli, 2020, ta samu sabon gyararren jirgi, ATR-42 (NAF 930)."
"Shugaban shirye-shiryen hukumar, AVM Oladayo Amao ya karbi sabon jirgi madadin babban hafsan hukumar, AM Sadiqque Abba, a tashar jirgin saman Nnamdi Azikwe dake Abuja yayinda shi babban hafsan yake Arewa maso gabas domin lura ga atisayen Operation LONG REACH II."
"Sauran wadanda suka hallaci taron sun hada da shugaban ayyukan hukumar, AVM Ayoola Jolasimi; diraktan ayyukan injiniyanci, AVM Isah Muhammad da kwamandan 307 EAG, Air Commodore Francis Edosa.
An sabunta jirgin ne a a kamfanin Rheinland Air Services (RAS) dake Monchengladbach, kasar Jamus bayan ta an kwashe sa'o'i 5,000 a sama."

Asali: Facebook

Asali: Facebook

Asali: Facebook

Asali: Facebook
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng