'Akwai Barayi fa': Sarki Sanusi II Ya Yi Gargaɗi kan Naɗa Wasu Muƙamai, Ya Faɗi Illarsu
- Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya aika sako da gwamnati kan nada wasu mutane da ba su cancanta ba muƙami
- Sarki na 16 ya ce bai kamata a rika ba wa barayi mukaman gwamnati ba, yana mai cewa hakan na lalata ƙimar al'umma
- Basaraken ya bayyana cewa mutane da dama da ke rike da mukamai a gwamnati ba su da tarbiyya
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya ba shugabanni shawara kan nada barayi mukamai.
Sarkin Kano ya koka da yadda daraja da dabi'u suka lalace a sassa daban-daban na al'ummar Najeriya a yau.

Source: Twitter
Muhammadu Sanusi II ya yi gargadi kan nada barayi
Basaraken ya bayyana haka ne yayin hira da gidan talabijin na Channels a shirin Politics Today a yau Laraba.
Sanusi II ya ce ya zama dole a daina bai wa mutane da suka wawuri dukiyar ƙasa damar sake samun mukaman gwamnati ko damar jagoranci.
Mai martaba ya ce mutane da dama a cikin gwamnati ba su samu tarbiyya ba, shi yasa sukan aikata abubuwa marasa da’a da kima.
Ya ce:
“Tasirin dabi'u a ƙasar nan gaba ɗaya ya lalace, wasu na shiga gwamnati ne domin neman kuɗi, amma ba domin neman kuɗi ake shiga gwamnati ba.
“An dade ana mulkar mu da mutane marasa daraja; Ba su da suna, kuma ba sa fatan barin suna mai kyau a baya.
“Waɗannan mutane sukan auna kansu da dukiyar da suka mallaka, irin gidajensu, jiragen sama ko kuɗin da ke asusun banki.
“Ba su damu da yadda jama'a ke kallonsu ba a matsayin barayi ko azzalumai da suka cinye dukiyar kasa."

Source: Twitter
Sanusi II ya fadi matsalar wasu yan siyasa
Sarkin ya bayyana cewa abin da yafi damunsu shine dukiya, ba yadda al’umma ke kallon su ko amana da tarihin da za su bari ba.
Sanusi ya tuna da rayuwar tsohon shugaban soja Marigayi Murtala Muhammed, yana mai cewa Najeriya na bukatar sabunta darajar al'ummarta.
Ya ce duka shugabanni da ‘yan kasa ne ke da alhakin sake gina nagartattun dabi’u a cikin al’umma baki ɗaya.
A cewarsa, dukiya ba ta kamata ta fi gaskiya, aiki tukuru da tausayi muhimmanci ba; al'umma na bukatar juyin dabi’u.
Ya kara da cewa:
“Al'umma da ke girmama dukiya, ko da an samu ta hanyar sata, za ta ci gaba da haifar da irin waɗannan munanan halaye.
“Ba mu tsanar barayi da ke mulki; sai ma mu ƙara ba su mukamai da damarmakin sata, wannan ce Najeriya a yau."
Sarki Sanusi II ya shawarci farfaɗo da ayyukan yi
Mun ba ku labarin cewa Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya shawarci gwamnatin tarayya ta gyara kamfanin auduga na Najeriya (UNTL).
Sarkin ya bayyana cewa kamfanin na samar da ayyukan yi akalla 10,000, yana mai cewa rufe shi babbar matsala ce ga Kaduna da Arewa.
Karamin ministan masana'antu, Sanata John Enoh ne ya jagoranci masu ruwa da tsaki ciki harda Sanusi II zuwa kamfanin a Kaduna.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

