Wasu na Kiran Sulhu, Ƴan Bindiga Sun Hallaka Malamin Addini da Wasu Mutane

Wasu na Kiran Sulhu, Ƴan Bindiga Sun Hallaka Malamin Addini da Wasu Mutane

  • Yan bindiga sun kai hari kauyukan Suwa da Ding’ak a Mushere, Bokkos a jihar Plateau, inda suka kashe mutum uku
  • Kefas Mallai ya tabbatar da mutuwar Fasto Gideon Katings, Sunday Ringkang da Meshach Bukata, yayin da wasu suka ji rauni
  • Gwamna Caleb Mutfwang ya kira harin “kisan kiyashi” da yunƙurin kwace ƙasa, yana tabbatar da hadin gwiwa da jami’an tsaro

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Jos, Plateau - Yan bindiga sun sake kai hari kauyukan Suwa da Ding’ak a masarautar Mushere inda suka hallaka mutane uku.

Lamarin ya faru ne a karamar hukumar Bokkos da ke jihar Plateau, inda suka kashe mutanen ciki har da Fasto.

Yan bindiga sun hallaka Fasto a Plateau
yawanci Fasto da wasu mutum 3 a Plateau. Hoto: HQ Nigerian Army.
Source: Facebook

Plateau: Fasto ya mutu a harin 'yan bindiga

An gano cewa harin ya faru tsakanin ƙarfe 1:00 zuwa 2:00 na rana a ranar Juma’a, wanda ya haifar da mutuwar mutum uku, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Musulmai sun shiga fargaba a Spain bayan kawo dokokin da za su iya hana ibada

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban masu lura da zaman lafiya a Bokkos, Kefas Mallai, ya tabbatar da mutuwar Fasto Gideon Katings na COCIN Suwa, Sunday Ringkang da Meshach Bukata.

Ya ƙara da cewa wani Michael Kamshak da wasu da dama sun ji rauni kuma suna samun kulawa a Asibitin Cottage, Bokkos.

Mallai ya kuma tabbatar cewa daruruwan mazauna yankin sun tsere daga gidajensu sakamakon harin da aka kai musu a wannan rana.

Mallai ya ce:

"Tsakanin ƙarfe 1:00 da 2:00 yau Juma’a, 8 ga Agusta 2025, an kai wa Suwa da Ding’ak hari da ya hallaka mutum uku ciki har da Fasto Gideon Katings na COCIN Suwa.
"Sauran sun hada da Sunday Ringkang da Meshach Bukata; yayin da Michael Kamshak da wasu suka ji rauni kuma suna jinya a Asibitin Cottage Bokkos."
An rasa rayuka bayan harin yan bindiga a Plateau
Fasto da wasu mutum 3 sun mutu a harin yan bindiga. Hoto: Legit.
Source: Original

Wane martani rundunar yan sanda ta yi?

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Plateau, Alabo Alfred, bai samu damar magana ba, domin wayarsa na kashe lokacin kiran da yan jaridu suka yi masa.

Kara karanta wannan

Shiri ya baci: 'Yan bindiga sun yi wa sojoji kwanton bauna, an samu asarar rayuka

Kisan na ranar Juma’a shi ne na baya-bayan nan cikin jerin hare-haren yan bindiga da aka sha fuskanta a Bokkos da kewaye.

Shugaban karamar hukumar Bokkos, Amalau Samuel Amalau, ya bukaci jami’an tsaro su dauki matakin gaggawa don kare rayuka da hana ƙarin raba mutane daga gidajensu.

Gwamna Caleb Mutfwang ya yi tir da hare-haren da ake kaiwa, yana kiran shi da “kisan kiyashi” da kuma “yunƙurin kwace ƙasa cikin shiri na hadin gwiwa.”

Mai girma Gwamnan ya yi alkawarin yin aiki tare da jami’an tsaro don kamo masu laifi da tabbatar da tsaron rayukan mazauna yankin.

Yan bindiga sun yi ajalin manoma a Plateau

Mun ba ku labarin cewa wasu ƴan bindiga ɗauke da makamai sun yi ta'asa bayan sun kai harin ta'addanci a jihar Plateau.

Ƴan bindigan sun hallaka manoma maza da mata a mummunan harin wanda suka kai a ƙaramar hukumar Riyom ta jihar.

Harin ya kuma yi sanadiyyar raunata wasu mutanen masu yawa bayan da ƴan bindigan suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.