Matsala Ta Tunkaro Ƴan Najeriya, Za a Ɗauke Sabis na Waya a Kaduna da Wasu Jihohi 2
- An fargabar da za a iya ɗauke sabis bayan rikicin da ya ɓarke tsakanin ƙungiyoyin dakon mai da ƙungiyar da ke kula da turakun sadarwa
- Rahotanni sun nuna cewa rikicin ya hana kai man dizal zuwa tashohin sadarwa 16,000 a jihohin Kaduna, Legas da Delta
- Kungiyar kamfanonin sadarwa (ALTON) ta nuna damuwarta kan matakin da masu dakon mai suka ɗauka na hana kai dizal ga turakun sadarwa
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kaduna - Rahotanni sun nuna cewa da yiwuwar a dakatar da ayyukan turakun sadarwa 16,000 a yankuna daban-daban a jihohin Kaduna, Legas da Delta nan ba da jimawa ba.
Rufe waɗannan tashoshin sadarwa mallakin kamfaninin sadarwa kamar MTN, Airtel da Glo, na iya jefa miliyoyin masu amfani da waya da bankuna cikin matsala.

Source: Getty Images
Wannan matsalar, a cewar Vanguard, za ta iya shafar asibiti, cibiyoyin ilimi da sauran bangarori da ke dogaro da sadarwar wayar hannu da intanet a wadannan jihohi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Za a ɗauke sabis a Kaduna da jihohi 2?
Bayanai sun nuna cewa turakun sadarwar na fuskantar daina aiki ne sakamkon rikicin da ya ɓarke tsakanin ƙungiyar ma’aikatan fetur da gas na (NUOENG), da kungiyar masu dakon mai da gas (NOGASA).
Rigimar ta shafi kamfanin kula da turakun sadarwa IHS, kan zargin karkatar da man dizal da ya kamata a yi amfani da shi wajen gudanar da harkokin sadarwa.
Kamfanin IHS na zargin wasu mambobin NOGASA da karkatar da man dizal da aka tanadar domin tashoshin sadarwa.
An hana kai dizal zuwa turakun sadarwa
Duk da cewa hukumomi na gudanar da bincike kan zargin, kungiyoyin NUOENG da NOGASA sun toshe hanyoyin raba dizal zuwa dubban turakun sadarwa da IHS ke kula da su a wadannan jihohi da kewaye.
Kungiyar kamfanonin sadarwa a Najeriya (ALTON), ta bayyana wannan matsala a matsayin cin amanar kasa da barazana ga tsaron kasa, duba da yadda doka ta ayyana cibiyoyin sadarwa a matsayin muhimman ababen more rayuwa.
A cikin wata sanarwa da Shugaban ALTON, Injiniya Gbenga Adebayo, ya sanya wa hannu, kungiyar ta ce irin wannan rikici ya kamata a warware shi ta hanyar tattaunawa, ba ta hanyar amfani da karfi ko tashin hankali ba.
Kamfanonin sadarwa sun nuna damuwa
A rahoton PM News, sanarwar ta ce:
"Mun samu rahotannin da ke cewa mambobin kungiyar NUPENG da NOGASA sun hana isar da dizal zuwa dubban turakan sadarwa da kamfanin IHS Towers ke kula da su a Kaduna, Legas da Delta.
"Wannan matakin dai ya samo asali daga zargin da IHS ke yi wa wasu mambobin NOGASA guda biyu na karkatar da dizal. Hakan ya jefa turakan sadarwa fiye da 16,000 a cikin hadari.
"Ko da yake ALTON ba ta tsoma baki cikin rikici tsakanin mambobinta da wasu kungiyoyi, muna matukar damuwa da irin illar da wannan matsala ke da ita ga ababen more rayuwa da tsaron al’umma."

Source: Getty Images
Kungiyar ALTON ta koka kan hare-hare
A wani labarin, kun ji cewa kamfanonin sadarwa da ke aiki a Najeriya sun roƙi hukumomin tsaro su kare kayan aikinsu daga hare-haren miyagu.
Kamfanonin sun buƙaci dakarun tsaron Najeriya su taimaka wajen kare turakan sadarwa domin gujewa rashin karfin intanet da ɗaukewar sabis.
Ƙungiyar manyan kamfanonin sadarwa ta kasa wato ALTON, ta nuna damuwa ƙwarai kan yadda sata da lalata kayayyakin sadarwa ke ƙaruwa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

