Wata Sabuwa: Soja Ya Daɓawa Ɗan Sanda Wuƙa har Lahira, Jami'an Tsaro Sun Haɗa Kai
- Ana zargin wani matashin soja ya daba wa ɗan sanda wuka har lahira a unguwar Mayo-Goyi, Jalingo a jihar Taraba
- Sojan wanda bai dade da shiga aikin ba da ake kira Dauda Dedan ya aikata hakan ne ga Aaron John wanda ya yi sanadin rayuwarsa
- Rahoton ‘yan sanda ya ce rikici tsakanin soja da mazauna ya jawo hatsaniyar da ta kai ga mutuwar ɗan sandan cikin dare
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Jalingo, Taraba - An samu tashin hankali bayan rigima ta kaure tsakanin dan sanda da kuma soja a jihar Taraba.
Ana zargin wani soja, Dauda Dedan ya daba wa ɗan sanda, Aaron John, na rundunar Taraba wuka har lahira a Jalingo.

Source: Twitter
Jami'in hulɗa da jama’a na ‘yan sandan jihar, James Lashen, ya tabbatar da lamarin ga manema labarai a Jalingo ranar Laraba, cewar Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An kashe wani dan sanda a Adamawa
Wannan dai ba shi ne karon farko ba da ake samun matsala tsakanin wasu daga cikin jami'an sojoji da 'yan sanda a Najeriya.
Ko a shekarar 2023 an samu hatsaniya tsakanin yan sanda da sojoji wanda ya yi ajalin wani daga cikin jami'an dan sanda.
Wani dan sanda ya rasa ransa yayin wani arangama tsakanin sojoji da 'yan sanda wanda ya afku a a jihar Adamawa a Arewacin Najeriya.
Rahotanni sun tabbatar da cewa hatsariniyar ta yi ajalin jami'in dan sanda mai suna Jacob Daniel wanda tuni aka ɗauki matakin da ya dace.

Source: Original
Yadda soja ya hallaka dan sanda a Taraba
Kakakin yan sanda, Lashen ya ce lamarin ya faru da misalin ƙarfe 9:00 na dare a ranar Litinin a Mayo-Goyi, wata unguwa da ke Jalingo.
Ya bayyana cewa marigayi John ya samu kiran gaggawa daga mazauna yankin kan wata takaddama tsakaninsu da sojan, inda ya shiga tsakani aka daba masa wuka.
Lashen ya bayyana cewa sojan ya tsere bayan lamarin, kuma rundunar soji ta fara bincike don gano inda yake domin hukunta shi, Sahara Reporters ta tabbatar da batun.
Ya ce:
"Muna da tabbacin cewa rundunar soji za ta kamo sojan da ya tsere domin ya fuskanci cikakken hukunci.
"Muna aiki tare da rundunar soji, mun je gidan sojan domin tabbatar da kama shi domin ya fuskanci hukunci daidai da abin da ya aikata."
Lashen ya jaddada cewa dangantakar da ke tsakanin sojoji da ‘yan sanda a jihar na da kyau kuma suna ci gaba da aiki tare.
Sojoji sun daku da 'yan sanda a Delta
A baya, mun ba ku labarin cewa rundunar sojin saman Najeriya ta bayyana cewa ta dauki mataki kan rikicin da ya faru tsakanin wasu jami’anta da ‘yan sanda a jihar Delta.
Jami’in hulda da jama’an sojojin, AVM Olusola Akinboyewa, ya ce an dauki matakan da suka dace don inganta fahimtar juna tsakanin jami’an tsaro.
An tabbatar da cewa an kula da ‘yan sandan da suka jikkata yayin da jami’an tsaron da suka yi hannun riga ke fuskantar hukunci bisa ka’idojin soja.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

