'Yan Ta'adda Sun Yi Garkuwa da Basaraken Zamfara Yana tsaka da Ƙoƙarin Barin Gari

'Yan Ta'adda Sun Yi Garkuwa da Basaraken Zamfara Yana tsaka da Ƙoƙarin Barin Gari

  • Basaraken garin Yankuzo a jihar Zamfara, Alhaji Babangida Kogo, ya fada hannun ƴan bindiga da suka kai wa tawagarsa hari
  • Rahotanni sun ce basaraken ya yi ƙoƙarin tserewa daga garin saboda fargabar ramuwar gayya daga ƴan ta’adda da aka kai wa farmaki
  • Rundunar sojojin saman Najeriya ta kai mummunan farmaki kan taron wasu ƴan bindiga a dajin dake tsakanin Yankuzo da Munhaye

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Zamfara Wasu ƴan bindiga sun sace basaraken garin Yankuzo, Alhaji Babangida Kogo, da ke ƙaramar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara.

Ƴan ta'adda da sun yi garkuwa da basaraken bayan luguden wuta da jiragen rundunar sojin saman Najeriya (NAF) suka yi a wani dajin kusa da garin, wanda ya halaka ɗaruruwan ƴan ta’adda.

Kara karanta wannan

An so a tashi gari, ƴan sandan Kaduna sun gano bam aka ɓoye a kayan gwangwan

Yan ta'adda sun kai hari Zamfara
'Yan ta'adda sun sace basaraken Zamfara Hoto: @ZagazOlaMakama
Asali: Twitter

Zagazola Makama, wanda ya wallafa batun a shafinsa na X, ya ce sace basaraken ne da yammacin ranar Talata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An bayyana ƴan ta'addan sun kama shi ne a kan hanyar Mararraba, yayin da yake ƙoƙarin barin garinsa saboda fargabar ramuwar gayya daga ƴan ta’addan da jiragen sama suka kai wa farmaki.

Ƴan ta'adda sun sace basarake a Zamfara

Rahotanni sun ce ƴan bindiga da dama dauke da makamai ne suka mamaye yankin a kan babura sama da goma.

Sun tare basaraken tare da tawagarsa a kusa da gonar tsohon marigayin Alhaji Malami Yandoto, inda suka dauke shi suka bar sauran a nan.

A ranar da aka sace basaraken, rundunar sojin sama ta kai wani farmaki na musamman a dajin da ke tsakanin Yankuzo da Munhaye.

Dakarun sojin saman Najeriya
'Yan ta'adda sun kai harin ramuwar gayya Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Facebook

An kai harin bayan rundunar ta samu tabbacin cewa wasu shugabannin ƴan ta’adda sun hallara domin wani taro, da ake zargin ko biki ne ko wata liyafa.

Kara karanta wannan

Ana murnar Bello Turji ya miƙa wuya, ƴan bindiga sun tarfa mutane 150 a Zamfara

An kai harin ne bisa sahihan bayanan leƙen asiri da kuma bin na’urorin gano motsi daga sama, inda aka gano fiye da ƴan bindiga 100 sun taru a wurin.

Yaran Turji sun zauna bayan zama da malamai

Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa taron ya haɗa da mayaƙa masu biyayya ga manyan shugabannin ƴan ta’adda da ke aiki a yankin Tsafe zuwa Zurmi da na dazukan Katsina da Sokoto.

Wata majiya ta tsaro ta bayyana cewa:

"Harin ya yi ƙamari. Gawarwaki sun ƙone kurmus, babura sun lalace – duka suna warwatse a wurin bayan farmakin."

Bayan harin, an shiga fargabar cewa za su dawowa ramuwar gayya, inda da dama suka fara gudun hijira saboda tsoron ƴan ta'addan.

Wani mazaunin yankin Yankuzo ya ce:

"Mun san za su dawo su rama. Shi ya sa hakiminmu ya ke ƙoƙarin barin gari. Abin takaici, sai dai sun cimmasa kafin ya samu mafaka."

Majiyoyin ƴan sa-kai sun tabbatar da cewa ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano inda basaraken ya ke.

Kara karanta wannan

An kuma: Tinubu ya gwangwaje ƴan wasan D'Tigress da $100,000 da gidaje a Abuja

A halin yanzu kuma, sojoji na ƙasa sun isa yankin domin dakile yiwuwar sake kai wani hari.

Sulhu da Turji ya bar baya da ƙura

A baya, kun ji cewa Bello Turji, daya daga cikin fitattun shugabannin ƴan bindiga a yankin arewa maso yamma, ya sako mutane 32 da aka daɗe da garkuwa da su.

An samu nasarar ceto mutanen ne bayan tattaunawa da wasu malamai da kuma jami'an gwamnatin tarayya a asirce a ƙoƙarin da ake yi na tabbatar da sulhu da Turji.

Duk da cewa wasu na kallon wannan lamari a matsayin wata dama don samun zaman lafiya, shugabanni a yankin na ganin za a kuma tafka kuskuren da aka yi a baya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng