Sojojin Saman Najeriya Sun Yi Ruwan Wuta a Garin Raan, An Rasa Rayukan Ƴan Bindiga 30

Sojojin Saman Najeriya Sun Yi Ruwan Wuta a Garin Raan, An Rasa Rayukan Ƴan Bindiga 30

  • Sojojin saman Najeriya sun dakile harin ‘yan ta’adda a garin Rann, bayan kazamin artabu da ya yi sanadiyyar mutuwar miyagu da dama
  • Air Commodore Ehimen Ejodame ya ce bayanan ISR da hare-haren sama sun taimaka wajen dakile mummunan shirin 'yan ta'addan
  • A cewar rundunar sojin NAF, an gano shirin 'yan bindigar na kai hari kan dakarun sojin kasa da ke Rann, kuma an yi nasarar kakkabe su
  • Wannan na zuwa ne 'yan kwanaki bayan rundunar ta hallaka ‘yan ta’adda 30 lokacin da ta yi luguden wuta kansu a Zamfara

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Borno - Sojojin saman Najeriya (NAF) ta yi luguden wuta kan 'yan bindiga a jihar Borno wanda ya kai ga mutuwar mutane da dama.

Rundunar sojin sama da ke karkashin Operation Hadin Kai (OPHK), ne suka kaddamar da harin a garin Rann, iyaka da Borno.

Kara karanta wannan

Shiri ya baci: 'Yan bindiga sun yi wa sojoji kwanton bauna, an samu asarar rayuka

Sojojin sama sun yi barin wuta kan 'yan ta'adda a garin Rann da ke jihar Borno
Jirgin sojojin saman Najeriya ya saki bama-bamai kan 'yan ta'adda. Hoto: @NigAirForce
Source: Twitter

Sojoji sun gano mummunan shirin 'yan bindiga

Jaridar The Nation ta rahoto cewa rundunar Operation Hadin Kai (OPHK) ce ke da alhakin kakkabe kungiyoyin ta'addanci a Arewa maso Gabas.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton ya ce an hallaka 'yan ta'addar ne a lokacin da suka yi yunkurin kai wani hari kan sojojin kasa da aka girke a garin na Rann.

Mai magana da yawun rundunar sojojin sama (NAF), Air Commodore Ehimen Ejodame ya tabbatar da wannan rahoto a sanarwar da ya fitar ranar Juma'a.

Air Commodore Ehimen Ejodame ya sanar da cewa an yi nasarar dakile wani yunkurin 'yan bindiga na farmakar sojojin kasa ta hanyar tsarin tattara bayanai na ISR da kuma hare-haren sama (AI) a safiyar ranar Juma'a.

Sojojin saman sun kashe 'yan ta'adda a Borno

A cewar kakakin NAF, sojojin sama sun tuntubi sojojin kasan bayan samu sahihan bayanai game da shirin 'yan ta'addar na kai harin.

Kara karanta wannan

Sojoji sun dakile harin 'yan bindiga bayan an gwabza fada a Katsina

Tashar NTA ta rahoto cewa tattaunawar ta taimakawa sojojin wajen tunkarar 'yan ta'addar tare da fafatawa da su, wanda ya kai ga an kashe da dama daga cikin miyagun.

"Matakin gaggawa da aka dauka ya taimaka wajen dakile harin tare da dawo da kwanciyar hankali a yankin da abin ya faru.
"Wannan ya sake nuna irin kokarin da rundunar sojin sama take yi na ganin ta taimakawa sojojin kasa a yaki da 'yan ta'adda da kakkabe su."

- Air Commodore Ehimen Ejodame.

An rahoto cewa garin Rann na fuskantar hare-haren 'yan bindiga a 'yan kwanakin nan, amma matarnin sojoji cikin gaggawa na taimakawa wajen dakile su.

An hallaka 'yan ta'adda 30 a Zamfara

A wani labari, mun ruwaito cewa rundunar sojoji ta kaddamar da harin sama kan 'yan bindiga a lokacin da suke bikin aure a tsaurin Asaula, gundumar Yankuzo, karamar hukumar Tsafe, jihar Zamfara.

Sojojin saman sun kai harin a yammacin ranar Talata, 5 ga watan Agusta bayan samun sahihan bayanai daga yankin da kuma jami'an fikira na HUMINT.

A cewar majiyoyin tsaro, sama da 'yan ta'adda 30 ne aka kashe a yayin da sojojin saman suka yi luguden wuta a kan mahalarta taron.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com