Wata Sabuwa: Bello Turji Ya Saki Sabon Bidiyo kan Sulhu, Ya Kira Babban Malami da 'Ɓarawo'
- Yayin da ake ta surutu kan sulhu, Bello Turji ya saƙi sabon faifan bidiyo yau Alhamis, 7 ga watan Agusta, 2025
- Ƙasurgumin ɗan bindigar ya tabbatar da cewa ana tattaunawa domin samar da zaman lafiya a jihar Zamfara da makwaftan jihohi
- Turji ya kuma caccaki Sheikh Murtala Asada, yana mai cewa ba shi da aiki sai ɓaɓatu da kira ga jami'an tsaro su gaggauta kama Bello Turji
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Zamfara - Shahararren shugaban dabar 'yan bindiga, Bello Turji, ya fitar da sabon sakon bidiyo yayin da ake ta surutu kan batun sulhu da shi a Zamfara.
Bello Turji ya tabbatar cewa ana ci gaba da tattaunawa da shi domin kawo karshen tashin hankali da rashin tsaro a wasu sassan jihar Zamfara da makwabtan jihohi.

Source: Twitter
Hakan na kunshe a cikin bidiyon da ɗan bindigar ya saki, wanda Zagazola Makama, masani kuma mai sharhi kan harkokin tsaro ya wallafa a X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bello Turji ya yi magana kan batun sulhu
A cikin bidiyon, Turji ya ce tattaunawar na da nufin samar da zaman lafiya mai dorewa domin ba wa manoma da makiyaya damar rayuwa tare cikin lumana, ba tare da fargabar tashin hankali ko muzgunawa ba.
“Abin da muke so shi ne zaman lafiya, domin da manomi da makiyayi da ɗan kasuwa ko ya je ya ci gaba da hulɗarsa ba tare da fargaba ba," in ji Bello Turji.
Turji ya caccaki Sheikh Murtala Asada
Sai dai kuma, ƙasurgumin ɗan bindigar ya caccakin babban malamin addinin Musulunci, Sheikh Murtala Bello Asada.
Sheikh Asada dai kwanan nan ya karyata rahotannin da ke cewa ana wata tattaunawa tsakanin Turji da wakilan gwamnati domin tabbatar da zaman lafiya.

Kara karanta wannan
Shiri ya baci: 'Yan bindiga sun yi wa sojoji kwanton bauna, an samu asarar rayuka
Bello Turji ya zargi malamin da yin ƙarya domin yaudaran jama'a. Ya ce:
"Yana nan ya fake a wuri ɗaya an zagaye shi, yana yaɗa cewa ba a sulhu da mu, gwamnan Sakkawato da Tinubu Allah Ya karya su. Mu da yake wa bakar fata Allah Ya halicce mu, idan ya so ya ɗauke mu zai ɗauke mu.
"Ka koma cikin ofis kana ta ɓaɓatun a kama Bello Turji, kana ci da addini, ka ji tsoron Allah, ba haka ake ba, Annabi bai zagi kowa wurin addini ba, kar ka zama jahili baƙauye.
"Kullum sai ka ce a aje a kamo mu, to a naɗa ka kwamandan ka zo ka kama mu, sai ka zo ka ga wurin da muke. Kana cewa jami'an tsaro kwamandan Bello Turji ya kirawo ka, ina ka samu lambarsa? Ashe kaima ɓarawo ne."
Har yanzu dai gwamnatin tarayya da gwamnatin jihar Zamfara ba su fito fili sun tabbatar da wannan tattaunawar sulhu ba.
Yan bindiga sun nemi Naira miliyan 56
A wani labarin, kun ji cewa manoma a yankin Dan Isa da ke karamar hukumar Kaura Namoda a jihar Zamfara sun bayyana barazanar da ƴan bindiga suka masu.
Hakimin Ɗan Isa, Malam Hassan Yarima, ya tabbatar da cewa kauyuka 35 da ke ƙarƙashinsa na fuskantar barazana daga ƴan bindiga a daminar bana.
Hakimin ya ce kowane ƙauye daga cikin ƙauyuka 35 da ke ƙarƙashin gundumarsa ya biya N800,000 kafin mazauna su samu damar fara noma.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

