'Babban Bala'in da ke Tunkaro Mu': Shehi Ya Faɗi Abin da Bello Turji Ya Faɗa Masa

'Babban Bala'in da ke Tunkaro Mu': Shehi Ya Faɗi Abin da Bello Turji Ya Faɗa Masa

  • Sheikh Musa Yusuf Assadus Sunnah ya bayyana yadda yara ƙanana masu shekaru 10 ke sarrafa bindigogi a wuraren 'yan ta'adda
  • Malamin musuluncin ya ce ya ziyarci yankin Zamfara, inda ya ga fiye da yara 500 da ba su je makaranta ba suna dauke da AK-47
  • Musa Yusuf Assadus Sunnah ya ce duk maganar da ake yadawa cewa an hallaka Kachallah Danbokolo karya ne, ya ce ya gan shi ido da ido

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kaduna - Sheikh Musa Yusuf Assadus Sunnah ya yi karin haske kan yanayin ta'addanci a Arewa maso Yammacin Najeriya.

Sheikh Assadus Sunnah ya bayyana babban abin da hango ka iya faruwa a gaba game da ta'addanci idan ba a tsaya ba.

Shehi ya bayyana damuwa kan ƙaruwar ta'addanci
Sheikh Assadus Sunnah ya magantu kan ganawa da Bello Turji. Hoto: Sheikh Musa Yusuf Assadus Sunnah.
Source: Facebook

Assadus Sunnah ya damu kwarai da matsalar ta'addanci

Kara karanta wannan

'Dalilin da ya sa jam'iyyar PDP ke son ba Goodluck Jonathan takara a zaɓen 2027'

Malamin ya fadi haka ne a cikin wani faifan bidiyo mai tsawon mintuna 55 da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shehin malamin ya ce zuwansu wurin Bello Turji ya ga yara ƙanana da ba su kai shekaru 11 ba suna sarrafa bindiga AK-47.

Ya ce wannan lamari ya daga masa hankali duba da irin abin da zai iya faruwa a gaba idan ba a dauki matakin da ya dace ba.

A cewarsa:

"A Giwa ta nan Kaduna, na ga yara yan shekara 12 da bindiga AK-47, da na je wajen Bello Turji sai na ga yara yan shekara 10.
"Babu boko, babu Islamiyya amma a shekara 10 sun iya sarrafa bindiga AK-47, wadanda suka je wajen zaman sun fi 500.
"A hakan ma suka ce wadannan mutanen ba su kai ɗaya bisa 100 na mutanensu ba da ke yankin."
Shehin malami ya ce ido da ido ya gana da Bello Turji
Sheikh Assadus Sunnah ya fadi yadda ya yi sanadi Turji ya ajiye makami. Hoto: Sheikh Musa Yusuf Assadus Sunnah.
Source: Facebook

Malamin ya fadi tashin hankali da ya gani

Sheikh Assadus Sunnah ya ce babban abin tashin hankali shi ne yadda kungiyoyin jihadi ke zawarcin su Bello Turji.

Malamin ya ce a yanzu ne fa da ake iya maganar sulhu da su idan lamarin ya koma akida sai yadda Allah ya yi.

Kara karanta wannan

Yaki zai kare: Bello Turji ya ajiye makamai bayan haduwa da malaman Musulunci

Ya ce daga ranar da lamarin ya bar garkuwa da mutane ya koma akida barnar da za a fuskanta sai ta fi wacce ake ciki yanzu.

"Abin tashin hankali da Turji ya fada mana shi ne Malam yadda ku ka zo nan domin tattaunawa, kun san kungiyoyin jihadi ma na zuwa gare mu?.
"Kungiyoyin irin su ISIS, to mu da muke cewa a yi sulhu ranar da wata akida ta ribace su duk wanda ba su ba za su dauke su a matsayin kafurai ne.
"Daga ranar da suka dauka akida ce idan sun kashe ka, wuta za ka je, su kuma aljanna za su tafi daga nan, babu damar ma yin sulhu da su.
"Kuma daga lamarin ya bar garkuwa da mutane ya koma akida, barnar da za mu fuskanta sai ya fi wanda muke ciki yanzu."

- Cewar Sheikh Assadus Sunnah

Har ila yau, Malamin ya ƙaryata maganar da ake yadawa cewa an kashe Kachallah Danbokolo inda ya ce ya ganshi ido da ido tare da Turji.

Sheikh ya magantu kan haduwarsa da Turji

Kara karanta wannan

Nafisa: Pantami ya nemi Tinubu ya karrama 'yar Yobe da ta ci gasar Turanci a duniya

Kun ji cewa shehin malami, Sheikh Musa Yusuf Assadus Sunnah ya bayyana damuwarsa kan ƙaruwar ta'addanci a Arewa maso Yamma.

Ya ce sun ziyarci Bello Turji sau uku a watan da ya wuce domin zaman sulhu, inda suka fuskanci bala’i duk a kokarin ceto al'umma.

Malamin ya koka kan yadda wasu ke sukar kokarinsu, duk da suna shiga hatsari suna wa'azi da rokon 'yan bindiga da su ji tsoron Allah.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.