Bayan Bidiyon Dan Bello, Gwamna Abba Yusuf Ya Kwace Kwangilar Aikin Titi a Kano

Bayan Bidiyon Dan Bello, Gwamna Abba Yusuf Ya Kwace Kwangilar Aikin Titi a Kano

  • Gwamnatin Kano ta soke kwangilar titin Jaba-Gayawa tare da mayar da Dakata-Yadakunya zuwa hannu biyu, a kan kudi N6.1bn
  • Soke kwangilar ya biyo bayan bidiyon Dan Bello da ya nuna lalacewar titin, wanda ya jefa mazauna yankin cikin tsananin damuwa
  • Gwamna Abba Yusuf ya kuma amince da kashe N14.8bn kan ayyukan da suka hada da gyaran asibiti, makarantu da sauransu

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Gwamnatin Kano, karkashin mai girma Abba Kabir Yusuf ta kwace kwangilar aikin titin Jaba-Gayawa da ke cikin jihar.

Gwamna Abba Yusuf ya dauki wannan matakin ne a taron majalisar zartarwar jihar da aka gudanar a ranar Laraba, 6 ga Agusta, 2024.

Gwamnatin Kano ta soke kwangilar titin Jaba-Gayawa wanda Dan Bello ya yi bidiyo a kansa
Gwamna Abba Yusuf ya ba da kwangilolin gyaran tituna a sassan Kano. Hoto: @Kyusufabba/X
Source: Facebook

Abba ya soke kwangilar titin Jaba-Gayawa

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa kwamishinan watsa labarai na Kano, Ibrahim Wayya ya sanar da manema labarai wannan matakin.

Kara karanta wannan

Kanawa na cikin alheri, Tinubu zai musu jirgin kasa na Naira tiriliyan 1.5

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A yayin zantawarsa da manema labaran, Ibrahim Wayya ya ce an sake ba da kwangilar mayar da titin Dakata-Yadakunya(Bela) zuwa hannu biyu.

Ya ce an yanke shawarar mayar da shi hannu biyu bayan an soke kwangilar titin Jaba-Gayawa, kuma aikin zai lakume N6,147,010,996.10.

Majalisar zartarwar ta kuma amince kashe Naira miliyan 52 domin aikin gina titin Badgery-Yusuf wanda ke a karamar hukumar Nasarawa.

'Dan Bello ya yi bidiyo kan titin Gayawa

Soke kwangilar hanyar Jaba-Gayawa na zuwa ne 'yan kwanaki bayan fitaccen dan jarida, kuma mai kare hakkokin dan Adam, Bello Galadanchi (Dan Bello) ya yi bidiyo kan titin.

A cikin bidiyon, Dan Bello ya nuna yadda titin ya lalace, wanda har ta kai ruwa ya cinye wasu sassansa, tare da jefa al'ummar yankin cikin damuwa.

Dan Bello ya wallafa bidiyon a shafinsa na Facebook a ranar 31 ga Yulin 2025 inda ya yi kira ga gwamnatin Kano da ta dauki mataki kan masu aikin titin.

Kara karanta wannan

Gwamna ya amince a kashe N1bn a fannoni 3, za a sayo littattafan N588m a jihar Katsina

A ranar 8 ga watan Nuwamba, 2024 Gwamna Abba Yusuf ya sha alwashin magance matsalar zaizayar kasa a yankunan Bulbula-Gayawa da ke karamar hukumar Ungogo.

A Disambar 2024, gwamnan ya ba shirin ACReSAL aikin magance duk wata matsalar zaizayar kasa a jihar.

Majalisar zartarwar Kano ta amince a kashe N14.828bn domin aiwatar da manyan ayyuka a jihar.
Gwamnan Kano, mai girma Abba Kabir Yusuf a wani taro da aka gudanar a jihar. Hoto: @Kyusufabba (X)
Source: Facebook

Gwamnatin Kano za ta kashe N14.828bn

Bayan taron majalisar na ranar Laraba, kwamishinan watsa labaran, ya kuma ce an amince da kashe N14.828bn don aiwatar da manyan ayyuka a fadin jihar.

Daga cikin ayyukan akwai daga darajar gidan marayu na Gaya zuwa cibiyar bunkasa rayuwar mata tare da gina wata cibiya a Gaya kan kudi N1.34bn.

Kwamishinan watsa labarai ya kuma kara da cewa majalisar ta amince da gyarawa da kuma daga darajar asibitin haihuwa na Sabo Bakin Zuwo da ke Jakara a kan N364,508,253.28.

Majalisar ta kuma amince a kashe N294,469,189.83 don sabunta dukkanin kayayyaki da gine-ginen makarantar kimiyyar lafiya da ke Bebeji.

Abba ya kai ziyara makarantar sakandare

A wani labari, mun ruwaito cewa, gwamna Abba Kabir Yusuf ya ziyarci makarantar sakandaren jeka-ka-dawo ta Kano (KDSC) bayan bidiyon Ɗan Bello.

Kara karanta wannan

'Dan shekara 32 ya yi barazanar kashe gwamna, ya jefa kansa a babbar matsala

A cikin wani bidiyo da fitaccen dan jarida, Ɗan Bello ya fitar, ya kutsa lungu da saƙo na makarantar inda ya riƙa nuna yadda ta lalace.

Ziyarar Gwamna Abba Yusuf ta ja hankalin al'ummar Kano, daga ciki har da fitaccen lauya, Abba Hikima da ya yaba da salon mulkin gwamnan.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com