Tirkashi: ASUU na Barazanar Rufe Jami'o'in Najeriya saboda Yunwa da Wasu Dalilai

Tirkashi: ASUU na Barazanar Rufe Jami'o'in Najeriya saboda Yunwa da Wasu Dalilai

  • Kungiyar ASUU ta yi barazanar shiga yajin aiki, tana cewa malamai na koyar da dalibai cikin yunwa da rashin kayan aiki
  • Malaman jami'o'in sun yi nuni da cewa suna koyarwa cikin matsin rayuwa na biyan kudaden wuta, haya, da karatun yara
  • Kungiyar ta zargi gwamnati da gaza sabunta yarjejeniyar 2009, tana mai cewa hakan ya haifar da tabarbarewar harkar ilimi

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Kungiyar malaman jami’o’i ta Najeriya (ASUU) ta yi gargadin yiwuwar shiga yajin aiki saboda gazawar gwamnati na cika alkawuran da ta dauka.

Barazanar tsunduma yajin aikin na zuwa ne yayin da ASUU ta bayyana cewa malamai na koyar da dalibai cikin yunwa, saboda rashin wadataccen albashi da alawus.

ASUU ta yi barazanar shiga yajin aiki saboda gwamnati ta gaza cika mata alkawurra
Shugabannin ASUU sun yi barazanar shiga yajin aiki a fadin kasar nan. Hoto: @ASUU_UNILAG
Asali: Twitter

ASUU ta nemi gwamnati ta dauki mataki

Kara karanta wannan

Ana batun yunwa, gwamnatin Tinubu ta fitar da ton 42,000 na hatsi a raba wa jihohi

ASUU ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da shugaban ta na kasa, Farfesa Chris Piwuna, ya sanya wa hannu a ranar Asabar, a cewr rahoton Arise News.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta bayyana cewa yanzu ASUU ta kai wuya, tana mai kira ga gwamnati da ta dauki mataki nan da nan don kauce wa yajin aikin da ke tunkaro jami’o’in gwamnati.

Kungiyar ta ruwaito wasu kalaman ministan ilimi, Dakta Tunji Alausa, da ya ce “ASUU ko wata kungiya ta manyan makarantu, malamai ko kwararru ba za su kara shiga yajin aiki ba.”

A cewar ASUU, Alausa ya danganta wannan ikirarin nasa da dabarar gwamnati ta “tattaunawa da kungiyoyin ma'aikata da kuma kyautata alaka da shugabannin kungiyoyin."

ASUU ta ce duk da cewa maganarAlausa na kan hanya, amma lokaci ya yi da gwamnati za ta magance matsalolin malamai ba wai a tsaya ana ta mayar da yadda aka yi ba.

Kara karanta wannan

Shiri ya baci: 'Yan bindiga sun yi wa sojoji kwanton bauna, an samu asarar rayuka

Dalilan da za su sanya ASUU shiga yajin aiki

Jaridar Punch ta rahoto sanarwar kungiyar ASUU ta ce:

“Rahotanni daga jami’o’i sun nuna cewa malamai a jami’o’in gwamnati na koyar da dalibai cikin yunwa.
“Suna gudanar da bincike a dakunan karatu da dakunan gwaje-gwaje marasa muhimman mujallu, littattafai ko takardun ilimi na zamani, sannan babu sinadarai da kayayyakin gwaji.
"Suna hawan tsofaffin motoci, ga biyan kudin wuta da tsada, kudin makarantar yara ma na son ya gagare su balle a yi maganar kudin hayar gida, kula da iyali da sauran nauyukan rayuwa.
“Duk da haka, wasu na korafin wai jami'o'i na yaye daliban da ba su da kwarewa a fannonin da suka karanta, alhalin ana yiwa malamai rikon sakainar kashi don a tozarta su."
ASUU ta ce gwamnatin tarayya ta ki cika alkawuran da ta daukar mata, don haka za ta shiga yajin aiki
Kungiyar ASUU ta fadawa gwamnatin Bola Tinubu dalilan da za su sanya ta shiga yajin aiki. Hoto: @ASUU_UNILAG, @officialABAT
Asali: Facebook

An bukaci gwamnati ta cikawa ASUU alkawari

ASUU ta ce ta sha gargadin gwamnati ta tarayya da ta jihohi kan illar kin mutunta ma’aikatan ilimi da tauye hakkokinsu, domin hakan zai kashe gwiwarsu, ya raunana ilimi.

Kara karanta wannan

Wata matsala ta tunkaro Najeriya, za a iya rasa Naira tiriliyan 1.6 duk shekara

"Rikon sakainar kashi da gwamnatocin baya suka yi na cika alkawuran da suka daukarwa malaman jami'o'i ya haifar da yanayin rashin amana da tangarda ga ilimi, wanda ya kamata wannan gwamnati ta gyara.
“Babu abin da ya fi damunmu kamar yadda aka gaza sabunta yarjejeniyar gwamnati da ASUU ta 2009, duk da an mika wa gwamnati kudirin yarjejeniyar daga kwamitin Alhaji Yayale Ahmed tun watan Disamba 2024, watanni takwas cif da suka gabata."

- Farfesa Chris Piwuna.

Kungiyoyin jami'a sun shiga yajin aiki

A wani labarin, mun ruwaito cewa, kungiyoyin ASUU, SSANU, NASU da NAAT sun shiga yajin aikin sai baba-ta-gani a jami’ar LASU daga Alhamis, 31 ga Yuli, 2025.

An umarci malamai da ma’aikata da su janye daga aiki a LASU, LASUCOM-Ikeja da sashen Epe har sai an biya bukatun kungiyoyin.

Bukatun sun hada da karin albashi, daidaita albashi da na sauran makarantu da kuma aiwatar da sabon mafi karancin albashi kamar yadda rahoton ya nuna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.