A Karshe, Tinubu Ya Magantu game da 'Yan Yobe da Suka Lashe Gasar Turanci a London
- Dalibai mata uku ne ‘yan Najeriya suka lashe manyan lambobin yabo a gasar TeenEagle ta duniya a birnin London
- Nafisa Abdullahi ta zama gwarzuwar a harshen Turanci, Rukayya Muhammad ta fi kowa kokari a bangaren muhawara
- Hadiza Kashim kuma ta samu lambar yabo, bayan nan aka ji Bola Tinubu ya ce wannan na nuna irin kwazon da ke tattare da matasan Najeriya
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Shugaban Bola Ahmed Tinubu ya taya wasu dalibai mata uku na Najeriya murna bayan sun samu gagarumar nasara a gasar TeenEagle ta duniya da aka gudanar a London.
Daliban sun nuna bajinta a fannoni daban-daban na ilimin Ingilishi, inda kowannensu ta lashe babbar lamba ta yabo.

Asali: Facebook
Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ne ya fitar da bayanin Bola Tinubu a wani sako da ya wallafa a Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wadanda suka yi fice a gasar sune Nafisa Abdullahi Aminu mai shekaru 17 da haihuwa, Rukayya Muhammad Fema mai shekaru 15, da Hadiza Kashim Kalli.
Shugaban kasa ya bayyana jin dadinsa kan wannan nasara, yana mai cewa matasan Najeriya na da irin hazaka da duniya ke bukata.
Rawar da 'yan Yobe suka taka a London
Nafisa Abdullahi ta zama gwarzuwa, inda aka bayyana ta a matsayin daliba mafi hazaka a fannin amfani da harshen Turanci a gasar.
Rukayya Muhammad Fema kuwa ta fi kowa bajinta a fannin muhawara, yayin da Hadiza Kashim ta lashe lambar yabo bisa bajintar da ta nuna a muhawara.
TeenEagle wata babbar gasa ce ta kasa da kasa da ke jan hankalin matasa masu hazaka daga sassa daban-daban na duniya.
Wannan nasara ta bayyana irin irin kyawawan halaye da kwazon da matasan Najeriya ke da su idan aka ba su dama da horo mai kyau.

Kara karanta wannan
Minista ya kwadaitawa Ibo mulkin Najeriya, ya ce taimakon Tinubu zai kai su Aso Rock
Tinubu ya jinjina wa daliban Yobe
Shugaba Tinubu ya jinjina wa makarantu da sauran cibiyoyin ilimi da suka ba wa wadannan ‘yan mata tarbiyya da horo da ya kai su ga wannan mataki.

Asali: Facebook
Ya ce nasarar da suka samu hujja ce da ke nuna cewa tsarin ilimin Najeriya na iya samar da hazikan matasa da za su iya gogayya da takwarorinsu a duk fadin duniya.
Shugaban kasar ya ce zai ci gaba da zuba jari a bangaren ilimi, musamman ta hanyar saukaka hanyoyin samun ilimi ga marasa galihu, ciki har da kafa asusun lamunin ilimi na NELFUND.
Tinubu ya bukace su da su dage da karatu
A karshen sakonsa, Tinubu ya bukaci Nafisa, Rukayya da Hadiza da su ci gaba da dagewa da karatu tare da ci gaba da zama abin koyi ga sauran matasa.
Punch ta wallafa cewa shugaban kasar ya musu fatan alheri tare da musu addu'ar cigaba da samun nasara a rayuwarsu a nan gaba.
Pantami ya nemi a karrama daliban Yobe
A wani rahoton, kun ji cewa tsohon ministan sadarwa, Sheikh Isa Ali Pantami ya taya 'yan Najeriya da suka lashe gasar Turanci a London murna.
Sheikh Pantami ya bukaci gwamnatin tarayya da ta yi wa daliban da malaminsu tarba ta musamman.
Hakan na zuwa ne bayan ganin goma ta arziki da gwamnatin Najeriya ta yi wa 'yan wasan Najeriya da suka ci kofi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng