Dakarun Sojoji Sun Gwabza da 'Yan Bindiga a Zamfara, an Samu Asarar Rayuka

Dakarun Sojoji Sun Gwabza da 'Yan Bindiga a Zamfara, an Samu Asarar Rayuka

  • Dakarun sojojin Najeriya masu aikin samar da tsaro sun samu nasara kan tsagerun 'yan bindiga a jihar Zamfara
  • Sojojin tare da hadin gwiwar 'yan sa-kai sun samu nasarar dakile wani yunkurin kai hari da 'yan bindigan suka yi a karamar hukumar Tsafe
  • Jami'an tsaron sun samu nasarar hallaka 'yan bindiga masu yawa tare da kwato makamai bayan sun yi gumurzu da masu addabar bayin Allah

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Zamfara - Dakarun sojoji na rundunar Operation Fansan Yanma tare da haɗin gwiwar yan sa-kai, sun gwabza da ‘yan bindiga a jihar Zamfara.

Dakarun sojojin sun yi fafatawar ne a wani mumunan artabu da ya faru da safiyar tanar Laraba a gabashin yankin karamar hukumar Tsafe da ke jihar Zamfara, inda suka kwato bindigogi kirar AK-47 guda uku.

Sojoji sun dakile harin 'yan bindiga a Zamfara
Sojoji sun kashe 'yan bindiga a Zamfara Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ne ya bayyana hakan a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

'Yan ta'addan Boko Haram sun sha azaba a hannun sojoji, an tura miyagu barzahu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sojoji sun ragargaji 'yan bindiga a Zamfara

Binciken da aka gudanar ya nuna cewa rikicin ya faru ne sakamakon yunkurin da ‘yan bindigan suka yi na kawo hari.

Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa an hango ‘yan bindigan suna kokarin shigowa garin Tsafe.

Sai dai, dakarun sojoji tare da ‘yan sa-kai sun yi gaggawar dakile yunkurin nasu, suka kuma shiga fafatawa da su wadda ta dauki dogon lokaci.

"An kashe ‘yan bindiga da dama a yayin artabun, kuma an kwato bindigogi kirar AK-47 guda uku."
"Dole aka tilastawa ‘yan bindigan suka ja da baya bayan sun samu rauni mai yawa, duk da cewa ba a tabbatar da adadin gawarwakin da aka samu ba tukuna."

- Wata majiya

Majiyar ta kara da cewa an tura karin jami'an tsaro na sojoji zuwa yankin domin kara samar da tsaro a yankin.

Dakarun sojoji sun kara shiga zurfin dajin da ‘yan bindigan ke fakewa, inda suka ci gaba da bin sawunsu.

Kara karanta wannan

Bayan ikirarin mika wuya, yaran Turji sun yi kisa a mummunan harin da suka kai

Wannan hari ya zo ne a lokacin da gwamnatin tarayya ke ƙoƙarin ƙara ƙaimi wajen fatattakar ‘yan bindiga da masu tada zaune tsaye a yankin Arewa maso Yamma, musamman a jihohin Zamfara, Katsina da Sokoto.

Sojojo sun kashe 'yan bindiga a Zamfara
Dakarun sojoji sun ragargaji 'yan bindiga a Zamfara Hoto: Legit.ng
Source: Original

Karanta wasu labaran kan sojoji

Sojoji sun hallaka 'yan ta'addan Boko Haram

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojoji sun samu nasara kan 'yan ta'addan Boko Haram a jihar Borno.

Sojojin sun hallaka 'yan ta'adda bayan sun yi musu kwanton bauna lokacin da suke tafiya a cikin daji.

Jami'an tsaron sun kuma kwato makamai masu yawa tare da raunata tsageru da dama bayan sun yi artabu mai zafi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng