Gwamnatin Tinubu Ta Yi Martani Mai Zafi, Ta ce ana Zuzuta Batun Yunwa a Najeriya
- Fadar shugaban kasa ta karyata ikirarin cewa Najeriya na dab da rugujewa saboda tarin matsalolin da su ka jefa jama'a a matsala
- Hadimin Shugaban Kasa, Sunday Dare ya soki sharhin da ke cewa Najeriya na cikin gagarumar matsala a gwamnatin Bola Tinubu
- Ya bayyana cewa jama'a ba su yaba kokarin gwamnati wajen ciyar da kasa da rage radadin tattalin arzikin da ake fuskanta a halin yanzu
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja – Fadar shugaban kasa ta karyata ikirarin da ke cewa Najeriya na dab da rugujewa, tana mai cewa ana kururuta matsaloin kasar nan fiye da kima.
Mai ba wa shugaban kasa Bola Tinubu shawara na musamman kan harkokin yada labarai da sadarwa da jama’a, Sunday Dare, ya amince cewa kasar na fuskantar matsalolin tattalin arziki.

Kara karanta wannan
Wata sabuwa: Bello Turji ya saki sabon bidiyo kan sulhu, ya kira babban malami da 'ɓarawo'

Source: Facebook
A sakon da ya wallafa a shafinsa na X, Sunday Dare ya yi martani ga wani rahoto, inda ya ce matsalolin ba su kai yadda jama'a ke fadi ba, ana zuzuta wa ne kawai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnati ta yi martani ga masu sukar Tinubu
Dare ya soki wani sharhin jaridar Daily Trust mai taken Najeriya na rugujew wa a karkashin Bola Tinubu, yana mai zargin rubutun ya yi rashin adalci ga mulkin Shugaban.
A cewarsa:
“Ikirarin cewa mutane miliyan 33 a Najeriya na cikin haɗarin yunwa hasashe ne kawai."
Ya ce wannan rubutun ya shiga sahun irin rahotannin kafofin yada labarai masu son zuciya da ke son da ƙile ƙoƙarin da gwamnatin tarayya ke yi na daidaita tattalin arziki da tallafa wa ‘yan ƙasa.
Dare ya lissafo ayyukan gwamnatin Tinubu
Dare ya bayyana wasu matakan da gwamnati ta dauka wajen taimaka wa 'yan kasa, daga ciki har da fitar da hatsi daga rumbunan ajiyar ƙasa domin ciyar da talakawa da mabukata.
Sauran sun hada da ci gaba da shirye-shiryen noma, da bayar da kuɗin tallafi ga marasa ƙarfi,wanda ya ce wannan na nuna jajircewar gwamnati.

Source: Facebook
Game da tattalin arziki, ya ce an samu ci gaba a fannin musayar kuɗi, inda Naira ke ƙara ƙarfi a kan Dalar Amurka,da kuma sauran ayyukan jin kai a kasar.
Ya ce:
"Muna maraba da kowace irin suka, amma a rika yinta a kan gaskiya."
Gwamnatin Tinubu ta ce 'yan ta'adda na tuba
A wani labarin, mun wallafa cewa a wani mataki na yaki da ta’addanci ba tare da amfani da karfin soja ba, gwamnatin tarayya ta bayyana cewa wasu tsofaffin ‘yan ta’adda sun mika wuya.
Rahotanni sun nuna cewa waɗannan tsofaffin ‘yan ta’adda na halartar wani shirin gyara halayya domin shirya mayar da su cikin al’umma su ci gaba da rayuwa kamar kowa.
Shugaban Cibiyar Yaki da Ta’addanci ta Ƙasa (NCTC), Manjo-Janar Adamu Laka, ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis a birnin Abuja, inda ya ce ana samun nasarar shirin sosai.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
