2027: Ana Shirin Tarwatsa Haɗakar Atiku da Peter Obi da Kujerar Minista Mai Tsoka

2027: Ana Shirin Tarwatsa Haɗakar Atiku da Peter Obi da Kujerar Minista Mai Tsoka

  • Ana zargin tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan ya fara ƙoƙarin janye Peter Obi daga haɗakar ƴan adawa domin ya mara masa baya
  • Dumebi Kachikwu ya yi ikirarin cewa Jonathan ya yiwa Peter Obi tayin kujerar minista mai gwaɓi domin ya janye masa takara a 2027
  • Ɗan takarar ADC a 2023 ya zargi Atiku da wasu manyan Arewa da ɓata sunan duka ƴan Kudu domin cimma burinsa na hawa mulki

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Dumebi Kachikwu, ya yi ikirarin cewa an fara yunkurun raba haɗakar Atiku Abubakar da Peter Obi.

Kachikwu ya ce tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, ya yi wa Mista Peter Obi, tayin kujerar ministan harkokin tattalin arziki idan ya janye daga takara, ya goyi bayansa.

Kara karanta wannan

Tinubu na tsaka mai wuya, PDP ta fara nuna wanda za ta tsayar takara a zaɓen 2027

Tsohon ɗan takarar shugaban kasa na ADC, Dumebi Kachikwu.
Kachikwo ya yi ikirarin Jonathan na kokarin janye Peter Obi daga haɗaka Hoto: Dumebi Kachikwu
Source: Facebook

Kachikwu ya yi wannan ikirari ne a wani taron manema labarai da ya gudanar a Abuja ranar Juma’a, 8 ga watan Agusta, 2025, cewar rahoton Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jonathan ya yiwa Peter Obi tayin kujera

Ya zargi cewa wasu ‘yan siyasa daga Arewa ne suka shigo da tsohon shugaban ƙasa Jonathan cikin takarar shugaban ƙasa domin raunana siyasar Kudu.

Kachikwu ya ƙara da cewa an shaida wa Obi cewa ba zai iya samun kuri’un Arewa ba saboda yana ɗan kabilar Ibo.

“Domin raunana Kudu, yanzu sun shigo da tsohon shugaban ƙasa Jonathan cikin fafatawar, wanda ake zargin ya yiwa Obi tayin kujerar ministan harkokin tattalin arziki domin ya mara masa baya," in ji shi.

Ya zargi tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, da wasu manyan Arewa da riƙe madafun iko tsawon shekaru ba tare da sun yi wani abu don rage jahilci da talauci a yankin ba.

Ana zargin Atiku da yaudarar ƴan Arewa

Kara karanta wannan

An yi hasashen yawan ƙuri'un da Shugaba Tinubu zai samu a zaɓen 2027

Har ila yau ya zargi manyan Arewa da amfani da makaman siyasa na yanki, addini, harshe, kabila da talauci, wajen sauya tunanin talakawan Arewa kan Tinubu.

A rahoton Daily Post, Kachikwu ya ce:

“Kullum suna yada ƙarya da gangan ba wai kawai kan Shugaba Tinubu ba, har ma da duk wani ɗan takara daga Kudu da zai iya neman kujerar shugaban ƙasa.
"An faɗa wa Peter Obi a fili cewa ba zai taɓa samun kuri’un Arewa ba saboda yana ɗan Ibo, saboda haka ya amince ya zama mataimakin Atiku.”
Jonathan da Peter Obi.
Jonathan ya yi tayin abin da zai iya raba Atiku da Peter Obi a haɗakar ADC Hoto: Getty Images
Source: Facebook

Kachikwu ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su yi watsi da Atiku da duk waɗanda ke tare da shi saboda ba sa ƙaunar a gina Najeriya kan turbar gaskiya da adalci.

Gwamna ya roƙi Peter Obi ya dawo PDP

A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Bala Mohammed na Bauchi ya roƙi tsohon ɗan takarar shugaban kasa, Peter Obi ya dawo jam'iyyar PDP,

Gwamna Bala, shugaban ƙungiyar gwamnonin jam'iyyar PDP, ya ce tsammanin da ‘yan Najeriya ke da shi game da zaɓen 2027 yana da yawa.

A cewarsa, lokaci ya yi da Obi zai dawo gidansa na asali watau PDP domin su haɗa kai wajen ceto ƙasar nan daga halik da ta shiga.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262