Tashin Hankali: 'Yan Bindiga Sama da 200 Sun Farmaki Ofishin 'Yan Sanda a Kwara

Tashin Hankali: 'Yan Bindiga Sama da 200 Sun Farmaki Ofishin 'Yan Sanda a Kwara

  • 'Yan bindiga 200 dauke da makamai sun kai farmaki garin Babanla, jihar Kwara, inda suka kashe dan sanda tare da kwace bindigarsa
  • ASP Adejumo Wasiu ya rasa ransa a harin da 'yan ta'addar suka kai ofishin ‘yan sanda na Babanla, kafin su farmaki kasuwar garin
  • A wani hari daban a garin Ipelle, 'yan bindiga sun kashe wani sufetan 'yan sanda da farar hula a harin da suka kai jihar Benue

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kwara – Wasu ‘yan bindiga da yawansu ya kai 200, dauke da makamai, sun yi wa garin Babanla na jihar Kwara dirar mikiya a kan babura a ranar Juma'a.

A yayin wannan mummunan harin da ya faru da misalin ƙarfe 1:00 na rana, 'yan bindigar sun kashe ɗan sanda ɗaya kuma suka fasa wata kasuwa.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun tare matafiya a hanya, an yi awon gaba da fasinjoji

'Yan ta'adda sun farmaki ofishin 'yan sanda a Kwara, sun kashe jami'i tare da sace bindigarsa
Gwamnati ta ba rundunar 'yan sanda kyautar sababbin motoci domin inganta tsaro. Hoto: @ubasanius
Source: Twitter

Kwara: 'Yan bindiga sun kashe dan sanda

Zagazola Makama ya tattaro cewa maharan, waɗanda suka bude wuta kan mai uwa da wabi, sun kai farmaki ofishin ‘yan sandan Babanla.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A harin ne ASP Adejumo Wasiu, wanda ke ƙarƙashin ACPOL Offa, ya rasa ransa bayan harbin da aka yi masa, kuma maharan suka tafiya da bindigarsa kirar AK-47.

Majiyoyi sun ce 'yan ta'addar sun yi kaca-kaca da ofishin ‘yan sandan, amma ba su samu ƙarin makamai ba saboda jami'ai sun fita aiki da sauran bindigogin.

'Yan bindiga sun farmaki kasuwar Kwara

Bayan farmakin ofishin ‘yan sandan, ‘yan bindigar sun nufi kasuwar garin, inda suka kwashe kayayyakin abinci masu yawa.

Jami’an tsaro na haɗin gwiwa, da suka haɗa da sojoji, ‘yan sanda, 'yan banga da mafarauta sun hanzarta kai dauki, inda suka kori maharan tare da dawo da zaman lafiya yankin.

Har zuwa wallafa wannan rahoton, ba a iya gano adadin wadanda aka kashe a wannan harin ba baya ga shi dan sandan da aka tabbatar da mutuwarsa.

Kara karanta wannan

Masu sayar wa ƴan ta'adda bindigogi sun gama guje guje, sun shiga hannu a Kaduna

'Yan bindiga sun farmaki jihar Benue

A wani harin na daban, wani sufetan ‘yan sanda da wani farar hula sun rasa rayukansu bayan wani harin 'yan bindiga a ƙauyen Ipelle na ƙaramar hukumar Agatu a jihar Benue.

'Yan sanda sun kashe dan sanda da farar hula a harin da suka kai Benue
Shugaban rundunar 'yan sandan Najeriya, IGP Kayode Egbetokun. Hoto: @PoliceNG
Source: Facebook

Majiyoyin da suka tabbatar da lamarin sun bayyana cewa marigayi, Insp. Daniel Omanyebu, yana aiki ne a ofishin ‘yan sanda na Ipelle ƙarƙashin sashen Agatu.

Bayan samun rahoton gaggawa, sassan rundunar ‘yan sanda, ciki har da Operation Zenda, rundunar PMF, sashen CTU, da tawagar sintiri sun garzaya wajen.

An ce an dauko gawar sufetan zuwa dakin ajiye gawa, yayin da ake ci gaba da kokarin kamo waɗanda suka aikata laifin.

Sashen binciken manyan laifuffuka na jihar (CID) ya karɓi ragamar gudanar da binciken bisa umarnin kwamishinan 'yan sandan jihar.

An kama masu safarar bindigogi a Kaduna

A wani labarin, mun ruwaito cewa, ‘yan sandan Kaduna sun cafke mutane biyu a Kurmin-Kogi, bisa zargin saye da sayar da bindigogi ga 'yan ta'adda.

Kara karanta wannan

Sojojin saman Najeriya sun yi ruwan wuta a garin Raan, an rasa rayukan ƴan bindiga 30

Wadanda ake zargi, Isah Bello da Sa’idu Haruna, sun kai jami’an tsaro mabuyarsu a cikin daji inda aka gano bindigogi daban daban.

Rundunar 'yan sandan ta kuma ce ta yi nasarar kama wani barawon babura, wanda ya amsa cewa yana cikin ƙungiyar barayin babura da ke addabar Giwa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com