"Mutuwa Mai Yankar Ƙauna": Ango da Abokinsa Sun Rasu Kwana 2 bayan Ɗaura Aure
- An kashe wani sabon ango da aka ɗaura aurensa a ranar 2 ga watan Agusta, 2025 a jihar Benuwai da ke Arewa ta Tsakiyar Najeriya
- An ruwaito cewa an kashe angon ne tare da abokinsa, lamarin da ya ja hankalin mazauna yankin saboda ba a san waɗanda suka yi kisan ba
- Sanata Abba Moro mai wakiltar Benuwai ta Kudu ya yi Allah wadai da wannan kisa, inda ya bukaci jami'an tsaro su kamo duk wanda ke da hannu
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Benue - Wani sabon ango da abokinsa sun rasa rayukansu a ranar Litinin a ƙauyen Ulam da ke kan titin Awajir-Oju, a Karamar Hukumar Gwer ta Gabas a Jihar Benue.
An gano sunayen waɗanda aka kashe da Jonathan Uko da Ogoda Gabriel, dukkansu 'yan asalin kabilar Igede daga Karamar Hukumar Oju.

Asali: Original
Daily Trust ta rahoto cewa abokanan biyu na tsaka da tafiya a kan babur daga Oju zuwa Makurdi lokacin da aka kai musu hari kuma aka hallaka su.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An ce an gano gawarwakin waɗanda aka kashe a Ulam, yankin da masu magana da harshen Tiv ke zaune, duk da an san suna zaman lafiya da ƴan kabilar Igede.
An kashe sabon ango a jihar Benue
Wata mazauniyar garin Oju mai suna Adia, ta bayyana cewa Jonathan ya yi aure ne a ranar 2 ga watan Agusta, amma aka kashe shi kwana biyu bayan bikin.
Ta ƙara da cewa matar abokin Jonathan, wanda aka kashe su tare, ba ta jima da haihuwa ba.
“Babu wata rigima tsakanin mutanen Ulam da Igede. A da, rikice-rikice sun faru ne tsakanin Bonta a Konshisha da Ukpute a Oju, amma yanzu an samu zaman lafiya.
"Har yanzu muna ƙoƙarin gano waɗanda ke da hannu a wannan ɗanyen aiki” in ji Adia.

Kara karanta wannan
Talaka bawan Allah: ADC ta fusata da Tinubu zai kashe N712bn a gyaran filin jirgin Legas
Ana zargin makiyaya ne suka kashe mutum 2
Sai dai wani mazaunin Tiv daga Gwer ta Gabas, wanda ya nemi a ɓoye sunansa, ya dage cewa makiyaya ne suka aikata kisan, saboda a cewarsa sun saba tare hanya suna kashe matafiya.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda a Jihar Benue, DSP Udeme Edet, bai amsa kiran waya ko sakon tes da aka tura masa ba dangane da lamarin.
Amma Sanata Abba Moro ya yi tir da kisan Jonathan da Gabriel, yana kiran lamarin da “aikin dabbanci.”

Asali: Facebook
Sanata Moro ya yi Allah wadai da kisan
Sanata Moro, wanda ke wakiltar mazabar Benue ta Kudu a Majalisar Dattawa, ya nuna cewa kisan gilla da aka yi wa waɗannan matasa masu tasowa abin Allah wadai ne.
“Wannan abin bakin ciki da takaici ne matuƙa,” in ji shi.
Sanatan ya yi kira ga hukumomin tsaro da su yi duk mai yiwuwa wajen cafke masu hannu a wannan mummunan laifi tare da tabbatar da an hukunta su bisa doka.
Mahara sun kashe basarake a jihar Benue
A wani labarin, kun ji cewa wasu da ake zargin makiyaya ne dauke da makamai sun kai farmaki a kauyen Ukohol da ke ƙaramar hukumar Guma a jihar Benue.
An tattaro cewa maharan sun kashe basaraken kauyen mai suna, Zaki Aondohemba Isho, tare da wasu mutane biyu.
Wani ganau ya bayyana cewa, wadanda aka kashe sun je gonarsu su yi noma ne lokacin da makiyayan suka zo suka bude musu wuta.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng