Ana Murnar Bello Turji Ya Miƙa Wuya, Ƴan Bindiga Sun Tarfa Mutane 150 a Zamfara
- Ƴan bindiga sun shafe kwanaki huɗu a jere suna kai hare-hare kan bayin Allah a kauyuka daban-daban a jihar Zamfara
- Wannan lamari ya jefa ɗaruruwan mutane cikin ƙunci da zaman ɗar-ɗar, inda bayanai suka nuna maharan sun yi garkuwa da mutum 150
- Hakan na zuwa ne a lokacin da labarin miƙa wuyan ƙasurgumin ɗan bindigar nan, Bello Turji ya bazu a sassan Zamfara da Najeriya baki ɗaya
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Zamfara - 'Yan bindiga sun sace mutane 150 a cikin jerin hare-hare da suka kai kan kauyuka daban-daban a Jihar Zamfara cikin kwanaki hudu da suka gabata.
Rahotanni sun tabbatar da cewa ƴan bindiga sun yi garkuwa da waɗannan mutane ne a daidai lokacin aka fara yaɗa labarin miƙa wuyan Bello Turji.

Source: Original
Gwamnatin Zamfara ta tabbatar da kai hare-hare
Mai magana da yawun Gwamnatin Jihar Zamfara, Mahmud Mohammed Dantawasa, ya tabbatar wa da BBC Hausa faruwar hare-haren da sace mutane masu yawa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai bai tabbatar ko ƙaryata adadin mutanen da aka sace ba, amma ya bayyana cewa gwamnati na ƙoƙarin ceto waɗanda ƴan bindigar duka yi garkuwa da su.
Wannan na faruwa ne a daidai lokacin da fitaccen malamin addinin Musulunci da ke zaune a Kaduna, Sheikh Musa Yusuf Asadus-Sunnah, ya bayyana yadda kwamitin zaman lafiya ke samun nasara.
An yi sulhu da dan bindiga, Bello Turji?
Sheikh Asadus-Sunnah ya ce kwamitin da yake jagoranta ya taimaka wajen cimma yarjejeniya tsakanin ƙasurgumin ɗan bindiga, Bello Turji da gwamnatin tarayya.
Wannan sulhu ya haifar da sakin mutane 32 da aka yi garkuwa da su da kuma mika wasu makamai masu yawa da shugaban dabar ƴan bindigar ya yi.
Sai dai yayin da ake murnar wannan ci gaba, mazauna kauyuka daban-daban a Zamfara sun tabbatar da cewa ƴan bindiga sun sace ƴan uwansu akalla 150, Daily Trust ta ruwaito.
Ƴan bindiga sun sace mutane 150 a Zamfara
Mazauna ƙauyukan da lamarin ya shafa sun ce 'yan bindigar da ke ɗauke da mugayen makamai sun ɗauki tsawon kwanaki huɗu suna kai masu hare-haren.
Kauyukan da lamarin ya shafa sun haɗa da Sabon Garin Damri, Dakko Butsa (wanda ke kan iyaka da Sokoto), da kuma Tungar Abdu Dogo, Tungar Sarkin Daji, Sadeda da Tungar Labi.
Sau da dama 'yan bindigar kan kai farmaki da daddare ko yayin ruwan sama, suna amfani da lokacin da mutane ke barci.
Majiyoyi sun bayyana cewa tabarbarewar hanyoyi a jihar Zamfara na taimakawa 'yan bindiga wajen aikata laifuffuka, kasancewar jami’an tsaro na fuskantar cikas sosai wajen kai dauki cikin gaggawa.
Sulhu da Bello Turji ya bar baya da ƙura
A wani rahoton, kun ji cewa sulhun da aka yi da Bello Turji ya bar baya da ƙura, mutane sun fara nuna damuwarsu kan ci gaban da aka samu.
Duk da wasu na ganin hakan wata dama ce ta zaman lafiya, wasu kuwa suna kallon lamarin a matsayin maimaita kuskuren da aka yi baya.
Alhaji Sani Shinkafi daga karamar hukumar Shinkafi wanda ya taba jagorantar kwamitin yaki da 'yan bindiga a Zamfara, ya soki tattaunawar da Turji.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

