Danwawu: Abba Ya Fatattaki Hadimi a Kano saboda Hannu a Belin Dilan Kwaya

Danwawu: Abba Ya Fatattaki Hadimi a Kano saboda Hannu a Belin Dilan Kwaya

  • Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya sallami manyan hadimai biyu saboda zargin hannu a karbo belin dilan dan kwaya da karkatar da tallafi
  • A kwanakin baya ne dai aka samu badakalar da ke zargin wani jami'in gwamnatin Kano da karbo Suleiman Danwawu daga hannun hukuma
  • Lamarin ya jawo gwamna Abba Kabir Yusuf ya samar da kwamitin da ya gano masa hannu a batun tare da daukar mataki a kansu

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Gwamnatin jihar Kano karkashin Injiniya Abba Kabir Yusuf ta amince da korar manyan hadimai biyu na musamman (SSAs).

Gwamnan ya dauki matakin ne bayan samun sakamakon bincike da kwamitoci daban-daban su ka yi tare da alakanta su da hannu a belin dilan kwaya a Kano, Suleiman Danwawu da karkatar da tallafi.

Kara karanta wannan

Kungiyar gwamnoni ta zabi gwamna 1 da ya fi kowa kokari a 2025

Gwamnatin Kano ta fusata
Gwamnan Kano ya kori hadimansa 2 Hoto: Sanusi Bature D Tofa
Asali: Facebook

Wannan na kunshe ne a wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Umar Farouk Ibrahim, ya fitar da Sanusi Bature Dawakin Tofa ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Asabar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Abba Kabir ya sallami hadimai 2 a Kano

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da korar Abubakar Umar Sharada, Mai Bai wa Gwamna Shawara ta Musamman kan Wayar da Kan Jama’a a Siyasa.

Sanarwar ta ce sakamakon binciken kwamiti na musamman ya tabbatar da cewa shi ne ya jagoranci belin shahararren dillalin miyagun kwayoyi, Sulaiman Aminu Danwawu.

Rahoton kwamitin ya tabbatar da cewa Abubakar ya amsa da kansa a gabansu cewa yana da hannu a belin, wanda hakan ya tabbatar da laifinsa.

A wata wasika da Sakataren Gwamnatin Jihar ya aika masa a ranar Juma’a, 8 ga watan Agusta 2025, an umarci Abubakar ya ajiye aiki.

An kuma umarce shi ya mika kadarorin gwamnati da ke hannunsa ga Ofishin SSG kafin karshen ranar Litinin, 11 ga watan Agusta 2025.

Kara karanta wannan

Bayan bidiyon Dan Bello, Gwamna Abba Yusuf ya kwace kwangilar aikin titi a Kano

Haka kuma an gargade shi da kada ya ci gaba da kiran kansa jami’in gwamnati bayan korar shi da aka yi.

Abba ya yi kora saboda karkatar da tallafi

Haka kuma gwamnan ya sallami Tasiu Adamu Al’amin Roba, Mai Bai wa Gwamna Shawara ta Musamman a Ofishin Majalisar Zartarwa.

An kore shi bayan kama shi a shekarar 2024 da sake mazubin tallafin hatsi a wani rumbun ajiya da ke Sharada.

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf
Gwamna ya ja kunnen hadimansa Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

An gurfanar da Roba a kotu, kuma yana fuskantar tuhuma kan sata da hada baki wajen karkatar da dukiyar gwamnati.

Sanarwar ta ce gwamnati ta umarce shi ya mika kadarorin gwamnati da ke hannunsa, ciki har da katin shaidar aiki, kafin Litinin, 11 ga watan Agusta 2025.

Haka kuma an gargade shi da kada ya ci gaba da kiran kansa jami’in gwamnati.

Gwamnan Kano, Abba ya wanke hadiminsa

A wani lamari dabam, gwamnatin Kano ta wanke Hon. Musa Ado Tsamiya, Mai Bai wa Gwamna Shawara kan Magudanan Ruwa, bayan kwamiti ya tabbatar da cewa bai da laifi a kan duk wata tuhuma da ake yi masa.

Kara karanta wannan

Abba ya yi magana a fusace bayan 'yan daban Kano sun yi ajalin hadiminsa

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya jaddada kudirin gwamnatinsa na ci gaba da rikon gaskiya, tare da cewa ba zai sassauta wa cin hanci da yaki da ta'ammali da kwayoyi ba.

Ya gargadi dukkanin jami’an gwamnati da su rike mutuncin aiki a kowane lokaci.

Kwamishina ya yi murabus a jihar Kano

A baya, kun ji cewa kwamishinan sufuri na jihar Kano, Ibrahim Ali Namadi, ya ajiye aikinsa sa’o’i kaɗan bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf ya karɓi rahoto kan zarginsa da belin dilan kwaya.

Sanarwar da hadimin gwamna, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar ta ce kwamishinan ya yi murabus don nuna jajircewar gwamnatin jihar wajen bin gaskiya da adalci a ayyukanta.

Namadi ya yi godiya ga Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa damar da ya ba shi na yi wa jihar hidima, tare da tabbatar da biyayyarsa ga manufofin kyakkyawan shugabanci da rikon amana.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.