Jiragen Yaki Sun Kona 'Yan Bindiga Kurmus Suna Bikin Aure a Dajin Zamfara

Jiragen Yaki Sun Kona 'Yan Bindiga Kurmus Suna Bikin Aure a Dajin Zamfara

  • Jiragen yakin rundunar sojin saman Najeriya sun kai gagarumin hari a wurin liyafar auren ’yan bindiga a Tsafe, Zamfara
  • Rahotanni sun tabbatar da mutuwar da dama a cikinsu, yayin da wasu da suka jikkata suka nemi mafaka a kauyuka na kusa
  • Harin ya zo ne karkashin atisayen rundunar Operation Fansar Yamma da ke yaki da ’yan ta’adda a jihohin Arewa maso Yamma

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Zamfara – Rundunar sojin saman Najeriya ta kai wani gagarumin hari a kan wasu ‘yan bindiga da suka hallara domin bikin aure a tsaunin Asaula da ke Tsafe a jihar Zamfara.

Harin, wanda aka kai da tsakar rana a ranar Talata, 5 ga watan Agusta, 2025 ya jawo asarar rayuka da dama daga cikin ‘yan bindigar, yayin da sauran suka tsere da raunuka.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun gwabza da 'yan bindiga a Zamfara, an samu asarar rayuka

Jiragen yaki yayin da suka kai wani hari
Jiragen yaki yayin da suka kai wani hari. Hoto: Nigeria Air Force
Source: Getty Images

Mai sharhi kan lamuran tsaro, Zagazola Makama ya wallafa a X cewa farmakin na cikin matakan da sojoji ke dauka wajen magance matsalar tsaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahotanni sun nuna cewa harin ya biyo bayan sahihan bayanan leken asiri da suka tabbatar da taruwar ‘yan bindiga daga wurare daban-daban domin gudanar da bikin auren.

Yadda sojoji suka farmaki 'yan bindiga

Wasu majiyoyi sun ce da misalin karfe 2:44 na rana ne rahotanni suka tabbatar da kasancewar dimbin ‘yan bindiga dauke da manyan makamai da babura sama da 100 a wurin taron.

Nan take, rundunar Operation Fansar Yamma ta tura jiragen yaki daga bangaren rundunar sojin sama ta Najeriya (NAF) domin kai hari kan ‘yan ta’addan.

Jirgin yaki ya isa wurin da misalin karfe 4:00 na yamma, inda ya kaddamar da luguden wuta yayin da taron ke tsakiyar gudana, wanda hakan ya rutsa da da dama daga cikin su.

Jirgin sojoji ya kona 'yan bindiga kurmus

Kara karanta wannan

'Yan ta'addan Boko Haram sun sha azaba a hannun sojoji, an tura miyagu barzahu

Majiyoyi sun ce an kashe ‘yan bindiga da dama nan take, yayin da wasu da dama daga cikinsu suka jikkata.

An kuma ga ragowar da suka tsira na kokarin kwashe gawa da wadanda suka jikkata zuwa kauyen Yankuzo domin neman agaji.

Rahoton leken asiri na baya-bayan nan ya tabbatar da gano gawa akalla 10 da ake iya gane su, yayin da wasu da dama suka kone kurmus har ba za a iya gane su ba.

Rahoton tashar TVC ya nuna cewa akalla ‘yan bindiga 33 da suka jikkata yayin da aka yi musu ruwan wuta ta sama.

Jagoran 'yan ta'adda, Bello Turji da ake rade radin ya mika wuya
Jagoran 'yan ta'adda, Bello Turji da ake rade radin ya mika wuya. Hoto: Imran Muhammad
Source: Facebook

Wasu rahotanni sun bayyana cewa wasu daga cikin ‘yan bindigar na samun magani a boye a wasu kauyuka.

Don haka, majiyoyi sun shawarci rundunar soji da ta tura dakarun kasa domin kammala bincike a wuraren da aka kai harin da kuma kauyukan da ake zargin ana yi wa ’yan bindigar jinya.

An kama mai taimakon Boko Haram

A wani rahoton, kun ji cewa dakarun sojin Najeriya sun kama wani matashi da ake zargi yana taimakon 'yan Boko Haram a Borno.

Kara karanta wannan

Bayan ikirarin mika wuya, yaran Turji sun yi kisa a mummunan harin da suka kai

An kama matashin ne dauke da rabobi a cikin buhuna cike da man fetur yana shirin tafiya da su iyakar Najeriya da kasar Kamaru.

Baya ga kama shi da man fetur, wasu rahotanni sun nuna cewa an same shi da wasu kayayyakin tsafi da ake zargin na 'yan ta'addan ne.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng