Tinubu Ya Dauko Tsohon Ciyaman a Kano, Ya ba Shi Mukamin Shugaban Hukumar NERC
- Shugaba Bola Tinubu ya naɗa Injiniya Abdullahi Garba Ramat, tsohon ciyaman din Ungogo, a matsayin shugaban hukumar NERC
- Injiniya Ramat, mai shekaru 39, zai fara aiki a matsayin mukaddashin shugaban NERC kafin lokacin da majalisa za ta tantance shi
- Baya ga Ramat, Tinubu ya naɗa Abubakar Yusuf da Fouad Animashun a matsayin kwamishinoni a NERC don inga harkar wuta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja – Shugaba Bola Tinubu ya naɗa Injiniya Abdullahi Garba Ramat a matsayin shugaban hukumar kula da wutar lantarki ta kasa (NERC).
Legit Hausa ta tattaro cewa kafin wannan naɗin, Ramat ya rike mukamin shugaban ƙaramar hukumar Ungogo da ke Kano daga shekarar 2021 zuwa 2024.

Asali: Facebook
Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ne ya sanar da nadin Ramar a sanarwar da Olusegun Dada ya wallafa a shafinsa na X a ranar Alhamis.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tinubu ya nada shugabannin hukumar NERC
Sanarwar Onanuga ta ce Injiniya Ramat zai fara aiki a matsayin mukaddashi har zuwa lokacin da majalisar tarayya za ta tantance shi bisa tanadin doka.
Baya ga Ramat, Shugaba Tinubu ya naɗa Abubakar Yusuf a matsayin kwamishinan kula da bukatun masu amfani da wuta na NERC.
Hakazalika, an nada Dr Fouad Olayinka Animashun a matsayin kwamishinan harkokin kuɗi da ayyukan gudanarwa a hukumar NERC.
“Shugaba Tinubu ya amince da naɗin Injiniya Abdullahi Garba Ramat a matsayin sabon shugaban kuma babban daraktan hukumar kula da wutar lantarki ta kasa
“Ramat, ɗan shekara 39, injiniya ne na lantarki kuma gogaggen mai gudanarwa, wanda ya ke da digirin digirgir (PhD) a fannin dabarun gudanar da aiki."
Ramat ya gode wa Tinubu kan wannan nadi
Onanuga ya ce, kodayake an tura sunayen ga majalisa domin tantancewa, shugaban ƙasa ya bayar da umarni cewa Ramat ya fara aiki a matsayin mukaddashi domin gujewa barin gurbin shugabanci a hukumar da ke da matuƙar muhimmanci.

Kara karanta wannan
Sabon shugaban APC da gwamnoni sun gana da Sheikh Jingir, malaman Izala da Darika
A wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook bayan naɗin, Ramat ya bayyana godiyarsa da cewa:
“Alhamdulillah. Daga jagorantar ƙaramar hukuma ɗaya, zuwa kula da dukkan kananan hukumomi 774 ta hanyar NERC. Hakika Allah Mai girma ne.”
Ya kuma gode wa Shugaba Tinubu bisa amincewa da ya yi da bai wa matasa irinsa wannan babbar dama ta shugabanci a matakin ƙasa.

Asali: Getty Images
Menene ya kamata a sani game da NERC?
NERC wata hukuma ce mai zaman kanta da aka kafa domin lura da dukkan harkokin masana’antar samar da wutar lantarki a Najeriya, kamar yadda aka gani a shafin hukumar.
An kafa ta ne a shekarar 2005 karkashin dokar sauya tsarin samar da wutar lantarki (EPSRA), wadda aka soke aka maye gurbinta da Sabuwar Dokar Wuta ta 2023.
NERC na da alhakin ba da lasisin aiki, tsara ka’idoji da tanade-tanade, kare haƙƙin masu amfani da wuta, da kuma tantance farashin da ya dace masu amfani da wuta su rika biya.

Kara karanta wannan
APC ta yi watsi da kalaman El Rufai, ta fadi dalilin da zai sa Tinubu yin tazarce a 2027
'Amfanin ba kananan hukumomi 'yanci' - Ramat
A wani labarin, mun ruwaito cewa, tsohon shugaban karamar hukumar Ungogo, Injiniya Abdullahi Garba Ramat ya ce lokaci ya yi da jama’a za su mori dimukuradiyya.
A tattaunarsa da Legit, tsohon shugaban karamar hukumar a gwamnatin Abdullahi Ganduje ya ce ba kananan hukumomi ‘yancin cin gashin kai abin murna ne ga talaka.
Ya ce nan gaba kadan, matukar hukumomi irin su ICPC da EFCC za su sa ido kan gudanarwar kananan hukumomi, to alkairai za su je ga mutane a kauyuka da karkara.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng