'A Murƙushe Su kawai': Shehi Ya Faɗi Hukuncin Musulunci kan irinsu Bello Turji
- Sheikh Ishaq Adam Ishaq ya yi watsi da ra'ayin tattaunawar sulhu da ‘yan bindiga, yana mai cewa Musulunci ya umurci a yake su
- Malamin ya bayyana cewa addini da dokar kasa duk sun amince a kashe su ko a hukunta su matukar suna ci gaba da barna
- Ya kalubalanci masu cewa ‘yan bindiga sun fi karfin jami’an tsaro, yana mai jaddada cewa gwamnati na da ikon kawo karshen su
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Ana ci gaba da samun mabambantan ra'ayoyi kan tattaunawa da yan bindiga domin samun zaman lafiya a Arewacin Najeriya.
Malamai sun bayyana ra'ayoyinsu game da haka inda wasu ke kushe bukatar tattaunawa da maharan.

Source: Facebook
Sheikh Ishaq ya yi caccaka kan zama da Turji
Sheikh Ishaq Adam Ishaq ya bayyana matsayarsa kan lamarin a wani bidiyo da shafin Karatuttukan Malaman Musulunci ya wallafa a Facebook.

Kara karanta wannan
Wata sabuwa: Bello Turji ya saki sabon bidiyo kan sulhu, ya kira babban malami da 'ɓarawo'
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Malamin ya ce ko kadan bai tare da masu fahimtar wai a yi sulhu da wadannan mutane da ke cikin daji suna kashe al'umma.
Ya bayyana abin da Musulunci ya ce game da su da kuma hukuncin da ya kamaci a yi musu bayan haka.
Ya ce:
"Kuma wadannan mutanen da ake ta cewa a yi sulhu da su ina da tambaya, menene matsayin Musulunci a kan irinsu?.
"Musulunci abin da ya ce shi ne a yake su, a kashe su har sai sun daina wannan barnar.
"Musulunci ya ce ko a kashe su, ko a tsire su ko a yanke kafar dama da hagu ko a kore su daga garin."

Source: Twitter
Matsayar Shehin kan zaman tattaunawa da Turji
Sheikh Ishaq Adam ya ce sun tattauna da wani wanda yake da irin wannan fahimta inda ya kalubalence shi kan lamarin.
Malamin ya ce shi kam ko kadan ba zai taba yadda cewa mutanen da ke cikin dajin nan sun fi karfin jami'an tsaron Najeriya ba.
Ya bukaci daukar tsauraran matakai domin kawo karshen matsalar tsaro da ta addabi yankin Arewa maso Yammacin Najeriya da sauran bangarori.
Ya kara da cewa:
"Jiya muna tattaunawa da wani, ya ce gwara a yi sulhu na ce a'a a yake su, na ce masa abin da addini ya ce shi ne a yake su, dokar kasa ta ce a yake su.
"Sai ya ce ai ba zai yiwu ba, na ce to me yasa ba zai yiwu ba, ni dai ban yadda wai wadannan da suke daji sun fi karfin jami'an tsaron Najeriya ba."
An soki maganar yin sulhu da Bello Turji
Kun ji cewa sakin mutane 32 da Bello Turji ya yi ya jawyo ce-ce-ku-ce, yayin da wasu ke ganin hakan tamkar dawowa da tsohon kuskure ne.
Masanin lamuran tsaro, Alhaji Sani Shinkafi ya ce tattaunawar da aka yi da Turji ba ta da amfani, inda ya bayyana ta a matsayin rashin adalci.
Hakan ya biyo bayan kokarin Sheikh Musa Yusuf Assadus Sunnah da ya ce sun tattauna da dan ta'addan lokuta da dama.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
