Sulhu da Turji Ya Bar Baya da Ƙura, an Faɗi Kuskuren da Aka Yi a Tattaunawar a Zamfara

Sulhu da Turji Ya Bar Baya da Ƙura, an Faɗi Kuskuren da Aka Yi a Tattaunawar a Zamfara

  • Sakin mutane 32 da Bello Turji ya yi ya janyo cece-kuce, yayin da wasu ke ganin hakan tamkar dawowa da tsohon kuskure ne.
  • Alhaji Sani Shinkafi ya ce tattaunawar da aka yi da Turji ba ta da amfani, inda ya bayyana ta a matsayin rashin adalci
  • Hakan ya biyo bayan kokarin Sheikh Musa Yusuf Assadus Sunnah da ya ce sun tattauna da dan ta'addan lokuta da dama

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Gusau, Zamfara - Hatsabibin dan bindiga, Bello Turji ya sako mutane 32 da aka sace, bayan tattaunawa da malamai da jami'an gwamnatin tarayya a boye.

Ko da yake wasu na ganin hakan wata dama ce ta zaman lafiya, wasu kuwa suna kallon lamarin a matsayin maimaita kuskuren da aka yi baya.

An soki shirin sulhu da Bello Turji a Zamfara
Sulhu da Turji ya bar baya da kura bayan sakin mutane 32. Hoto: HQ Nigerian Army.
Source: Twitter

Shinkafi ya yi shakkun sulhu da Bello Turji

Kara karanta wannan

A karshe, Tinubu ya magantu game da 'yan Yobe da suka lashe gasar Turanci a London

Rahoton Zagazola Makama ya ce wasu na ganin an koma gidan jiya ne kuma babu tasirin da hakan zai yi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Alhaji Sani Shinkafi daga karamar hukumar Shinkafi wanda ya taba jagorantar kwamitin yaki da 'yan bindiga a Zamfara, ya soki tattaunawar da Turji.

Shinkafi ya bayyana hakan a cikin wata tattaunawa inda ya ce:

“Wannan sulhu ba zai dore ba kuma bai dace ba.”

A cewarsa, tattaunawar da aka yi da Turji ya hada da malamai da jami’an ofishin Nuhu Ribadu da shugaban kwamitin leken asiri na majalisar dattijai.

Ya ce:

“An ce sun gana da shi sau uku a watan Yuli a mafakar Turji, ba a bi ka’ida ba wajen sakin mutanen, shin an duba lafiyar su? Ba a yi hakan ba."
Ana kokwanton sulhu da Bello Turji a Zamfara
Masana tsaro suna fargaba kan maganar sulhu da Bello Sulhu. Hoto: Legit.
Source: Original

'Babu ka'ida a sulhu da Bello Turji' - Shinkafi

Ya ce ba a kai mutanen fadar Sarki ba, ko asibiti ko wajen gwamnati yayin da masu lura da harkokin tsaro suka ce irin wadannan tattaunawa sun sha faruwa a karkashin gwamnonin da suka gabata.

Kara karanta wannan

Bayan ikirarin mika wuya, yaran Turji sun yi kisa a mummunan harin da suka kai

A wancan lokacin an samu dan sulhu ko musayar fursunoni, amma daga baya sai rikici ya sake kunno kai, da karbar haraji da kisan jama’a.

Ya kara da cewa wannan sulhu da Bello Turji bai kunshi sauran shugabannin ‘yan bindiga kamar Mallam Ila, Dan Bokolo da Dogo Gide ba.

Shinkafi ya bayyana cewa akalla kananan hukumomi 40 a Arewa maso Yamma na fama da ‘yan bindiga, amma gwamnati na tattaunawa da mutum daya kacal.

Ya yi gargadi cewa sulhu da mutum daya ba tare da tuntubar sauran ba na iya nuna karancin karfi ko gazawar gwamnati a idon jama’a.

“In har Turji ya sako mutane 32 da wasu makamai kadan, yaya game da sauran da bai sako ba ko shugabannin da ba su shiga ba?"

- Cewar Shinkafi

Shinkafi ya ce bambanci da Boko Haram ko yan Niger Delta, ‘yan bindigar Arewa maso Yamma ba su da wata manufa ko akida sai kudi.

Ya kara da cewa:

“Wadannan mutane na gina daular ta'addanci ne, ba su da wata akida, sai sata, garkuwa da mutane, da hakar ma'adinai ba bisa ka’ida ba."

Kara karanta wannan

Belin dilan ƙwaya: Kwamishinan Abba a jihar Kano ya yi murabus

Ya ce Turji na iya fakewa da sulhu ne kawai don ya samu hutu, ko kariya daga farmakin sojoji ko kuma neman halaltawa.

Masanin tsaro ya yi tone-tone kan Turji

Kun ji cewa mai sharhi kan lamuran tsaro, Sani Shinkafi ya ce gwamnatin tarayya ta dakile rundunar CJTF da CPG daga kashe Bello Turji a Zamfara.

Shinkafi ya ce CJTF da CPG na dab da shafe babin Turji, gwamnatin tarayya ta ce su koma Shinkafi.

A cewarsa, gwamnatin tarayyar ta ce za ta yi sulhu da shugaban ƴan ta'addar, abin da Bello Turji ya ƙi amincewa da shi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.