'Yan Majalisa Sun Jawowa Kansu, An Dakatar da Su kan Aikata Rashin Gaskiya

'Yan Majalisa Sun Jawowa Kansu, An Dakatar da Su kan Aikata Rashin Gaskiya

  • Majalisar dokokin jihar Benue ta tauna aya domin tsakuwa ta ji tsoro bayan da ta dauki matakin ladabtarwa kan wasu mambobinta
  • Majalisar ta dakatar da mambobinta bayan da aka sanya su bincike kan zarge-zargen da ake yi kan wani shugaban karamar hukuma
  • An dai zargi 'yan majalisar da yunkurin boye gaskiya aikin da aka ba su domin ba da kariya ga shugaban karamar hukumar

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jinar Benue - Majalisar dokokin jihar Benue ta dauki matakin ladabtarwa kan wasu daga cikin mambobinta.

Majalisar dokokin ta jihar Benue ta dakatar da mambobi biyar daga halartar zaman majalisa har sau uku.

Majalisar dokokin Benue ta hukunta mambobinta
Majalisar dokokin Benue ta dakatar da wasu mambobinta Hoto: Benue State House of Assembly
Source: Facebook

An dakatar da 'yan majalisa a Benue

Jaridar The Nation ta rahoto cewa an dakatar da 'yan majalisar ne bisa zargin katsalandan da suka yi a cikin rahoton bincike kan ayyukan shugaban karamar hukumar Otukpo, Hon. Maxwell Ogiri.

Kara karanta wannan

Wani rikicin ya barke a Filato, an rasa rai bayan kona tarin gidaje

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wadanda aka dakatar sun hada da Hon. Shimawua Terna, Hon. Mathew Damkor, Hon. Cephas Dyako, Hon. Moses Egbodo, da Hon. Isaac Echekliye, rahoton tashar Channels tv ya tabbatar.

Dukkan 'yan majalisar da aka dakatar mambobi ne na kwamitin dindindin na majalisa kan harkokin kananan hukumomi, tsaro da harkokin masarautu.

Tun da farko dai, Majalisar ta ba wa kwamitin wanda da Hon. Shimawua Terna ke jagoranta, umarnin gudanar da bincike kan zarge-zargen almundahana da amfani da ofishi ba bisa ka'ida ba da aka yi wa Hon. Mazwell Ogiri.

Amma yayin gabatar da rahotonsu, an gano cewa kwamitin ya kauce daga abubuwan da bincikensu na gaskiya ya gano.

Bayan rashin gamsuwa da rahoton, majalisar ta kafa wani kwamitin bincike na wucin gadi mai mambobi biyar karkashin jagorancin Hon. Bemdoo Ipusu domin sake gudanar da bincike na gaskiya da bayyana abin da ya faru.

Meyasa aka dakatar da 'yan majalisar?

Majalisar ta yanke shawarar dakatar da mambobin kwamitin saboda zargin yunkurin boye gaskiyar lamari game da almundahana da amfani da ofishi ba bisa ka’ida ba, tare da rufe zauren majalisar karamar hukumar Otukpo da shugaban ya yi.

Kara karanta wannan

Sun aikata manyan laifuffuka: Gwamnati ta kori manyan alkalai 2 daga aiki a Neja

Majalisar ta kalli abin da suka yi a matsayin wani yunkuri na kare shugaban karamar hukumar daga fuskantar hukunci kan laifuffukan da ake zarginsa da su.

Majalisa ta dakatar da mambobinta a Benue
Majalisar dokokin Benue ta dakatar da wasu mambobinta Hoto: Legit.ng
Source: Original

Karanta karin wasu labaran kan jihar Benue

Gwamnan jihar Benue ya kori kwamishinoni

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Benue, Rev. Fr. Hyacinth Iormem Alia, ya sallami dukkanin kwamiahinoninsa daga bakin aiki.

Gwamna Hyacinth Alia ya rushe majalisar zartarwar jihar gaba dayanta, a wani matakin garambawul wanda ba a yi zaton faruwarsa ba.

Bayan rushe majalisar.zartarwar, Gwamna Hyacinth Alia, ya nada mukamin shugaban ma'aikatan fadar gwamnati.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng