Gwamna Abba: 'Yadda Sadiq Gentle Ya Cika alhali Muna Shirin Kai Shi Asibitin Kasar Waje'

Gwamna Abba: 'Yadda Sadiq Gentle Ya Cika alhali Muna Shirin Kai Shi Asibitin Kasar Waje'

  • Gwamnatin Kano ta yi ta’aziyyar rasuwar Sadiq Gentle, babban mai ɗaukar rahoto ga Mai girma Abba Kabir Yusuf
  • Gwamnan ya ce ya bayar da umarnin gaggawa domin fitar da Sadiq zuwa ƙasar Masar a ci gaba da neman magani kafin rasuwarsa
  • Manyan jami’an gwamnatin Kano sun halarci jana’izar, inda aka yi addu’ar Allah Ya gafarta masa, Ya sa ya huta

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Gwamnatin jihar Kano ta yi ta'aziyyar rasuwar ɗaya daga cikin masu ɗaukar rahoton musamman ga Gwamna Abba Kabir Yusuf, Sadiq Gentle.

Matashin ɗan Kwankwasiyyan ya rasu a ranar Alhamis bayan wasu ‘yan daba suka kutsa gidansu, suka sare shi a wurare da dama.

Bashir Gentle ya rasu
Gwamna Abba ya yi ta'aziyyar rasuwar Bashir Gentle Hoto: Bashir Gentle
Asali: Facebook

A cikin wani saƙo da Aka Abbaji ya wallafa a shafinsa na Facebook, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana takaicinsa kan rasuwar tare da fayyace matakan da aka ɗauka tun don ceto rayuwarsa da fari.

Kara karanta wannan

Lokaci ya yi: Babban mai ɗauko rahoto ga gwamnan Kano, Sadiq Gentle ya rasu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda Abba ya so ceto rayuwar Sadiq Gentle

Gwamna Abba ya bayyana cewa tun bayan samun labarin harin da aka kai wa Sadiq Gentle, ya bayar da umarni domin a ceton ransa a cikin gaggawa.

A cewarsa:

“A jiya da daddare, bayan na samu labarin halin da ake ciki, na bayar da umarni a gaggauta ɗauke shi zuwa asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano, tare da ba shi ɗaki na musamman da kulawa ta musamman.”

Gwamnan ya ƙara da cewa, bayan wannan umarni, ya kuma bukaci a gaggauta karɓar takardun tafiya na Sadiq da na ‘yan uwansa biyu domin fitar da su ƙasar waje a ci gaba da neman magani.

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf
Gwamnan Kano ya ce an shirya fitar da Sadiq kasar waje Hoto: Abba Kbair Yusuf
Asali: Facebook

Ya ce:

“Na kuma bayar da umarni ga kwamishinan lafiya a yau da safe ya tafi ya karɓi fasfo ɗinsa da na ‘yan uwansa guda biyu domin mu yi biza cikin gaggawa zuwa ƙasar Misra don ceto rayuwarsa.”

Kara karanta wannan

Gwamna Abba ya ba iyalan 'yan wasan kano da su ka rasu tallafin miliyoyin Naira da filaye

Gwamnan Kano ya yi takaicin rasuwar Sadiq

Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya bayyanan cewa sai dai kafin a kammala shirye-shiryen fitar da shi, Sadiq Gentle ya rasu.

Gwamna Abba ya ce:

“Kowane mai rai, mamaci ne. Allah ya nufa lokacinsa ya yi. A yau da safiyar nan wannan bawan Allah ya rasu, kuma tuni an yi jana’izarsa.”
Babban sakataren gwamnatin jiha, shugaban ma’aikata na gidan gwamnati, kwamishinoni, masu ba gwamna shawara, shugabannin ƙungiyar SSR, da sauran manyan jami’an gwamnati sun halarci jana’izar.

Hadimin Gwamnan Kano, Sadiq ya rasu

A baya, mun wallafa cewa babban mai ɗauko rahoto ga Gwamnan jihar Kano (SSR), Sadiq Gentle, ya rasu bayan fama da jinyar munanan raunukan da 'yan daba su ka masa.

Sadiq Gentle, wanda ke aiki a ma’aikatar kula da harkokin tarihi da al’adu, na ɗauko rahoto wa Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya rasu ne a asibiti a ranar Alhamis, 7 ga watan Agusta, 2025.

Rahotanni sun nuna cewa wasu ‘yan daba sun kutsa cikin gidansa suka sare shi da adda tare da burma masa wuƙa a wurare daban-daban na jikinsa, wanda ya yi sanadin rasuwarsa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.