Mutuwar Ministoci 2 Lokaci Guda Ta Girgiza Shugaba Bola Tinubu, Ya Yi Masu Addu'a
- Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya jajantawa takwaransa na ƙasar Ghana, Jonh Mahama bisa rasuwar ministocinsa biyu da wasu mutum shida
- Ministan tsaron Ghana da ministan Muhalli na cikin mutane takwas da suka rasa ransu sakamakon hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu ranar Laraba
- Bola Tinubu ya yi alhinin wannan hatsari tare da mika sakon ta'aziyya a madadin gwamnatin Najeriya ga ƴan uwa da abokan arziki na ƙasar Ghana
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana jimami da alhini bisa rasuwar ministoci biyu da wasu jami'an gwamnatin kasar Ghana a hatsarin jirgin sama.
Bola Tinubu ya miƙa sakon ta'aziyya a madadin Najeriya ga Shugaba John Mahama, gwamnatin Ghana da al’ummar ƙasar, bisa hadarin jirgin sama da ya auku.

Source: Twitter
Mai magana da yawun shugaban Najeriya, Bayo Onanuga ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X yau Laraba, 6 ga watan Agusta, 2025.

Kara karanta wannan
Ministoci, tsohon ɗan majalisa da mutum 5 sun mutu a mummunan hatsarin jirgin sama a Ghana
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ministoci 2 sun rasu a hatsarin jirgin Ghana
Hatsarin jirgin saman mai saukar angulu ya yi sanadiyyar rasuwar Ministan Tsaron Ghana, Edward Omane Boamah, Ministan Muhalli, Ibrahim Murtala Muhammed, da wasu mutane shida.
Fadar Shugaban Ƙasar Ghana ce ta sanar da afkuwar wannan haɗari, sa’o’i baya rundunar sojin ƙasar ta bayyana cewa wani jirgin sama mai saukar ungulu da ke ɗauke da mutane takwas ya sauka daga hanya.
Tinubu ya kaɗu da jin labarin hatsarin jirgin
A sanarwar da Bayo Onanuga ya fitar, Shugaba Tinubu ya bayyana kaɗuwarsa bisa faruwar wannan hatsarin, tare da miƙa jajen gwamnatin Najeriya ga al'ummar Ghana.
Shugaba Bola Tinubu ya kuma yi addu’ar Allah Ya jiƙan waɗanda suka rasu, tare da yi wa iyalansu da dukan al’ummar Ghana addu’ar ƙarfafa zuciya da juriya a wannan yanayi.

Source: Twitter
Shugaba Tinubu ya yi wa mamatan addu'a
Sanarwar ta ce:
"Shugaba Tinubu ya tabbatar wa Shugaba Mahama da daukacin al’ummar Ghana cewa gwamnatin da al’ummar Najeriya na tare da su a wannan lokaci da suka tsinci kansu na jimami.

Kara karanta wannan
A karshe, Tinubu ya magantu game da 'yan Yobe da suka lashe gasar Turanci a London
"Shugaban Najeriya ya roƙi iyalan da wannan jarabawa ta afka masu da abokan arziki da su kwantar da hankulansu kuma su samu natsuwa saboda 'yan uwansu sun rasu ne a wajen yi wa ƙasarsu hidima.
“Bola Tinubu ya kuma yi addu’ar Allah Ya yi wa waɗanda suka mutu rahama, Ya kuma ba iyalan da suka bari ƙarfin zuciya da juriyar rashinsu."
Jirgin sojin sama ya yi hatsari a Venezuela
A wani rahoton, kun ji cewa jirgin rundunar sojin saman Venezuela ɗauke da mutane 10 ya yi hatsari a dajin Amazon inda aka rahoto cewa an samu asarar rayuka.
Ma’aikatar tsaron Venezuela ta ce mutum uku sun tsira daga haɗarin, ciki har da matukin jirgin, kuma haɗarin ya faru ne sanadiyyar tangarɗar na'ura.
Hatsarin jirgin sojin saman Venezuela ya shiga cikin jerin haɗurran jiragen sama da suka faru a duniya a kasa da wata biyu ciki har da wanda ya faru a jirgin Air India.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng