Ranar Lahadi: Mamakon Ruwan Sama Zai Haddasa Ambaliya a Katsina, Neja da Jihohi 12

Ranar Lahadi: Mamakon Ruwan Sama Zai Haddasa Ambaliya a Katsina, Neja da Jihohi 12

  • NiMet ta yi hasashen ruwan sama mai yawa a jihohin Arewa, ciki har da Sokoto, Kebbi, Adamawa, Taraba, Kano, Kaduna da Jigawa
  • Hukumar ta ce za a iya samun ambaliya a Katsina, Zamfara, Sokoto, Kebbi, Plateau, Nasarawa, da Niger, da yammacin Lahadi
  • A Kudancin Najeriya, jihohin Delta, Imo, Bayelsa, Rivers, Cross River da Akwa Ibom za su iya fuskantar ambaliya a wannan rana

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Yayin da aka cinye rabin ranar Lahadi, 10 ga Agusta, 2025, hukumar NiMet ta yi hasashen cewa mamakon ruwan sama zai jawo ambaliya a wasu jihohi a yau din.

Kamar yadda ta saba, hukumar NiMet ta fitar da hasashen yanayin ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a daren ranar Asabar, wadda Legit Hausa ta gani.

Kara karanta wannan

An yi rashi a Najeriya, babban Sarki ya yi bankwana da duniya yana da shekaru 82

Ana fargabar ambaliya za ta afku a jihohin Katsina, Kebbi, Neja da sauransu
Ambaliya ta cinye wasu gidaje a Arewacin Najeriya. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

A cikin sanarwar da aka wallafa a shafinta na X, hukumar da ke hasashen yanayin ta kasa ta ce akwai jihohin Arewa bakwai da ambaliya za ta iya shafa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jihohin Arewa 7 da ambaliya za ta shafa

A safiyar Lahadi, hukumar NiMet ta hasasho cewa za a samu ruwan sama mai yawa a sassan jihohin Sokoto, Kebbi, Adamawa, da kuma Taraba.

A yammacin ranar, NiMet ta ce za a samu ruwan sama hade da tsawa a sassan jihohin Bauchi, Borno, Kaduna, Kano, Jigawa, Taraba, da Adamawa.

A wannan gabar ne hukumar NiMet ta ce wasu yankuna na jihohin Katsina, Kebbi, Zamfara, da Sokoto za su iya fuskantar ambaliyar ruwa.

Ambaliyar ruwa a jihohin Arewa ta Tsakiya

A Arewa ta Tsakiya kuwa, hukumar ta ce za a samu ruwan sama ne a jihar Neja kadai, yayin da hadari zai iya haduwa a sauran jihohin shiyyar.

Kara karanta wannan

Davido: Mawakin Najeriya ya yi auren kece raini, ya kashe sama da Naira biliyan 5

Amma da yammacin ranar, NiMet ta ce babban birnin tarayya Abuja da jihohin Plateau, Niger, Nasarawa, Benue, da Kogi States za su samu ruwan sama.

A wannan shiyyar ma, hukumar hasashen yanayin ta ce za a iya samun ambaliyar ruwa a jihohin Plateau, Nasarawa da Niger.

Hasashen NiMet a Kudancin Najeriya

Yayin da ta leka shiyyar Kudancin Najeriya, hukumar NiMet ta ce za a samu ruwan sama a safiyar Lahadi a jihohin Ebonyi, Cross River, da Akwa Ibom.

Ana hasashen jihohin Arewa da Kudu 16 za su gamu da ambaliya a ranar Lahadi
Jami'an ba da agaji na kokarin ceto wadanda suka makale a ambaliyar da ta afkuwa a wani gari. Hoto: Sani Hamza/Staff
Source: Original

Hakazalika, za a samu ruwan sama marar karfi a jihohin Enugu, Edo, Ebonyi, Ekiti, Osun, Abia, Cross River, Rivers, Delta, da Akwa Ibom.

NiMet ta yi hasashen cewa jihohin Delta, Imo, Bayelsa, Rivers, Cross River, da Akwa Ibom za su iya gamu wa da ambaliya a wannan rana.

Shawarwarin NiMet ga jama'a

Hukumar NiMet ta shawarci wadanda ke zaune a yankunan da suka saba fuskantar ambaliya da su dauki matakin gaggawa ko su kaura daga wuraren.

An kuma shawarci hukumomi da jami'an al'umma da ma masu ruwa da tsaki su zama a cikin shirin ko ta kwana na yiwuwar ambaliya a wannan rana.

Kara karanta wannan

Najeriya ta yi babban rashi, tsohon ministan Buhari, Audu Ogbeh ya rasu

Ambaliya ta cinye gidaje a jihohin Arewa

A wani labari, mun ruwaito cewa, ruwan sama ya jawo rushewar gidaje da cinye gonaki a Bauchi, Filato da Neja wanda ya tilasta mutane yin kaura.

A jihar Filato, sama da gidaje 50 da makarantu da majami’a sun rushe yayin da guguwar ta kakkarya bishiyoyi, ta fasa turakun wuta.

A Bauchi da Neja, ambaliya ta cinye gonaki da dama, inda hukumar SEMA ta sanar da shirin fara kai tallafi ga wadanda abin ya shafa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com