Bayan Ikirarin Mika Wuya, Yaran Turji Sun Yi Kisa a Mummunan Harin da Suka kai

Bayan Ikirarin Mika Wuya, Yaran Turji Sun Yi Kisa a Mummunan Harin da Suka kai

  • ‘Yan bindiga da ake zargin yaran Bello Turji sun bude wuta kan matafiya, inda suka kashe mutum daya mai shekaru 35
  • Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 5:30 na yamma a kusa da hanyar Isa zuwa Shinkafi
  • Biyo bayan faruwar lamarin, dakarun tsaro sun fatattaki ‘yan ta’addan, inda aka kwato mota da babur a wurin harin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Sokoto - Wasu ‘yan bindiga da ake zargin yaran Bello Turji ne sun kai hari a kan hanyar Isa zuwa Shinkafi da ke jihar Sokoto.

Rahoto ya nuna cewa sun kashe wani matafiyi mai suna Yusuf Isah, kuma lamarin ya faru ne a yammacin ranar Talata, kamar yadda rundunar ‘yan sanda ta tabbatar.

Jagoran 'yan ta'adda a Arewa ta Yamma, Bello Turji
Jagoran 'yan ta'adda a Arewa ta Yamma, Bello Turji. Hoto: Imran Muhammad
Source: UGC

Legit ta tattaro bayanai kan harin ne a wani sako da Zagazola Makama ya wallafa a X a yau Laraba, 8 ga Agusta, 2025.

Kara karanta wannan

Ana fargabar mummunar ambaliya a wurare 76 a Kano, Gombe da jihohi 17

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ce ‘yan bindigar sun tare hanya ne da babura, suka fara harbe-harbe kan motoci da ke wucewa.

Lamarin ya haifar da firgici a tsakanin matafiya da mazauna yankin lura da cewa hari ya zo ne kwanaki kalilan bayan rahotannin da ke cewa Bello Turji ya mika wuya.

Yaran Bello Turji sun harbe Yusuf Isah

Majiyoyi daga yankin sun bayyana cewa ‘yan bindigar da ake kyautata zaton daga bangaren Bello Turji ne, sun tare hanya da kusan karfe 5:30 na yamma.

Sun bude wuta kan motocin da ke wucewa ba tare da tantance su ba, a cikin wannan rikici ne aka harbe Yusuf Isah, wanda nan take ya riga mu gidan gaskiya.

Harin ya sake jaddada matsalar rashin tsaro da ke addabar yankunan Arewa maso Yammacin Najeriya, musamman Zamfara da Sokoto, inda ‘yan bindiga ke addabar mutane da garkuwa da su.

Dakarun tsaro sun fatattaki yaran Turji

Kara karanta wannan

Yaki zai kare: Bello Turji ya ajiye makamai bayan haduwa da malaman Musulunci

Bayan samun rahoton harin, dakarun Operation Fansan Yamma sun gaggauta kai dauki zuwa wurin da lamarin ya faru.

A cewar jami’an tsaro, da isarsu wurin, suka ci karo da ‘yan ta’addan inda aka yi artabu na musayar wuta.

Bayan dan lokaci ana fafatawa, ‘yan bindigar suka janye zuwa cikin dazukan da ke kewaye da yankin da gudu.

Hafsun tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa
Hafsun tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa. Hoto: Defence Headquaters
Source: Facebook

Sai dai dakarun sun samu nasarar kwato wata mota da babur daya a wurin harin, wanda ake zargin barayin suka bari yayin guduwar da sukayi.

A yanzu, ana sa ran hukumomi za su kara zage damtse wajen tabbatar da tsaro da hana sake afkuwar irin wannan hari.

Bello Turji ya mika wuya a Sokoto

A wani rahoton, kun ji cewa jagoran 'yan ta'adda a Najeriya, Bello Turji ya mika wuya bayan tattaunawa da ya yi da wasu malaman addinin Musulunci.

Malamin addini a jihar Kaduna, Sheikh Musa Yusuf da aka fi sani da Asadus Sunnah ne ya bayyana haka bayan wata tattaunawa da ya yi da Bello Turji.

Shehin Malamin ya bayyana cewa sun tattauna a lokuta mabanbanta da dan ta'addan kuma sun yi nasarar sanya shi mika wasu daga cikin makaman shi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng