Yadda Masu Zuba Jari daga Ƙasashen Duniya Suka 'Kunyata' Kano, Gombe da Jihohi 30 a Najeriya
- Najeriya ta samu ƙarin zuba jari a fannoni daban-daban a shekarar 2024 idan aka kwatanta da adadin jarin da aka zuba a 2023
- Sai dai duk da wannan ci gaba da aka samu, masu zuba jari daga ƙasashen ƙetare sun kaucewa jihohi 32 a Najeriya a bara
- Daga cikin waɗannan jihohin da ba su samu masu ziba jari ba a 2024 har da Kano, Katsina, Bauchi da dai wasunsu a sassan ƙasar nan
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Ƴan kasuwa daga kasashen ƙetare da ke shigowa Najeriya suna zuba hannun jari sun ƙauracewa jihohi 32 a sheƙarar 2024.
Alƙaluma sun nuna cewa masu zuba jari daga ƙasashen waje sun yi watsi da jihohi 32 a Najeriya a shekarar 2024, duk da cewa an samu ƙarin zuba jari a wannan shekara.

Asali: Getty Images
An samu karin zuba jari a Najeriya a 2024
Jaridar The Cable ta tattaro cewa a 2024, darajar hannun jarin da ƴan ƙasashen ƙetare suka zuba a Najeriya ya ƙaru da kashi 215%, daga Dala biliyan 3.91 a 2023 zuwa Dala biliyan 12.32 a 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan na ƙunshe ne a cikin rahoton “Jarin da ya shigo Najeriya” na farkon kwata (Q1) na shekarar 2025 da Hukumar Kididdiga ta Ƙasa (NBS) ta fitar a ranar Talata.
Jarin waje na nufin kuɗaɗen da ke shigowa ƙasa daga ƙetare domin zuba jari a fannoni kamar kasuwanci, masana’antu da ayyukan kuɗi.
Jerin jihohi 32 da masu zuba jari suka ƙaurace
A cewar rahoton, jihohi 32 da masu zuba jari suka kau da kansu daga gare su sun haɗa da:
1. Jihar Abia
2. Jihar Adamawa
3. Jihar Akwa Ibom
4. Jihar Anambra
5. Jihar Bauchi
6. Jihar Bayelsa
7. Jihar Benuwai
8. Jihar Borno
9. Jihar Kuros Riba
10. Jihar Delta
11. Jihar Ebonyi
12. Jihar Edo
13. Jihar Enugu
14. Jihar Gombe
15. Jihar Imo
16. Jihar Jigawa
17. Jihar Kano
18. Jihar Katsina
19. Jihar Kebbi
20 Jihar Kogi
21. Jihar Kwara
22. Jihar Nasarawa
23. Jihar Neja
24. Jihar Ogun
25. Jihar Ondo
26. Jihar Osun
27. Jihar Filato
28. Jihar Ribas
29. Jihar Sakkwato
30. Jihar Taraba
31. Jihar Yobe
32. Jihar Zamfara.
Jihohi 8 da ba a zuba jari ba a shekara 6
Bincike ya kuma nuna cewa jihohi takwas daga cikin waɗannan 32 ba su samu ko kwabo daga jarin waje ba tsawon shekaru shida da suka gabata, wato daga 2019 zuwa 2024.
Jihohin su ne, Bayelsa, Ebonyi, Gombe, Jigawa, Kebbi, Taraba, Yobe da kuma Zamfara.
Wannan na nuna irin ƙalubalen da wasu yankuna ke fuskanta wajen jawo hankalin masu zuba jari daga ƙasashen waje.
Ɗangote zai sayar da hannun jari ga ƴan Najeriya
A wani rahoton, kun ji cewa hamshaƙin attajirin nan, Alhaji Aliko Ɗangote ya bayyana shirinsa na bai wa ƴan Najeriya damar mallakar hannun jari a matatarsa.
Ya bayyana cewa matatar tana samar da tan 2,500 na iskar gas a rana domin bunkasa amfani da makamashi wajen girki a gidaje.
Dangote ya ce shirye yake ya hada gwiwa da gwamnatoci, 'yan kasuwa masu zaman kansu da cibiyoyi domin ciyar da harkar man fetur gaba a nahiyar Afirka.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng