Ta'addanci: Bam Ya Tarwatsa Yara 3 Suna tsaka da Wasa a Borno

Ta'addanci: Bam Ya Tarwatsa Yara 3 Suna tsaka da Wasa a Borno

  • Tsautsayi ya fada a kan wasu yara uku a jihar Borno a lokacin da su ke tsaka da wasa a yankin Pulka, lamarin da ya yi sanadin rasuwarsu
  • Rahotanni sun bayyana cewa yaran sun taka wani bam da ake zargin cewa 'yan ta'addan Boko Haram ne su ka dasa a yankin
  • Bayan an garzaya da su asibiti ne, likitoci su ka tabbatar da cewa yan matan, Fati Dahiru, Aisha Ibrahim, da Fati Yakubu sun rasu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar BornoJama’ar jihar Borno sun shiga cikin tashin hankali da alhini bayan wani bam ya tashi ya hallaka yara uku a yayin da suke wasa cikin nishadi.

Lamarin ya faru ne a garin Pulka, ƙaramar hukumar Gwoza ta jihar Borno, a ranar Alhamis da rana, inda fashewar bam ɗin ta yi sanadiyyar mutuwar yaran.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun titsiye Sarki a dajin Zamfara, ya amsa tambayoyi masu zafi

Taswirar jihar Borno
Yara 3 sun rasu a jihar Borno Hoto: Legit.ng
Source: Original

Masanin tsaro, Zagazola Makama ya wallafa a shafinsa na X cewa wadanda su ka rasu sun hada da Fati Dahiru, Aisha Ibrahim, da Fati Yakubu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda yara su ka rasu a Borno

Rahoton ya ci gaba da cewa wani jami;in kungiyar tsaron sa kai ta CJTF, Buba Yaga, ya ce yaran na wasa ne da wani bam ya tashi.

Ya ce ana zargin ‘yan ta’addan Boko Haram ne su ka bar shi a wajen, kuma ya tashi ne da 2:20 na ranar Alhamis, yayin da tsautsayi ya fada a kan yaran.

Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum
Ana fargabar akwai sauran bam da aka dasa a Borno Hoto: The Borno State Governor
Source: Original

Bayan faruwar lamarin, tawagar haɗin gwiwa ta jami’an EOD-CBRN na ‘yan sanda, sojojin Operation Hadin Kai, CJTF da mafarauta na yankin suka isa wurin.

Sun kebe yankin, sannan suka gudanar da bincike domin gano ko akwai wasu bama-bamai da ba su fashe ba domin daukar mataki na gaba.

Pulka: Babu sauran bam a Borno

Kara karanta wannan

'A murƙushe su kawai': Shehi ya faɗi hukuncin Musulunci kan irinsu Bello Turji

Bayan cikakken bincike, jami’an sun tabbatar cewa ba a samu wasu bama-bamai ba, kuma tuni hankalin jama'ar yankin ya fara dawo wa jikinsu.

Duk da haka, sun gargadi jama’a da su rika sanar da hukumomin tsaro nan take idan suka ga wani abu mai kama da na fashewa, domin kauce wa irin wannan mummunan lamari.

Bayan an garzaya da yaran da bam ya tashi da su asibitin gwamnati na Gwoza, likitoci sun tabbatar da mutuwarsu.

Tuni aka mika gawawwakin nasu ga iyalansu domin yi musu jana’iza bisa ga tsarin addinin Musulunci.

Rahotannin baya-bayan nan sun nuna cewa duk da raguwar hare-haren ‘yan ta’adda a Borno, barazanar abubuwan fashewa da aka bari a baya na ci gaba da zama matsala ga tsaron yankin.

'Yan ta'adda sun sha wuya a Borno

A baya, mun wallafa cewa dakarun sojojin Najeriya na rundunar Operation Hadin Kai sun samu nasarar hallaka wasu da ake zargin mayakan Boko Haram ne guda bakwai a jihar Borno.

Rahotanni sun nuna cewa dakarun sojojin sun kashe ‘yan ta’addan ne yayin wani kwanton bauna da suka shirya a kan hanyar Mayanti da ke yankin Dar El-Jamal na jihar.

Majiyoyin tsaro sun tabbatar cewa kwanton baunar ya shafi gagarumin shirin dakile ‘yan ta’adda a yankin, inda sojoji suka toshe duk wata hanyar tserewa kafin su kai farmaki.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng

iiq_pixel