NSCDC Ta Kara Kamen Dilan Kwaya a Kano bayan Gagarumin Samame

NSCDC Ta Kara Kamen Dilan Kwaya a Kano bayan Gagarumin Samame

  • Jami’an NSCDC a jihar Kano sun kama wani mutum mai suna Basiru Ahmed, ɗan shekara 42 a unguwar Salanta, karamar hukumar Gwale
  • Wannan ya faru ne bayan an same shi da buhuna fiye da 106 na tabar wiwi bayan an samu bayanan sirri cewa ana buga cinikin tabar
  • Bayan kamun Basiru, hukumar NSCDC ta mika shi ga hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta kasa (NDLEA)

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Jami’an Hukumar Tsaro ta NSCDC reshen Jihar Kano sun cafke wasu mutane biyu da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi da kuma fasa gidaje a wasu yankuna na jihar..

Mai magana da yawun rundunar, Ibrahim Abdullahi, ne ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Jiragen sojojin sama sun saki bama bamai a dajin Zamfara, an hallaka miyagu 100

Jami'an NSCDC
NSCDC ta kama dillalin kwata a Kano Hoto: @official_NSCDC
Asali: Twitter

Punch ta wallafa cewa Ibrahim Abdullahi ya ce an kama ɗaya daga cikin wadanda ake zargi ne bisa sahihan bayanan leƙen asiri.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kara da cewa an kuma kama shi a lokacin da yake sayar da kuma raba miyagun ƙwayoyi ga jama’a cikin al’umma.

NSCDC za ta kama dillalan ƙwaya a Kano

NSCDC ta bayyana cewa jami’anta sun sake samun nasara a yaki da laifuffuka, bayan da suka kama wasu mutane biyu a samame daban-daban da aka gudanar a Kano.

Ya shaida wa Legit cewa:

"A samame na farko, jami’an NSCDC sun kama wani da ake zargi da safarar ƙwaya, Basiru Ahmed, mai shekaru 42, a Salanta, karamar hukumar Gwale, tare da wasu abubuwa da ake zargin tabar wiwi ce."
"An kama wanda ake zargi da buhuna sama da 106 na tabar wiwi, kuma tun daga lokacin aka mika shi ga hukumar yaƙi da fataucin miyagun ƙwayoyi ta jiha domin ci gaba da bincike da ɗaukar matakin shari’a da ya dace."

Kara karanta wannan

'Yan sandan Kano sun fara binciken kisan 'ɗan fashi' bayan koken uwarsa

Jami'an NSCDC sun kama barawo a Kano

A wani lamari makamancin haka, jami’an NSCDC sun kama wani matashi mai suna Muhammad Abbas mai shekara 22 a unguwar Gurungawa da ke Karamar Hukumar Kumbotso.

An kama shi ne bisa zargin fasa gidaje da sace kadarori masu darajar dubunnan Naira tare da jefa jama'ar yankin a cikin fargaba.

Taswirar jihar Kano
NSCDC ta nemi hadin kan jama'ar Kano Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Sanarwar ta kuma bukaci al’umma da su ci gaba da kasancewa masu lura da abin da ke faruwa a yankunansu tare da samar da bayanai a kan lokaci.

Ya ce bayar da bayanan sirri a lokacin da ya dace zai taimaka matuka a ci gaba da magance ayyukan masu laifi a cikin al’umma.

Dilan kwaya: Kwamishinan Kano ya ajiye aiki

A baya, kun ji Kwamishinan sufuri na jihar Kano, Alhaji Ibrahim Ali Namadi, ya ajiye mukaminsa bayan zarge-zarge da suka shafi belin wanda ake zargi da dillancin kwaya.

Ya ajiye aiki bayan gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ta karbi rahoton kwamitinsa domin gano rawar da ya taka wajen belin Suleiman Danwawu da NDLEA ke shari'a shi.

Namadi ya yanke shawarar ajiye aiki ne duba da nauyin lamarin da kuma kokarin kwantar wa da jama'a hankali, domin ba gwamnati damar ci gaba da gudanar da bincike cikin lumana.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.