'Dan Shekara 32 Ya Yi Barazanar Kashe Gwamna, Ya Jefa Kansa a Babbar Matsala

'Dan Shekara 32 Ya Yi Barazanar Kashe Gwamna, Ya Jefa Kansa a Babbar Matsala

  • An gurfanar da Rasaq Gafar a kotun Iyaganku bisa zargin barazanar kashe Gwamnan Osun, Ademola Adeleke da tayar da zaune tsaye
  • Lauyan gwamnati ya ce Gafar ya aikata laifin ne a ranar 12 ga Yulin 2025, wanda ya sabawa dokar Oyo ta 2000 sashi 249(D) da 323
  • Kotun ta bayar da belin Gafar kan N2.5m, amma saboda bai iya cika sharudda ba, aka tura shi gidan yari zuwa watan Nuwamba, 2025

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Oyo – An gurfanar da wani matashi mai shekaru 32, Rasaq Gafar, a gaban kotun majistare ta Iyaganku da ke Ibadan bisa zargin barazanar kashe gwamnan Osun, Ademola Adeleke.

Gafar yana fuskantar tuhume-tuhume kan barazanar kisa, barazanar ga rayuwa da kuma tada hankali, wadanda ya musanta aikata wa.

An gurfanar da matashin da ya yi barazanar kashe Gwamna Ademola Adeleke a gaban kotu
Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke zauna a ofishinsa da ke gidan gwamnati a Osogbo. Hoto: @AAdeleke_01
Source: Instagram

Matashi ya yi barazanar 'kashe' gwamna

Kara karanta wannan

Sukar Tinubu: El Rufai ya debo ruwan dafa kansa, APC ta yiasa martani mai zafi

Lauyan gwamnati, Matthew Ojei, ya bayyana cewa wanda ake zargi ya aikata laifin ne a ranar 12 ga Yulin 2025, kamar yadda rahoton Vanguard ya nuna.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matthew Ojei, ya ce wanda ake zargin ya wallafa sakonni a shafukan sada zumunta yana bazarana ga rayuwar gwamnan osun da kuma son tayar da tarzoma.

Lauyan ya kara da cewa laifin da ake zargin Rasaq Gafar ya aikata ya saba da sassan dokokin laifuffuka na jihar Oyo na shekarar 2000, watau sashe na 249(D) da 323.

Osun: Kotu ta tura Gafar zuwa gidan yari

Lauyan da ke kare wanda ake kara, Marvelous Ojeleye, ya roki kotu da ta bada belin Rasaq Gafar a mafi saukin sharadi.

Mai shari’a, Olabisi Ogunkanmi, ta bayar da belin wanda ake kara kan kudi N2.5m tare da masu tsaya masa guda biyu; dole ne daya daga cikinsu ya kasance ya mallaki fili, sannan dayan kuma ya kasance dan uwansa na jini.

Sai dai Gafar bai iya cika sharuddan belin ba, lamarin da ya sa aka tura shi gidan gyaran hali na Agodi.

Kara karanta wannan

2027: Malamin addini ya hango kujerar gwamnoni 7 da ke fuskantar barazana

Mai shari’a, Olabisi Ogunkanmi ta dage sauraron karar zuwa ranar 13 ga Nuwamba, 2025.

Kotu ta daure matashin da ya yi barazanar kashe gwamnan Osun bayan ya gaza cika sharudan beli
Kofar shiga babbar kotun tarayya da ke Abuja. Hoto: @YeleSowore
Source: UGC

Barazanar matashi ga gwamna da cafke shi

Wani rahoto na wata jaridar yanar gizo, MouthpieceNGR ya nuna cewa Gafar ya yi barazanar 'gamawa da rayuwar Gwamna Adeleke' idan har ya kuskura ya koma jam'iyyar APC.

A cikin bidiyon, matashin ya ce sai gwamnan ya gwammace da ma mutuwa ya yi da irin azaba da wulakancin da zai dandana masa.

Tuhumar da ake yi wa Gafar ta samo asali ne daga korafin da babban jami’in tsaron Gwamna Ademola Adeleke, CSP Adefisoye Kazeem da kuma Barista Nurudeen Kareem, mai ba gwamnan shawara kan harkokin shari’a, suka gabatar.

Bisa wannan koke ne jami’an tsaro suka cafke Gafar kuma suka gurfanar da shi a kotun majistare da ke Oyo.

Matashi ya yi barazanar kashe kakakin 'yan sanda

A wani labarin, mun ruwaito cewa, rundunar 'yan sandan Kano ta yi ram da wasu matasa da ake zargi da laifin tayar da hatsaniya a lokacin zanga-zanga.

Kara karanta wannan

Gaba da gabanta: Kotu ta nuna iko bayan hana gwamna zaɓe da naɗa Sarki a jiharsa

Da alama kamen ya yiwa wasu matasa zafi, inda wani Isma'il Yusif ya yi ikirarin kashe kakakin 'yan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Kiyawa.

Matashin ya ce idan har ya hadu da SP Kiyawa, to sai ya kawo karshen rayuwarsa saboda ba ya kaunar ci gaban matasan da ke nuna adawa da azzalumar gwamnati.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com