Abin Mamaki: Pantami Ya Faɗi yadda Aka Yi Buhari Ya Naɗa Shi Minista, Shugaban NITDA

Abin Mamaki: Pantami Ya Faɗi yadda Aka Yi Buhari Ya Naɗa Shi Minista, Shugaban NITDA

  • An gani wani bidiyo da ake zaton tsoho ne inda Farfesa Isa Pantami ya yaba wa marigayi Muhammadu Buhari bisa ba shi mukamai
  • Pantami ya ce Buhari ya karbi takardunsa a Madina, kasar Saudi daga baya sai kawai ya ji an naɗa shi shugaban hukumar NITDA a 2016
  • Malamin musuluncin kuma masanin komfuta ya ce a 2019 ma sai kawai ya ga sunansa a jerin ministoci, Buhari ya kuma saka sunansa da kansa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Katsina - An yaɗa wani bidiyo wanda tsohon ministan tattalina arzikin zamani ke tuna alherin marigayi Muhammadu Buhari gare shi.

Farfesa Isa Ali Pantami ya bayyana yadda aka yi Muhammadu Buhari ya naɗa shi mukamai a gwamnatinsa ba tare da ya san za a yi hakan ba.

Kara karanta wannan

Masoyan Pantami sun dura kan Shehi da ya ce Malam bai gina masallaci ko 1 ba

Pantami ya tuna alherin Buhari gare shi
Pantami ya tuna yadda Buhari ya naɗa shi minista, shugaban NITDA. Hoto: Professor Isa Ali Pantami.
Source: Facebook

Haduwar Pantami da Buhari a London

Hakan na cikin wani faifan bidiyo da ake zaton ya dade da Pantami ya yaɗa a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A bidiyon, Pantami ya bayyana haduwarsa da Buhari a Madina kafin nada shi mukamin shugaban hukumar NITDA.

Pantami ya ce ya yi mamaki yadda Buhari bai shawarce shi ba kawai ya karbi takardunsa, ya ba shi mukami.

Ya ce:

"Mai gida na Muhammadu Buhari, na kammala karatu a UK na tafi Madina ina karantarwa, a watan Fabrairun 2016 shigowarsa ta farko bayan zama shugaban ƙasa.
"Aka fadamin ya shigo Madina ya yi ziyara ya wuce Umrah, ya umarci na zo na gan shi, na zo mun gaisa ya ce na jira shi a waje har ya ban kudi na ba yara.
"Bayan na fito na tsaya a waje, sai ya turo sako na ba da takardu na ban san me yake nufi ba kuma bai shawarace ni ba."

Kara karanta wannan

Jigon APC ya gano dalili 1 da zai hana 'yan Arewa zabar Peter Obi a 2027

Farfesa Pantami ya yabawa Buhari kan halaccinsa
Farfesa Pantami ya fadi yadda ya samu minista a gwamnonin Buhari. Hoto: Professor Isa Ali Pantami.
Source: Facebook

Yadda Buhari ya karbi takardun Pantami

Farfesa Pantami ya ce Buhari ya karbi takardunsa a watan Fabrairu zuwa Satumba kawai ya ga sunansa a matsayin shugaban NITDA.

Ya kuma bayyana yadda ya tsinci kansa cikin jerin wadanda za a nada ministoci a wa'adin mulkin Buhari na biyu.

Ya kara da cewa:

"Bayan ya karbi takardun a Fabrairu zuwa Satumba 26 sai na ji ya nada ni shugaban hukumar NITDA ban san komai ba sai sanarwa kawai na ji.
"Bayan wannan, a watan Yuli, 2019 ina London a wani taro, kawai na fito shan iska na kunna wayata sai na ke ganin sakon taya murna da addu'o'i.
"Ban san me yake faruwa ba, a can sai naga an saka sunana a cikin wadanda za su zama ministoci, ina dubawa sai naga sunana."

Har ila yau, Pantami ya bayyana kalmar da Buhari ya fada masa bayan ya je shi gare shi yin godiya da abin alheri da ya yi masa.

Kara karanta wannan

Bayan bidiyon Ummi Nuhu, Mai Dawayya ya yi tone tone, ya faɗi shura da ya yi a baya

"Ban sani ba, bai shawarce ni ba, babu wanda na sani da ya je ya ce a saka sunana, a kashin kansa ya rubuta sunana.
"Daga baya, na same shi na ce ranka ya dade na dauka ka manta da ni, ya ce mani mutum yana mantawa da masoyinsa ne."

- Cewar Pantami a bidiyon

Pantami ya yi kyauta ga masoyin Buhari

Mun ba ku labarin cewa wani bawan Allah a Bauchi ya sanya wa dansa suna Muhammadu Buhari domin girmamawa.

Tsohon Ministan sadarwa, Farfesa Isa Ali Pantami, ya tura masa kyautar N200,000 domin sayan rago don bikin suna.

Malam Danladi Mai Kaset ya ce ya samu sakonni daga jihohi daban-daban da suka yaba masa, ya kuma roki Allah ya albarkaci jaririn.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.