Shehu Sani Ya Kare Tinubu, Ya Fadi Masu Laifi kan Matsalolin Arewa
- Tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani ya bukaci a daina dora laifi kan Bola Tinubu dangane da matsalolin da suka addabi Arewa
- Sanata Shehu Sani ya bayyana cewa shugaban kasa mai-ci ba shi ba ne ya jawo matsalolin talauci da rashin tsaro a yankin ba
- Tsohon sanatan ya nuna babu masu laifi sai tsofaffin shugabannin da suka fito daga yankin wadanda suka gaza yin amfani da damarmakin da suka samu
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kaduna - Sanata Shehu Sani ya bayyana cewa talauci, rashin tsaro, da lalacewar ababen more rayuwa a Arewacin Najeriya ba laifin manufofin Shugaba Bola Tinubu ba ne.
Tsohon sanatan na Kaduna ta Tsakiya ya bayyana cewa tsofaffin shugabannin yankin Arewa ne suka haifar da wadannan matsalolin.

Source: Facebook
Tsohon sanatan ya bayyana hakan ne yayin da yake karɓar tawagar kungiyar Tijjaniyya Grassroots Mobilisation and Empowerment Initiative of Nigeria a gidansa da ke Kaduna a ranar Talata, cewar rahoton jaridar The Punch.

Kara karanta wannan
APC ta yi watsi da kalaman El Rufai, ta fadi dalilin da zai sa Tinubu yin tazarce a 2027
Shehu Sani ya soki shugabannin Arewa
Shehu Sani ya zargi shugabannin baya na Arewacin Najeriya da rashin yin amfani da damarsu, wawushe dukiyar ƙasa, tare da watsi da al’ummar da suka ba su amanar mulki.
"Muna da Buhari a kan mulki na tsawon shekaru takwas, amma Arewa ta ci gaba da zama cikin talauci."
"Masana’antu irin su KTL, UNTL, Nortex, Arewa Textiles da sauran su an bar su a lalace. Shugabanninmu sun fi mayar da hankali kan amfanin kansu fiye da ci gaban jama’a.”
Shehu Sani ya wanke Bola Tinubu
Shehu Sani ya ce ba adalci ba ne kuma yaudara ce a dora wa Tinubu laifin matsalolin yankin Arewa, alhali shekara biyu kawai ya kwashe a kan mulki, rahoton jaridar The Nation ya tabbatar.
"Matsalolin Arewa ba sun fara bame shekaru biyu da suka wuce. Tsofaffin shugabanni suna da damar gyara ilimi, lafiya, da tsaro amma sun kasa."
"Yanzu suna ƙoƙarin yaudarar ku da cewa Tinubu ne matsalar ku. Ku tambayi kanku: Shin asibitocin da suka lalace, tituna da suka rushe, da rashin tsaro duk sun fara ne cikin watanni 24 da suka gabata?”
- Sanata Shehu Sani

Source: Twitter
Tsohon Sanatan ya ƙara da jero manyan ayyukan da aka yi watsi da su kamar titunan Kaduna–Abuja, Minna–Abuja, Lokoja–Abuja, kamfanin karafa na Ajaokuta, da aikin wutar lantarki na Mambilla a matsayin shaidar yadda shugabanni suka ci amanar yankin.
"Ko da abubuwa suka tabarbare a yanzu, ku sani cewa 'yan’uwanku daga Arewa ne suka ci amanarku. Idan suka dawo mulki, babu abin da zai canza."
- Shehu Sani
Shehu Sani ya bukaci a goyi bayan Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya yaba da ci gaban da aka samu a mulkin Shugaba Bola Tinubu.
Sanata Shehu ya bukaci mutanen yankin Arewa da su marawa shugaban kasan baya, ya yi tazarce a zaben shekarar 2027.
Tsohon sanatan ya nuna cewa gwamnatin Tinubu ta yi wa 'yan Arewa ayyuka masu muhimmanci sosai.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
