Abubuwa 9 da Kwamitin Bincike Ya Gano game da Kwamishinan da Ake Zargi a Kano

Abubuwa 9 da Kwamitin Bincike Ya Gano game da Kwamishinan da Ake Zargi a Kano

  • Kwamitin binciken da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kafa kan zargin da ake wa tsohon kwamishinan sufuri na Kano ya miƙa rahotonsa
  • Ana dai zargin kwamishinan wanda ya yi murabus da hannu wajen karɓar belin dillalin miyagun ƙwayoyi, Sulaiman Aminu Ɗanwawu
  • A rahoton binciken da aka yi, kwamitin ya gano muhimman abubuwa tara game da zargin da ake wa kwamishina, Ibrahim Ali Namadi

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano - Kwamishinan harkokin sufuri na jihar Kano, Ibrahim Ali Namadi, ya ajiye muƙaminsa bayan fuskantar zarge-zarge dangane da alaƙarsa da wani mutum da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi.

Murabus ɗin ya biyo bayan karɓar rahoton kwamitin binciken da aka kafa domin tantance zargin cewa kwamishinan ya tsaya wa Sulaiman Aminu Danwawu, wanda ake zargi da safarar ƙwayoyi, domin samun beli.

Kara karanta wannan

Belin dilan ƙwaya: Kwamishinan Abba a jihar Kano ya yi murabus

Tsohon kwamishinan sufurin Kano, Ibrahim Ali Namadi.
Rahoton kwamitin bincine ya gano abubuwa da dama game da tsohon kwamishinan sufurin Kano Hoto: Ibrahim Namadi
Source: Twitter

Gwamnatin Kano ta tabbatar da murabus ɗin a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya wallafa a Facebook.

Zargin da ake wa kwamishinan ya tayar da ƙura

Wannan lamari ya haifar da ce-ce-ku-ce mai zafi a jihar Kano da ma faɗin ƙasar, inda al’umma ke bayyana rashin jin daɗinsu game da rawar da kwamishinan ya taka a lamarin.

A cewar kwamishinan, ya yanke shawarar yin murabus ne saboda la’akari da damuwar jama’a da kuma girman tasirin al’amarin ga gwamnati da al’umma baki ɗaya, rahoton BBC Hausa.

Abubuwa 9 kwamitin bincike ya gano

Kwamitin da Barista Aminu Hussaini ya jagoranta ya mika rahotonsa a ranar Litinin ga sakataren gwamnatin Kano, inda aka bayyana abubuwa tara da suka fito fili a binciken:

1. Kwamishinan ya amince ya tsayawa Danwawu bisa raɗin kansa a ranar 18 ga Yuli, 2025.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta karɓi rahoton kwamitin bincike kan zargin kwamishina da belin dilan ƙwaya

2. Ya yi rantsuwa a matsayin kwamishina mai ci, tare da alkawarin bin ka’idojin kotu da sharuɗɗan beli har zuwa ƙarshen shari’ar.

3. Ya san cewa matsayinsa na kwamishina, mamba a Majalisar Zartarwa ta Kano, ya ba shi ikon tsaya wa wani bisa tanadin dokar kotu.

4. Kwamishinan bai yi taka-tsantsan ba kafin yanke shawarar tsayawa wanda ake zargi da babban laifi mai nasaba da safarar ƙwayoyi.

5. Ya fahimci girman laifin da ake zargin Danwawu da shi na safarar miyagun ƙwayoyi.

6. Ya karya manufar gwamnatin jihar Kano, wacce ta tsaya kai da fata wajen yaƙi da safara da ta'amali da miyagun ƙwayoyi, musamman dangane da matsalolin da ke shafar matasa.

Gwamna Abba da Ibrahim Ali Namadi.
Kanawa sun nuna damuwa kan zargin alaƙar tsohon kwamishina da dillalin ƙwaya Hoto: Abba Kabir Yusuf
Source: Twitter

7. Ba a samu wata shaida mai kwari ba da ke nuna akwai wata alaƙa ta musamman tsakanin kwamishinan da wanda ake zargi kafin wannan lokaci.

8. Kwamitin bai samu wata shaida da ke nuna an yi amfani da kuɗi ko dukiya ba domin jan hankalin kwamishinan wajen karɓar belin Danwawu.

9. Kwamishinan bai biya kuɗin beli ba, ciki har da Naira miliyan 5 da ake zargin an bayar. Wannan adadi ne kawai da aka ambata a cikin takardar rantsuwar wanda ake tuhuma.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun harbe 'dan limamin Abuja, ya mutu har lahira

Gwamna Abba ya yiwa muƙarrabansa gargaɗi

A wani rahoton, kun ji cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya gargadi kwamishinoni da sauran hadimnsa da su kaucewa duk abin da zai ɓara sunan gwamnatinsa.

Abba ya ce dole ne kowane mamba a Majalisar Zartarwar Kano ya zama mai gaskiya da rikon amana domin guje wa abubuwan da za su bata sunan gwamnati.

Gwamnan ya yi wannan gargaɗi ne a taron majalisar zartarwa karo na 30 da aka gudanar a gidan gwamnati Kano ranar Laraba, 6 ga watan Agusta, 2025.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262