Fasinjojin Kano 22 Sun Mutu a Hanyar Neja, Tirela Dauke da Mutum 42 Ta Yi Hatsari
- Wani hatsarin motar tirela a hanyar Lambata zuwa Lapai ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 22 tare da jikkatar wasu 20
- Tirelar na dauke da mutane da dabbobi daga Kano zuwa Legas lokacin da ta yi hatsari da karfe 3:00 na daren Litinin, 4 ga Agusta
- Hukumar FRSC ta danganta hatsarin da gudun wuce sa’a da lodin da ya wuce kima, inda ta gargadi direbobi kan tafiyar dare
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Neja - Wani mummunan hatsarin mota ya rutsa da wata motar tirela a hanyar Lambata zuwa Lapai da ke jihar Neja, inda mutane 22 suka mutu.
An rahoto cewa motar tirelar na dauke da dabbobi da kuma mutane 42 a lokacin da ta yi hatsari a ranar Litinin, 4 ga Agusta, 2025.

Source: Facebook
Mutane 22 sun mutu a hatsarin tirela

Kara karanta wannan
Ministoci, tsohon ɗan majalisa da mutum 5 sun mutu a mummunan hatsarin jirgin sama a Ghana
Hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) reshen jihar Neja ta sanar da cewa mutane 20 da suka tsira a hatsarin, sun samu munanan raunuka, inji rahoton The Guardian.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahoton ya ce shugabar hukumar, Aishat Sa'adu ta bayyana cewa hatsarin ya afku ne da misalin karfe 3:00 na dare.
Tirelar, wacce ta baro Kano na yi hatsari kilomita 10 daga Lambata, sannan kilomita 30 daga Lapai, a hanyarsu ta zuwa jihar Legas.
Aishat Sa'adu, wacce ta shiga cikin jami'anta wajen ceto wadanda hatsarin ya shafa, ta ce mutane 22 sun mutu nan take yayin da aka kwashe gawarsu zuwa babban asibitin Suleja.
"Laifin gudun wuce sa'a ne" - FRSC
Ta ce an kwashe sauran mutane 20 da suka rayu zuwa cibiyar kiwon lafiya ta tarayya da ke Lambata domin ganin an ba su agajin gaggawa.
Shugabar hukumar ta alakanta wannan hatsari da gudun wuce sa'a, tana mai cewa FRSC ta dade tana gargadi kan yin lodin da ya wuce sa'a, musamman hada dabbobi da mutane ko kaya a cikin mota daya.
"Mun tare muna jan hankalin mutane a kan wannan mummunar dabi'ar, amma ina, ba sa ji, kullum za ka ga suna loda mutane, kaya da dabbobi a waje daya."
- Aishat Sa'adu.

Source: UGC
FRSC ta gargadi direbobi kan tuki da dare
Punch ta rahoto shugabar hukumar ta kuma bayyana irin hadarin da ke tattare da yin tafiye-tafiye da tsakar dare, inda ta ce direbobi ba sa jin shawarwarin da ake ba su kan illar yin hakan.
Ta ce:
"Mun sha mu shirya tarukan wayar da kan jama'a da masu ruwa da tsari kan illar yin tuki da daddare, amma mutane sun koma kamar sun fi jin dadin yin tafiya da dare."
Ta tabbatar da cewa an kira sashen kai daukin gaggawa na hukumar FRSC, inda suka garzaya wurin da hatsarin ya faru tare da ceto wasu daga cikin fasinjojin.
Hatsarin tirela ya yi ajalin mutum 7
A wani labarin, mun ruwaito cewa, hatsarin mota a kan titin Kaltungo-Cham ya yi sanadin mutuwar mutane bakwai, yayin da wasu 31 suka jikkata.
Hukumar kiyaye hadurra ta jihar Gombe ta danganta hatsarin da matsalar birki, wanda ya jawo kifewar tirela dauke da mutane 38.
FRSC ta gargadi mutane da su guji hawa tirela ko manyan motoci da nufin yin tafiye-tafiye, "domin an yi su ne don daukar kaya kawai".
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
