Ana Fargabar Mayakan Turji Sun Koma Ruwa, Gwamnati Ta Faɗi Adadin Ƴan Ta'adda da Su ka Tuba
- Gwamnatin tarayya ta ce tsofaffin 'yan ta’adda 300 na ci gaba da samun horo a sansanin Mallam Sidi da ke Gombe don dawo wa cikin gari
- Shugaban cibiyar yaki da ta'addanci, Manjo Janar Adamu Laka ya ce ana samun karuwar 'yan ta'adda da ke mika wuya daga Arewa
- An kuma kaddamar da sabon shirin noma da sana’o’i don taimaka wa masu su samu damar dogaro da kai da rayuwa mai kyau
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja – A wani mataki na yaki da ta’addanci ba tare da amfani da karfin soja ba, gwamnatin tarayya ta bayyana ce wasu 'yan ta'adda sun tuba.
Ta kara da cewa sama da 'yan ta’adda 300 da suka tuba na halartar wani shirin gyara halayya domin a shirya mayar da su cikin al'umma.

Kara karanta wannan
Gwamna Abba ya ba iyalan 'yan wasan kano da su ka rasu tallafin miliyoyin Naira da filaye

Source: Facebook
Jaridar Punch ta ruwaito cewa, Shugaban Cibiyar Yaki da Ta’addanci ta Ƙasa (NCTC), Manjo-Janar Adamu Laka, ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis a Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya fadi haka ne yayin wani taro da ya kunshi manyan masu ruwa da tsaki da kuma masu bada tallafi don samar da hanyoyin dogaro da kai ga tsofaffin 'yan ta'adda.
‘Yan ta’adda sun tuba a Najeriya
Jaridar The Cable ta ruwaito cewa Laka ya ce shirin wani kokari ne na gwamnati na kawar da ta’addanci da kuma sake mayar da tubabbun 'yan ta'addan cikin al'umma.
Ya ce fiye da tsofaffin mayaƙa 2,600 ne aka kammala horar da su da kuma gyara masu hali a sansanin Mallam Sidi da ke Jihar Gombe.
A cewar Laka, mutum 300 da ke cikin shirin a yanzu sune wadanda suka mika wuya da kansu cikin watannin baya, musamman daga yankunan Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya.

Source: Twitter
Ya ce:
“A kammala shirin gyara halayyar tsofaffin mayaƙa 2,600 da dawo da su cikin al’umma. An ba su horo, tallafin da koya masu sana’o’i. A yanzu haka, mutum sama da 300 na ci gaba da samun horo a sansanin.”
Ana samun karuwar ‘yan ta’adda masu tuba
Laka ya kara da cewa ana samun yawaitar masu aikata ta’addanci da ke zubar da makamansu tare da rungumar zaman lafiya a Najeriya.
Ya ce:
“Haka kuma, yawan ‘yan ta’adda da ke nuna niyyar mika wuya na karuwa a yankunan Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya. Akwai kokarin kaddamar da shirye-shiryen kwace makamai, gyara halayya da dawo da su cikin al’umma a wadannan yankuna.”
Sai dai ya jaddada cewa yawancin tsofaffin ‘yan ta’adda da suka tuba ba sa samun cikakken damar ci gaba bayan an dawo da su cikin al’umma, abin da ka iya hana ci gaban da aka samu.
Haka kuma, Laka ya sanar da fara wani sabon shirin noma da sana’o’i tare da hadin gwiwar Cibiyar Binciken Ayyukan Noma na Duniya (IITA) don tallafawa tubabbun mayakan.
Wasu 'yan ta'adda sun sace basarake
A baya, mun wallafa cewa wasu ƴan bindiga sun sace basaraken garin Yankuzo, Alhaji Babangida Kogo, da ke ƙaramar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara a ranar Talata.
Rahotanni sun ce an sace basaraken jim kaɗan bayan jiragen rundunar sojin saman Najeriya (NAF) sun kai mummunan farmaki a wani daji da ke kusa da garin tare da kashe wasu da dama.
Basaraken yana kan hanyarsa ta barin garin ne zuwa barin garin saboda fargabar harin ramuwar gayya daga ƴan bindigan da suka gamu da luguden wutan sojoji aka dauke shi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

