Sojoji Sun Dakile Harin 'Yan Bindiga bayan an Gwabza Fada a Katsina

Sojoji Sun Dakile Harin 'Yan Bindiga bayan an Gwabza Fada a Katsina

  • Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar dakile wani hari da 'yan bindiga suka kai a.jihar Katsina
  • Sojojin na rundunar Operation Fansan Yanma sun ragargaji 'yan bindigan bayan sun yi gumurzu a cikin daji
  • Hakazalika sun ceto wasu mutane da 'yan bindigan suka sace a karamar hukumar Malumfashi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Katsina - Dakarun sojoji na rundunar Operation Fansan Yanma sun dakile wani hari da ‘yan bindiga suka kai a jihar Katsina.

Sojojin sun dakile harin ne a kauyen Tashar Gemu, da ke ƙaramar hukumar Malumfashi a jihar Katsina.

Sojoji sun dakile harin 'yan bindiga a Katsina
Sojoji sun kashe dan bindiga a Katsina Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ne ya bayyana hakan a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sojoji sun yi nasara kan 'yan bindiga

Dakarun sojojin sun kashe ɗaya daga cikin ‘yan bindigan da ake zargi kuma suka ceto mutum uku da aka yi garkuwa da su ba tare da jin rauni ba.

Kara karanta wannan

Jiragen yaki sun kona 'yan bindiga kurmus suna bikin aure a dajin Zamfara

Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne da safiyar ranar Laraba da misalin ƙarfe 6:00 na safe.

Jami'an tsaron sun samu sahihan bayanan sirri daga mazauna yankin cewa wasu ‘yan bindiga dauke da muggan makamai dake tafiya a kan babura, na ƙaratowa kauyen da niyyar kai hari.

Bayan samun bayanan, dakarun sojoji da suka haɗa kai da 'yan sanda tare da mambobin rundunar C-Watch sun dakile harin na 'yan bindigan.

"Da isar su yankin, sai suka shiga musayar wuta da ‘yan bindigar, lamarin da ya sa suka tsere. Sai suka bi su har zuwa kauyen Unguwar Gambo, inda suka samu nasarar kashe ɗaya daga cikin su."

- Wata majiya

Dakaru sun ceto mutanen da aka sace

A yayin da ake fafatawar, jami’an tsaron sun yi nasarar ceto wasu mutane uku da aka yi garkuwa da su, inda aka kwato su ba tare da wani jin wani rauni ba.

Wadanda aka ceto ɗin su ne: Yahaya Murtala, Murwana Murtala, da Suleiman Abdullahi, dukkansu mazauna kauyen Tashar Gemu.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun gwabza da 'yan bindiga a Zamfara, an samu asarar rayuka

Wannan nasara ta zo ne a wani mataki na ci gaba da ƙarfafa tsaro a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya, inda ayyukan ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane ke ƙara yawaita.

Sojoji sun samu nasara kan 'yan bindiga a Katsina
Sojoji sun hallaka dan bindiga a Katsina Hotto: Legit.ng
Source: Original

Jami’an tsaro sun tabbatar da cewa za su ci gaba da kai farmaki ga masu laifi a duk inda suka buya har sai an tabbatar da cewa an dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankunan da lamarin ke faruwa.

Ana kuma kira ga jama'a da su ci gaba da bayar da bayanan sirri da za su taimaka wajen gano duk wani motsin da ya ke da haɗari, domin taimakawa hukumomin tsaro wajen sauke nauyin da ke kansu cikin sauƙi da nasara.

Sojoji sun fafata 'yan bindiga a Zamfara

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar dakile wani harin 'yan bindiga a jihar Zamfara.

Sojojin sun yi artabu mai zafi da 'yan bindigan bayan da suka yi kokarin kai hari a karamar hukumar Tsafe.

Jami'an tsaron wadanda suke tare da 'yan sa-kai sun samu nasarar hallaka 'yan bindiga tare da kwato makamai da dama.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng