"Ka Saki Kanu," Tsohon Ɗan Majalisa Ya Fadawa Tinubu Sirrin Samun Kuri'u a 2027
- Tsohon ɗan majalisar Legas, Jude Idimogu, ya roƙi Shugaba Bola Tinubu da ya yi wa jagoran IPOB, Nnamdi Kanu afuwa
- Idimogu ya ce sakin Kanu zai rage tashin hankali a Kudu maso Gabas, zai dawo da kasuwanci da zaman lafiya a yankin
- Idan aka yi wa Nnamdi Kanu afuwa, dan majalisar ya shaida cewa Tinubu zai samu ruwan kuri'u a Kudu maso Gabas a zaben 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Legas - Tsohon ɗan majalisar dokokin jihar Legas daga 2015 zuwa 2023, Jude Idimogu, ya roƙi Shugaba Bola Tinubu da ya yi afuwa ga shugaban ƙungiyar IPOB, Nnamdi Kanu.
An kama Nnamdi Kanu, wanda ke jagorantar ƙungiyar fafutukar kafa kasar Biafra a Nairobi, Kenya, a 2021, aka kawo shi Najeriya, inda yake a tsare tun daga lokacin.

Kara karanta wannan
Minista ya kwadaitawa Ibo mulkin Najeriya, ya ce taimakon Tinubu zai kai su Aso Rock

Asali: Facebook
An fadawa Tinubu sirrin Kudu maso Gabas
Idimogu, a hira da kamfanin NAN a ranar Lahadi a Legas, ya ce sakin Kanu zai taimaka wa APC mai mulki a yankin Kudu maso Gabas yayin da ƙasar ke tunkarar zaɓen 2027.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Zai ƙara mana ƙuri’u a Kudu maso Gabas. Idan shugaban kasa zai duba batun nan, Kudu maso Gabas ba za ta taɓa mantawa da shi ba, za ta zama mai masa biyayya har abada,” in ji shi.
Ya yi kira ga ’yan Najeriya masu kishin ƙasa, ciki har da shugabannin Igbo da gwamnonin Kudu maso Gabas, da su yi magana da murya ɗaya wajen roƙon Tinubu ya yi wa Kanu afuwa.
Ana so Tinubu ya saki Nnamdi Kanu
Tsohon ɗan majalisar ya ce irin wannan afuwa idan aka yi ya, ba za a manta da ita ba, kuma za ta ƙara wa jam’iyyar APC rinjaye a Kudu maso Gabas a zaɓen 2027.

Kara karanta wannan
2027: Yadda aka samu shugabanni 2 ko fiye a ADC da wasu jam'iyyun adawa a Najeriya
Jude Idimogu ya ce:
“Ina so in roƙi shugabanmu, Asiwaju Bola Tinubu, da ya duba muhimmancin amfani da hanyar siyasa wajen yi wa Nnamdi Kanu afuwa.
“Ina roƙon ’yan Najeriya masu kishin ƙasa, har wadanda ba ’yan asalin Igbo ba, su taimaka su roƙi shugaban kasa ya yi amfani da kujerarsa wajen sakin Nnamdi Kanu.
“Idan an yi haka, na yi imanin matsalar tsaro da tashin hankali a Kudu maso Gabas za su ragu, ko ma a shawo kansu gaba ɗaya.”
A cewarsa, mutane da dama marasa gaskiya suna amfani da sunan Kanu wajen tayar da hankula da aikata laifuka a yankin.

Asali: Twitter
An fadawa Tinubu amfanin sakin Kanu
Idimogu, wanda shi ne mataimakin jagoran Ndigbo a jam’iyyar APC ta jihar Legas, ya ce sakin Nnamdi Kanu zai kawo fa’ida mai yawa ga Kudu maso Gabas da Najeriya baki ɗaya.
Ya ce hakan zai rage tashin hankali kuma ya farfaɗo da tattalin arziƙin yankin, inji rahoton Punch.

Kara karanta wannan
APC ta yi watsi da kalaman El Rufai, ta fadi dalilin da zai sa Tinubu yin tazarce a 2027
“Shugaban kasa, ka duba halin da Kudu maso Gabas ke ciki ka farfado da harkokin kasuwanci da suka daɗe suna durƙushewa a yankin saboda matsalar tsaro.
“Kudu maso Gabas a da gida ne ga mutane da dama, amma yanzu ta zama mafakar masu kawo matsalar tsaro da sauran munanan ayyuka. Za a iya magance hakan idan aka saki Kanu.
“Shugaban kasa, mun san kai uba ne mai zuciyar tausayi, don Allah, ka taimake mu a Kudu maso Gabas, ka ba Kanu ’yanci ko yankinmu ya samu salama."
- Hon. Jude Idimogu.
Gwamnonin Kudu sun yi matsaya kan Kanu
A wani labarin, mun ruwaito cewa, kungiyar gwamnonin Kudu maso Gabas sun gana a jihar Enugu domin tattaunawa kan batutuwan da suka shafi yankin na su.
Gwamnonin a yayin ganawar ta su sun cimma matsayar za su gana da shugaban ƙasa kan ƙalubalen matsalar rashin tsaron da ke addabar yankin.
Sun kuma yanke shawarar cewa za su buƙaci a saki shugaban ƙungiyar IPOB, Nnamdi Kanu wanda ke fuskantar tuhumar ta'addanci a gaban kotu.
Asali: Legit.ng