Gwamnati Ta Jika Makoshin Ma'aikata, An Fara Biyansu Hakkokinsu bayan Jinkirin Watanni

Gwamnati Ta Jika Makoshin Ma'aikata, An Fara Biyansu Hakkokinsu bayan Jinkirin Watanni

  • Gwamnatin tarayya ta fara biyan kuɗin tallafin albashin da aka yi alkawarin ba wa ma'aikatan gwamnati
  • Ofishin Akanta Janar na Ƙasa ya tabbatar da cewa an fara biyan kuɗin ne a matakai har sai an gama biyan bashin watanni biyar da ake bi
  • Gwamnatin tarayya ta fara biyan tallafin albashin na N35,000 domin rage radadin cire tallafin fetur da hauhawar farashin rayuwa

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja – Gwamnatin tarayya ta fara biyan ma’aikatan gwamnati hakkokinsu na N35,000 a matsayin tallafin albashi don rage masu wahala.

Gwamnati ta bayyana cewa wannan na daga cikin wani mataki na ci gaba da cika alkawarin da ta ɗauka ga ma’aikatan gwamnatin tarayya don sauƙaƙa masu.

Kara karanta wannan

Ana batun yunwa, gwamnatin Tinubu ta fitar da ton 42,000 na hatsi a raba wa jihohi

Shugaban kasa, Bola Tinubu
Gwamnati ta fara biyan tallafin albashin ma'aikata Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

The Nation ta wallafa cewa wannan na kunshe a cikin wata sanarwa Ofishin Akanta Janar na Ƙasa (OAGF) ya fitar na tabbatar da cewa an fara biyan ma'aikatan kudinsu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnati ta fara biyan ma’aikata bashin N35, 000

Channels ta ruwaito cewa Daraktan Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na OAGF, Mista Bawa Mokwa, ya ce gwamnatin tarayya ta riga ta biya bashin wata ɗaya daga cikin watanni biyar da ma'aikatan ke bi.

Tallafin albashin N35,000 da gwamnatin ta bayar ta samar ne a matsayin matakin rage sauye-sauyen tattalin arziki ga ma’aikatan gwamnati.

An cimma yarjejeniyar biyan kudin bayan tattaunawa tsakanin gwamnatin tarayya da ƙungiyoyin ƙwadago, domin rage wa ma’aikata raɗaɗin rayuwa.

N35, 000: Gwamnatin tarayya ta kare kanta

Dangane da rade-radin cewa gwamnatin tarayya ta daina biyan tallafin albashi, ofishin Akanta Janar ya karyata wannan zargi.

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu
Gwamnati ta ce tana cika alkawari ga ma'aikata Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Ya bayyana cewa gwamnatin ba ta karya alkawari ba, inda ya yi bayani cewa ana biyan kuɗin ne a matakai har sai an gama biyan bashin.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba: 'Yadda Sadiq Gentle ya cika alhali muna shirin kai shi asibitin kasar waje'

Ya ce:

“Gwamnatin tarayya ba ta karya alkawarinta ba. Za a ci gaba da biyan bashin tallafin albashi na N35,000 a kowane wata har sai an gama biyan kuɗin gaba ɗaya.”

Wannan tabbaci na zuwa ne a daidai lokacin da ƙungiyoyin ƙwadago da ma’aikatan gwamnati ke matsa wa gwamnati lamba kan batun inganta albashi a yayin da farashin kayayyaki ke ƙara tashi.

Ma'aikata sun fara samun kudinsu

Wani ma'aikacin gwamnatin tarayya a hukumar NITT da ke Kano ya tabbatar wa Legit cewa ya samu tallafin da gwamnati ta alkawarta.

Mutumin da ya nemi a sakaye sunansa ya ce:

"Dazu na samu alat, amma na wata ɗaya aka biya mu gaskiya. Na ɗauka za a biya da yawa."

Sai dai ya ce ba dukkanninsu ne su su ka samu kuɗin ba, amma ana sa ran sauran za su samu na su daga baya.

Gwamnatin Tinubu ta ce ana kokari

Kara karanta wannan

Ana fargabar mayakan Turji sun koma ruwa, gwamnati ta faɗi adadin ƴan ta'adda da su ka tuba

A wani labarin, mun wallafa cewa Fadar shugaban kasa ta karyata ikirarin da ke cewa Najeriya na dab da rugujewa, tana mai cewa ana kambama matsalolin kasar fiye da kima.

Mai ba wa shugaban kasa Bola Tinubu shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai da hulɗa da jama’a, Sunday Dare, ya amince cewa kasar na fuskantar ƙalubalen tattalin arziki.

Dare ya ƙara da cewa rahoton da aka fitar da ke sukar gwamnati ya fi kama da son zuciya, waɗanda ke ƙoƙarin rage kushe gwamnatin tarayya na daidaita tattalin arziki.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.