Ana Fargabar Mummunar Ambaliya a Wurare 76 a Kano, Gombe da Jihohi 17

Ana Fargabar Mummunar Ambaliya a Wurare 76 a Kano, Gombe da Jihohi 17

  • Ma’aikatar Muhalli ta ƙasa ta yi gargaɗi game da yawan ruwa da ka iya haddasa ambaliya a fadin Najeriya
  • Hakan na zuwa ne bayan an yi hasashen ruwan sama mai tsanani a wurare 76 da ke cikin jihohi 19 na Najeriya
  • Wani rahoto ya nuna cewa Gombe da Ogun sun riga sun fara fuskantar karin ruwa tun kafin lokacin hasashen

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta bayyana hasashen aukuwar ambaliya mai tsanani a wasu sassan ƙasar nan.

An yi hasashen ne sakamakon yawan ruwan sama da ake sa ran zai sauka daga ranar 5 zuwa 9 ga watan Agusta, 2025.

Ana hasashen ambaliya a jihohin Najeriya 19
Ana hasashen ambaliya a jihohin Najeriya 19. Hoto: Getty Images
Asali: Original

Punch ta wallafa cewa ma’aikatar muhalli ce ta fitar da wannan gargaɗi a ranar Talata, inda ta buƙaci hukumomi da mazauna yankunan da abin ya shafa su ɗauki matakan kare kansu.

Kara karanta wannan

Bayan ikirarin mika wuya, yaran Turji sun yi kisa a mummunan harin da suka kai

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar sanarwar, an riga an samu yawan ruwa a jihohin Gombe da Ogun, yayin da sauran jihohi irinsu Legas, Filato, Anambra da Delta ma ke fuskantar haɗarin shiga cikin yanayi irin haka.

Jihohi da wuraren da za su fuskanci ambaliya

Gwamnati ta bayyana takamaiman wurare 76 da ke cikin jihohi 19 da ke hasashen haɗarin ambaliya, ga jerin wasu daga cikinsu:

  1. Akwa Ibom: Edor, Eket, Ikom, Oron, Upenekang
  2. Bauchi: Tafawa-Balewa, Azare, Jama’are, Kari, Misau
  3. Ebonyi: Abakaliki, Echara, Ezilo
  4. Cross River: Ogoja, Edor, Obubra
  5. Nasarawa: Keana, Keffi, Wamba
  6. Benue: Gboko, Ugba, Vande-Ikya, Buruku
  7. Kaduna: Jaji, Zaria, Birnin-Gwari, Kafanchan
  8. Kano: Kano, Gezawa, Wudil, Bebeji
  9. Kebbi: Birnin-Kebbi, Bagudo, Jega, Gwandu
  10. Katsina: Daura, Funtua, Bindawa
  11. Gombe: Bajoga
  12. Plateau: Mangu
  13. Jigawa: Dutse, Hadejia, Gumel
  14. Sokoto: Sokoto, Wamakko
  15. Borno: Biu
  16. Yobe: Potiskum, Machina
  17. Zamfara: Anka
  18. Taraba: Donga, Takum
  19. Niger: Kontagora, Rijau

Kiran gwamnati ga jama'ar yankunan

Ma'aikatar muhalli ta ce ya kamata a sanya ido kan al’amura domin hana asarar rayuka da dukiyoyi.

Kara karanta wannan

Belin dilan ƙwaya: Kwamishinan Abba a jihar Kano ya yi murabus

Ta bukaci hukumomin jihohi da kananan hukumomi su tuntuɓi mazauna yankunan da ke cikin haɗari domin gaggauta daukar matakai.

Daily Post ta wallafa cewa sanarwar ta ce:

“Lura da sauyin yanayi da tsananin ruwan sama da aka yi hasashe, akwai buƙatar ɗaukar matakan kare kai da dukiya, musamman a gabar kogi da rafi.”
Yadda aka yi ambaliya a Borno a 2024
Yadda aka yi ambaliya a Borno a 2024. Hoto: Umar Muhammad
Asali: Getty Images

Ma’aikatar ta buƙaci haɗin gwiwar dukkan masu ruwa da tsaki da ma al’umma wajen kare lafiyar jama’a da dukiyoyinsu.

Ta kuma nemi a shiryawa fuskantar matsalolin da ka iya tasowa, ciki har da kwashe mutane daga wuraren da ruwa ka iya mamaye su.

A halin yanzu dai ana ci gaba da bibiyar sauyin yanayi da nufin fitar da sababbin bayanai, yayin da hukumomi ke sa ran rage tasirin abin da ka iya faruwa.

Legit ta tattauna da Lawan Kari

Biyo bayan sanya Kari da ke karamar hukumar Darazo ta jihar Bauchi a jerangiyar, Legit ta zanta da wani mazaunin garin.

Kara karanta wannan

Yaki zai kare: Bello Turji ya ajiye makamai bayan haduwa da malaman Musulunci

Lawan Kari ya bayyana wa Legit cewa:

"Duk da cewa ba mu san ta wani yanki ba ne ake tsammanin ambaliyar, za mu yi kokarin daukar matakin da ya dace.
"Sanin abin da zai iya faruwa yana da kyau domin jama'a su dauki mataki kafin bala'i ya same su."

An yi hasashen samun ruwa a jihohi 7

A wani rahoton, kun ji cewa hukumar NiMET ta yi hasashen samun mamakon ruwan sama a jihohi akalla bakwai.

Rahoton ya yi gargadi da cewa samun ruwan zai iya jefa al'ummomi da dama a jihohin cikin hadarin ambaliya.

Legit Hausa ta rahoto cewa Kano, Kaduna, Neja, Nasarawa, Kwara, Sokoto, Filato na cikin jihohin da ake hasashen samun ruwan.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng