Wata Matsala Ta Tunkaro Najeriya, Za a Iya Rasa Naira Tiriliyan 1.6 duk Shekara

Wata Matsala Ta Tunkaro Najeriya, Za a Iya Rasa Naira Tiriliyan 1.6 duk Shekara

  • Ƙungiyar SEREC ta yi hasashen cewa Najeriya na iya rasa N130bn duk shekara saboda durkushewar ayyuka a tashoshin jiragen ruwa
  • SEREC ta bayyana cewa Najeriya na iya yin asarar jimillar N800bn zuwa N1.6tn idan aka hada haraji da karancin masu zuba jari
  • Ƙungiyar ta bukaci gwamnatin tarayya da ta dauki matakan gaggawa ciki har da amfani da fasaha da warware cunkoso a Apapa da Tincan

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Wata ƙungiyar bincike ta fannin sufurin ruwa mai suna SEREC ta ce Najeriya na iya rasa kimanin N130bn a kowace shekara sakamakon durkushewar harkokin tashar jiragen ruwa a kasar.

SEREC ta ce hakan zai shafi harajin kwastan, harajin VAT na shigo da kayayyaki da wasu haraji daban-daban, wanda zai rage wa gwamnati kudaden shiga.

Wata kungiya ta hango irin asarar biliyoyin da najeriya za ta yi a duk shekara
Tashoshin jiragen ruwan Najeriya yayin da ake sauke kwantenoni. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Najeriya za ta rasa haraji daga tashoshi

Kara karanta wannan

2027: An ji ra'ayin Jonathan kan fafatawa da Shugaba Tinubu

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban sashen binciken cibiyar, Mista Eugene Nweke ya fitar a karshen mako, inji rahoton Punch.

SEREC ta ce raguwar ayyuka a tashoshin ruwa za ta shafi kudin shigar gwamnati, wanda hakan zai iya kawo cikas wajen samar da ababen more rayuwa da muhimman ayyuka.

“Najeriya na iya rasa N130bn duk shekara a kudin harajin kwastan, VAT da sauran haraji saboda rage ayyuka a tashoshin ruwa,” in ji Nweke.

Mista Eugene Nweke ya kara da cewa hakan na iya janyo asarar kusan kashi 10 zuwa 20 na kudaden shigar gwamnati, wanda zai kai tsakanin N300bn zuwa N600bn.

Asarar za ta iya kai Naira tiriliyan 1.6

Nweke ya yi gargadin cewa kasuwanni da dama na iya karkata zuwa makwabtan kasashe masu ingantattun tashoshi, lamarin da zai janyo wa Najeriya asarar biliyoyin Naira na zuba jari.

Ya ce:

“Idan har aka samu koma bayan kashi 20% na zuba jari daga waje a bangaren sufuri, Najeriya na iya rasa N500bn zuwa N1tn daga masu zuba jarin waje.”

Kara karanta wannan

Ana jiran Tinubu ya karrama daliban Yobe, lauya ya gwangwaje su da kyaututtuka

Shugaban ya kara da cewa idan aka hada kudaden da ake fargabar gwamnati za ta rasa, to Najeriya na fuskantar asarar N800bn zuwa N1.6tn gaba daya a shekara.

Sai dai Nweke ya ce ya isa izina ga gwamnati, rahotannin baya-bayan nan da ke nuna cewa Najeriya ta rasa matsayin ta na cibiyar sufuri a Yammacin Afirka.

An shawarci gwamnatin tarayya da ta dauki matakan gaggawa domin magance matsalolin tashoshin jiragen ruwa.
Kungiya na son Shugaba Bola Tinubu ya farfado da tashoshin jiragen ruwa na Najeriya. Hoto: @officialABAT/X, Getty Images
Source: Getty Images

Shawarwarin SEREC ga gwamnatin tarayya

Ya bukaci gwamnati da ta dauki matakin gaggawa wajen magance kalubalen da ke barazana ga bangaren sufurin ruwa, tare da kirkiro hanyoyin hana su faruwa nan gaba.

A cewar Nweke, wanda kuma shi ne tsohon shugaban ƙungiyar masu jigilar kaya ta gwamnati (NAGAFF), dole ne Najeriya ta fara amfani da sababbin fasahohi na kasuwanci don rage wahala da kashe kudi.

Ya kuma bukaci gwamnati da ta shawo kan matsalolin cunkoso da jinkirin saukewa da dora kayayyaki a tashoshin Apapa da Tincan, inji rahoton The Sun.

Dangote zai gina babbar tashar jirgin ruwa

A wani labarin, mun ruwaito cewa, hamshakin dan kasuwa, Aliko Dangote, ya bayyana shirin gina tashar jiragen ruwa da fadada kamfanin siminti a Ogun.

Kara karanta wannan

Tinubu: Gwamnati ta kashe N26.38bn a kan jiragen shugaban ƙasa a cikin watanni 18

Ana sa ran cewa wannan aikin zai farfado da shirin da aka dade da watsi da shi a yankin, wanda zai inganta tattalin arzikin Ogun da ma Najeriya baki ɗaya.

Aliko Dangote ya kuma bayyana cewa gina tashar jiragen ruwan zai jawo masu zuba jari da kuma inganta harkokin kasuwanci a yankin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com