Minista Ya Kwadaitawa Ibo Mulkin Najeriya, Ya ce Taimakon Tinubu zai Kai Su Aso Rock

Minista Ya Kwadaitawa Ibo Mulkin Najeriya, Ya ce Taimakon Tinubu zai Kai Su Aso Rock

  • Ministan ayyuka, Dave Umahi, ya musanta zargin da ke cewa Shugaba Bola Tinubu yana watsi da yankin Kudu maso Gabas
  • Umahi ya bayyana cewa gwamnatin Tinubu tana gudanar da muhimman ayyukan ci gaba da dama a shiyyar
  • Umahi ya roƙi mutanen yankin su goyi bayan Tinubu ya samu wa’adin mulki na biyu don su kai ga mulkin Najeriya

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja– Ministan ayyuka, Dave Umahi, ya bayyana cewa yankin Kudu maso Gabas zai samar da shugaban ƙasar Najeriya a nan gaba.

A wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, Umahi ya roƙi mutanen Kudu maso Gabas da su marawa shugaba Bola Ahmed Tinubu karo na biyu.

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu
Minista na son Ibo su sake zaɓen Tinubu Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa Ministan ya mayar da martani ne kan wani rahoto da ke zargin Tinubu da watsi da yankin Kudu maso Gabas.

Kara karanta wannan

APC ta yi watsi da kalaman El Rufai, ta fadi dalilin da zai sa Tinubu yin tazarce a 2027

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Umahi ya kare gwamnatin Bola Tinubu

Tribune Online ta wallafa cewa Umahi ya bayyana rahoton da ƙanzon kurege, yana mai cewa Tinubu bai ware yankin Kudu maso Gabas ba.

Ya ce:

“Na fahimci cewa yanzu siyasa ta fara ɗaukar zafi, kuma wasu na amfani da dabarar ruɗar da mutane, su nuna kamar su ne ke kare martabar shiyyar."

Umahi ya bayyana cewa ya umurci dukkanin daraktocin yankuna na ma’aikatar ayyuka da su koma wuraren aiki domin tattara bayanan.

Ana sa ran za su taimaka da samo bayanai a kan ayyukan da aka gada da kuma sababbin ayyuka da ake aiwatarwa.

Ya ƙara da cewa Tinubu yana adalci wajen rarraba ayyuka domin haɗa kan ‘yan Najeriya da kuma farfaɗo musu da fata, inda ya ce:

‘Ibo zai yi mulki,’ Ministan ayyuka, Umahi

Umahi ya lissafa wasu muhimman ayyuka da ake aiwatarwa a yankin, daga ciki har da hanyar gadar Niger ta biyu da ke jihar Delta, wanda ya kai kimanin Naira biliyan 46.

Kara karanta wannan

'Mene aka yi mana?' Hadimin Ganduje ya ce za su tuhumi Tinubu a Kano

Ya buƙaci mutanen yankin su marawa Tinubu baya saboda ya nuna soyayya da adalci ga yankin Kudu maso Gabas.

Ana son Tinubu ya zarce
Minista ya ce zaɓen Tinubu zai taimaki Ibo bayan 2027 Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Ya ce:

“Bai kamata mu sake bari a ruɗe mu ba. Dole ne Shugaban Ƙasa ya samu kuri’un Kudu maso Gabas har zuwa 90% domin ƙarfafa dangantakar nan.”
“Idan muna son mu zama shugaban ƙasa, dole ne mu guji siyasar ƙiyayya, yaɗa ƙarya da kuma jin kai da banbanci.”
“Dole ne mu tallafa wa sauran yankuna, kuma da ikon Ubangiji, wata rana su ma za su tallafa mana."

Martanin gwamnatin Tinubu ga ƴan Arewa

A baya, kun ji gwamnatin tarayya ta yi watsi da zargin da wasu fitattun 'yan siyasa daga Arewa ke yi na cewa gwamnatin Bola Tinubu ya yi watsi da shiyyar.

Darakta Janar na ofishin kasafin kuɗi na ƙasa, Tanimu Yakubu, ne ya bayyana haka a wata sanarwa da aka fitar, tare da bayyana yawan aikin da aka turo Arewa.

Tanimu Yakubu ya ƙara da bayyana cewa Arewa ce ta fi kowane yanki samun kaso mafi tsoka daga cikin kasafin kuɗi na manyan ayyuka a shekarun 2024 da 2025.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng