Yadda Remi Tinubu Ta Raba Tallafin N4.15bn a Najeriya a cikin Shekara 1

Yadda Remi Tinubu Ta Raba Tallafin N4.15bn a Najeriya a cikin Shekara 1

Tun bayan shigarsu ofis a ranar 29 ga Mayu, 2023, Sanata Oluremi Tinubu ta fara rangadin bayar da tallafi a faɗin ƙasar nan ta gidauniyarta, inda aka raba tallafin da ya kai biliyoyin Naira.

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja – Remi Tinubu ta bayyana cewa duk kuɗin da ake bayarwa a karkashin wannan shiri ba su fito daga asusun gwamnati ba, sai dai tana nemo su ne da kanta domin tallafa wa marasa galihu.

Uwargidan Shugaban Kasa, Remi Tinubu
Remi Tinubu ta raba tallafi a Najeriya Hoto: @oluremitinubu
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa yayin da wasu ke yabawa da waɗannan tallafi, wasu kuma na tambayar inda aka samo kudin.

Suna tambayar ne ganin cewa ofishin Uwar Gidan Shugaban Ƙasa bai da wani kasafi a kundin mulki na Najeriya.

Kara karanta wannan

Ana fargabar mummunar ambaliya a wurare 76 a Kano, Gombe da jihohi 17

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Duk da haka, ta raba tallafi a wurare da dama da suka hada da:

1. Remi Tinubu ta raba N1bn a Neja

Jaridar Channels TV ta rawaito cewa Remi Tinubu ta ba da tallafi a jihar Neja a ranar Talata, inda ta mika N1bn da kayan agaji ga waɗanda ibtila’i ya shafa.

A ziyarar da ta kai Minna don jajanta wa gwamnati da al’umma sakamakon mummunan ambaliya da ta auku a Mokwa, wacce ta hallaka mutane da dama.

Remi Tinubu, matar Shugaban Najeriya Bola Tinubu
Remi ta raba biliyoyin Naira a cikin shekara 1 Hoto: Oluremi Tinubu
Asali: Twitter

Ta ce:

“A matsayina na uwa, ina jin zafin wannan masifa kamar ku, kuma na yi imani da cewa zamu iya shawo kan wannan ibtila’i.”

Uwar gidan Shugaban Ƙasa ta jinjina wa Maigidanta bisa yadda ya gaggauta ba da umarnin a kawo kayan agaji da kuma sake gina gidajen da ruwa ya rushe.

Ta bayyana cewa tallafin ya haɗa da N1bn, buhunan shinkafa 2,000 da takalma don tallafawa wadanda lamarin ya rutsa da su.

Kara karanta wannan

Belin dilan ƙwaya: Kwamishinan Abba a jihar Kano ya yi murabus

2. Tallafin Remi Tinubu ga mutanen Binuwai

Jaridar Punch ta ruwaito cewa a ranar 29 ga Yuli, Uwar Gidan Shugaban Ƙasa ta bada N1bn ga waɗanda harin 'yan ta'adda ya shafa a unguwar Yelwata da ke Karamar Hukumar Guma a Binuwai.

Remi Tinubu ta miƙa tallafin ne a lokacin da ta kai ziyarar jaje a gidan gwamnatin jihar da ke Makurdi bayan an samu rasuwar sama da mutum 100 a watan Yuni, 2025.

Ta kuma sha alwashin ci gaba da baya r da goyon baya ta hannun shirinta na Renewed Hope Initiative domin magance harin da ake kai wa daga wasu iyakokin jihohi.

3. Mai dakin Tinubu ta kai tallafi Filato

A ranar 3 ga Yuli, Remi Tinubu ta ba da N1bn ga wadanda rikice-rikice suka shafa a faɗin Jihar Filato.

Ta bayyana hakan ne yayin ziyarar ta a birnin Jos, inda ta jajanta wa iyalan waɗanda lamarin ya shafa da kuma Gwamnatin Jihar Filato.

Kara karanta wannan

Minista ya kwadaitawa Ibo mulkin Najeriya, ya ce taimakon Tinubu zai kai su Aso Rock

Mai dakin shugaban kasa, Remi Tinubu
Remi ta ce ta samu kudin ne daga asusun tallafinta Hoto: Oluremi Tinubu
Asali: Twitter

Remi Tinubu ta roki sarakunan gargajiya da su taimaka wajen wanzar da zaman lafiya a jihar domin wanzuwar ci gaba.

4.Tarin fuka: Sanata Remi ta ba da tallafi

A watan Maris 2025, Uwar Gidan Shugaban Ƙasa ta ƙara bayar da N1bn domin yaki da cutar Tarin Fuka (TB) a Najeriya.

Ta bayyana haka ne a lokacin wani taron wayar da kai da aka yi a Sauka, Abuja, a cikin shirin bikin ranar TB ta duniya.

Wannan ne karo na biyu da ta ke bayar da irin wannan tallafi, domin a 2024 ma ta yi irin wannan alkawari lokacin da aka naɗa ta a matsayin jakadiyar yaki da TB ta ƙasa da ta duniya.

Ta ce:

“A wannan mataki, zan yi ƙarin alkawarin bayar da N1bn daga RHI domin ci gaba da yaƙi da TB a Najeriya.”

5. Remi ta ba da N100m don inganta ilimi

A watan Mayu, Remi Tinubu ta yi alkawarin ba da Naira miliyan 100 ta hannun Renewed Hope Initiative (RHI) domin tallafa wa shirin Five Cowries Art Education Initiative.

Kara karanta wannan

Talaka bawan Allah: ADC ta fusata da Tinubu zai kashe N712bn a gyaran filin jirgin Legas

Ta bayyana haka ne a yayin liyafar sada zumunta da gamayyar matan Jakadun kasashen waje suka shirya a Abuja.

Matar Shugaban Kasar ta yi kira ga jama’a da su tallafa wa fannin ilimin zane-zane da tallafi, wayar da kai da haɗin gwiwa.

Ta ce:

“A madadin shirin Renewed Hope Initiative, muna ba da Naira miliyan 100 domin tallafa wa nune-nunen zane-zane 5,000 a faɗin Najeriya.”

6.Remi ta ba da N50m ga mata

A watan Fabrairu, Remi Tinubu ta ba da tallafin Naira miliyan 50 domin taimakawa mata ‘yan kasuwa 1,000 a Jihar Kaduna.

An raba tallafin ne ta hannun Matar Gwamnan Jihar Kaduna, Hafsat Uba Sani, wacce ke matsayin Kwamishinar RHI a jihar.

Remi Tinubu ta umarci matar Gwamna da ta baiwa kowace mace daga cikin 1,000, tallafin N50,000 don ƙarfafa kasuwancinsu.

Ta sake jaddada cewa kuɗin da ake bayarwa ba daga asusun gwamnati suke fitowa ba, sai dai ta gidauniyarta ta RHI domin taimakawa ‘yan Najeriya.

Kara karanta wannan

Amnesty Int'l ta dura kan Tinubu da gwamnati ta ƙi tsoma baki shekaru 6 da 'sace' Dadiyata

A lokacin da ta bayar da tallafin N1bn a Filato, ta ce:

“Idan zan riƙe waɗannan kuɗin a aljihuna, wannan tamkar son zuciya ne. Ba haka ya kamata a yi ba.”

Remi ta raba miliyoyi a Gombe, Nasarawa

A wani labarin, mun ruwaito cewa Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta ƙaddamar da rabon tallafin Naira miliyan 50 ga tsofaffi 250 daga jihohin Nasarawa da Gombe.

A jihar Nasarawa, an gudanar da taron rabon tallafin ne a birnin Lafia, inda tsofaffi daga kananan hukumomin jihar suka ci gajiyar shirin domin rage masu radadin rayuwa.

Sanata Remi Tinubu ta bayyana cewa gwamnati ta ware Naira biliyan 1.9 domin rabawa tsofaffi a faɗin Najeriya, ciki har da babban birnin tarayya, Abuja domin saukaka masu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng