Da Gaske Yan Sanda Sun Karya Hannun Sowore? An Samu Bayanai kan Zargin

Da Gaske Yan Sanda Sun Karya Hannun Sowore? An Samu Bayanai kan Zargin

  • ‘Yan sanda sun musanta cewa sun karya hannun Omoyele Sowore ko sun azabtar da shi, sun ce kama da tsarewar sa ta halasta ce
  • Sowore ya ce an tsare shi ba bisa ka’ida ba, yana kuma zargin an buge shi yayin da yake hedikwatar ‘yan sanda a Abuja
  • Rundunar ‘yan sanda ta ce an saki Sowore cikin awanni 48 da doka ta tanada, kuma yana fuskantar shari’a kan zargin jabun takardu da cin zarafi

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Rundunar ‘Yan Sanda ta Najeriya ta yi karin haske kan zargin cin zarafin dan gwagwarmaya, Omoyele Sowore a Abuja.

Rundunar ta musanta zargin cewa ta azabtar da mai gidan jaridar Sahara Reporters, Sowore har da karya masa hannu.

Yan sanda sun musanta cin zarafin Sowore
Rundunar yan sanda ta bayyana abin da ya faru da Sowore. Hoto: Omoyele Sowore.
Source: Twitter

Kakakin rundunar, Olumuyiwa Adejobi ya bayyana haka a Facebook cewa an kama shi bisa zargin jabun takardu, cin zarafi ta kafofin sadarwa, da wasu laifuka.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun tare matafiya a hanya, an yi awon gaba da fasinjoji

‘Yan sanda sun ce an kama Sowore kuma an sake shi bisa beli cikin awanni 48 da kundin tsarin mulki ya tanada, ba tare da tauye masa hakki ba.

Sowore ya yi magana bayan an sake shi

Sowore ya tabbatar da sakin nasa a shafin Facebook, inda ya kira tsarewar tasa “ba bisa ka’ida ba kuma rashin adalci.”

A wani bidiyo, Sowore ya yi ikirarin cewa an karya masa hannu, kuma ba a kawo masa likita ba, sai jinya kawai.

Ya kuma zargi ‘yan sanda da kawo ‘yan jarida maimakon likita yayin da ake tsare da shi a Abuja.

Yan sanda sun bayyana gaskiya kan zaman Sowore a wurinsu
Yan sanda sun musanta cin zarafin Sowore. Hoto: Nigeria Police Force.
Source: Facebook

Martanin yan sanda kan sakin Sowore

Kakakin rundunar, Olumuyiwa Adejobi, ya ce wannan zargi karya ne don bata sunan rundunar da shugabancinta.

Ya ce an kama Sowore ne bisa bayanan sahihai na laifukan da ake masa bincike.

Adejobi ya kara da cewa an samu umarnin kotu kafin tsare shi, kuma an sanar da shi dalilin kama shi.

Kara karanta wannan

An kama boka mai ba 'yan ta'adda maganin bindiga da kayan tsafi

Game da hoton da ya nuna Sowore da bandeji, ‘yan sanda sun ce daman da bandeji ya je ofishinsu tun kafin kama shi.

Duk da haka, Sufeto-janar na yan sanda ya umarci a gudanar da bincike kan yadda ya samu damar sa bandeji a tsare.

Rundunar ta ce ta tura kwararrun likitoci biyu daban-daban a ranar 7 da 8 ga Agusta 2025 domin duba lafiyarsa, amma ya ki amincewa da gwajin, wannan kin amincewa an rubuta shi a hukumance.

‘Yan sanda sun jaddada cewa tsarewar tasa ta yi daidai da doka, babu wata manufa ta siyasa.

Sun roki kafafen yada labarai su guji yada labarin da zai rage amincewar jama’a ga binciken da ake gudanarwa.

Ana zargin yan sanda sun raunata Omoyele Sowore

Kun ji cewa rahotanni na nuni da cewa yan sanda sun ji wa Omoyele Sowore rauni bayan daga tsare shi da aka yi.

Sowore ya zargin yan sanda a cin zarafinsa wanda ya ce hakan bai da dalili kuma ba bisa doka aka yi ta ba.

Ya bayyana cewa ‘yan sanda sun karya masa hannu tun lokacin da aka kama shi, kuma ba a kawo masa likita ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.